Tsarin Tattalin Arziki a Musulunci

Shin a musulunci akwai tattalin arzikin?
Na’am shi ne ma mafi tsarin wanda duniya ta taba gani.

Shin tattalin arzikin musulunci dan jari hujja ne ko kuma gurguzu ko kuma na rabawa na tsattsauran gurguzu?
Shi tsari ne ba na jari hujja ba, kuma ba na guguzu ba, kuma ba na rabawa ba da ma’anar da aka sani a yau.
T: To yaya tsarin tattalin arizikin musulunci yake kenan?

A: Shi tsarin musulunci yana girmama ikon mallakar daidaikun mutane ga dukiya kuma yana tabbatar da hakan da sharadin kada dukiya ta kasance ta haram kuma ya bayar da hakkinta[1].

Yaya dukiya take taruwa ga daula?
Ta hanyar hakkokin da suke wajibi da aka sanya a musulunci.
Wane hakkoki ne na wajibi?
Su guda hudu ne: humusi, zakka, haraji, jizya
Madogarar Dukiya A Musulunci

Mene ne ake nufi da madogarar samun dukiya a musulunci ga daula da kuka ambata?
Humusi: shi dukiya ce da shugaban musulmi yake karbar kashi ishirin cikin dari nata: daga ribar cinikayya da kuma ma’adinai, da taskoki, da abin da aka samu a karkashin ruwa, da dukiyar halal da ta cakuda da haram da kuma ganimar yaki da kuma wani kaso daga kasa.
Zakka: dukiya ce da shugaban yake karba daga daya cikin arba’in na tumaki da shanu da rakuma da zinare da azurfa da dabino da zabib da sha’ir da alkama.

Haraji: shi ne abin da shugaban yake karba daga masu shuka a kasashen da aka ci su da yaki da kai hari.

Jizya: shi ne abin da shugaban musulmi yake karba daga Yahudawa da Nasara da majusawa da suke karkashin alkawari da sauran kafirai domin a kare su kuma su samu kariya.

Shin a musulunci akwai banki?
Na’am sai dai kada ya kasance akwai riba ko karbar kari, domin a musulunci ana ganin riba a matsayin yaki da Allah da manzonsa, kuma a aiwatar da dokokin musulunci a dukkan hukunce-hukuncen banki, kuma ana tafiyar da hakkokin masu aiki daga dukiyarsa (banki) amma idan ta tawaya to sai a ba su daga Baitulmali.
Shin daula tana iya karbar wani abu daga mutane bayan wannan?
A’a, daula ba ta da hakkin karbar wanin wannan daga mutane, kuma ya zo a hadisi cewa; Wanda ya karbi dukiyar wani ba tare da yardarsa ba, to Allah zai kwatar masa a ranar lahira maimakon kowane dirhami salla dari bakwai daga sallolinsa karbabbu a bayar da ita ga mai dukiya.

Baitulmali (Gidan Dukiyar Daula)

Me daular musulunci zata yi da abin da take karba na dukiyoyi?
Daular musulunci tana da wani ofis da ake kira Baitulmali da ake boye dukiyar a cikinsa kuma ana tanadin sa ne domin bukatun dukkan mabukatan musulmi.
Daula ce take yin dukkan ayyukan gyara da raya kasa da ci gaba, kuma ta dauki nauyin duk wani talaka da dukiya isasshiya domin tafiyar da rayuwarsa, har sai ya kasance babu wani talaka a kasa.

Kuma a biya bukatar duk wani mai bukata,, wanda yake bukatar aure ko jari ko gida ko kanti ko likita don magani ko kuma tafiya ta lalura, ko yana neman guzuri a kan hanyar tafiyarsa ko kuma karatu da yake bukatar dukiya da sauransu to wannan duk yana komawa ga Baitulmali ne, kuma hanyar tabbatar da bukatarsa tana da sauki, wato; ita ce shedu biyu ko rantsuwa a kan cewa yana bukatar abu kaza kuma ba shi da dukiya da zata ishe shi, to ta haka ne zai kasance babu wani mabukaci ko talaka da zai ragu a daula.

Shin wadannan hakkoki hudu sun isa dukkan bukatun mutane?
Wannan ya isa idan aka hada da abin da daula take samu na Anfal, kuma ya zo a hadisi cewa; “idan ma ba ta isa ba to Allah zai kara yawanta”[2].

karancin Ofisoshi Da Ma’aikata

Yaya dukiyar da kuka ambata zata isa tare da karancinta, kuma muna ganin yau ga dukiya mai yawa amma ba ta isa?
Zata isa saboda karancin ma’aikata da kuma rikon amanar masu kula da ita, da kuma barin al’amura a hannun mutane. Misali: masu aiki a daula ba su da yawa kuma mafi yawan ayyukan hukuma a yau suna hannun mutane ne, sai ayyukan hukuma suka zama ba su da yawa sosai, kuma abin sani cewa idan ma’aikata suka yi karanci kuma aka bar al’amura a hannun mutane kuma masu kula da albarkatun kasa suka zama amintattu, to dukiya zata yawaita[3].
T: Shin ana ba wa wanda ya kasa aiki dukiyar?

A: Idan talaka ya kasance ba zai iya aiki ba to ana ba shi daidai gwargwadon bukatarsa kamar yadda yake bisa al’adar hukumomi a yau[4].

Lamunin Rayuwa A Musulunci[5]

Shin a musulunci akwai lamunin rayuwa?
Na’am kuma shi ne mafi kyawun lamuni na al’umma kuma mafi daukaka.
Shin zaku iya yi mana bayanin wani abu na lamunin rayuwar al’umma a musulunci?
Lamunin rayuwar al’umma a musulunci -wato daukar nauyin rayuwa da matsalolin al’umma- wani abu ne da ya kai matukar da ba a taba samun irinsa ba a wani tsari a fadin tarihin samuwar dan Adam.

Misalan Lamunin Rayuwar Al’umma Na Musulunci

Musulunci ya lamunce rayuwa yana cewa:

1-Dukkan wanda ya mutu yana da bashi ko ya bar iyali ba mai kula da su, to yana kan jagoran musulmi ya biya bashinsa kuma yana kansa ya reni iyalansa.

2-Duk wanda ya mutu yana da dukiya to dukiyarsa ta magadansa ce gaba daya.

3-Hade kuma da hidimar dukiya da Baitulmali yake yi wa mutane, domin daukar nauyin bukatunsu na farko, da kuma yalwata musu.

Shin kana iya ganin duk da haka akwai lamunin rayuwar al’umma irin wannan a duk duniya hatta da inda ake da cigaban wayewa?
Tabbas babu.
Kai tsari na jahiliyya kafin musulunci da kuma na cigaban zamani a yau suna ma sanya haraji mai yawa ne a kan gado, kamar yadda kuma ba sa daukar nauyin biyan bashin wani mutum ko kuma daukar kulawa da iyalansa, kuma ba laifi idan muka kawo wasu misalai kan lamunin musulunci kamar haka.

Misali na farko

Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da daukar nauyin al’amuran al’umma da zamu kawo wasu kamar hakan:

Daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: manzon (S.A.W) ya ce: “Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (A.S) shi ne ya fi cancanta da shi bayana”. Sai aka ce da shi Imam Ja’afar Sadik me wannan yake nufi? Sai ya ce: fadin Annabi (S.A.W) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce”[6].

Misali na biyu

Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kubuta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi”[7].

Bayan Imam Sadik ya fadi wannan hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce: “babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (S.A.W), kuma sun yi imani da su da iyalansu”[8].

Misali na uku

Sheikh Mufid ya karbo daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) yana cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: “ya ku jama’ar musulmi! ni an aiko ni ne kusa da alkiyama … -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to ta iyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni”[9].

Haka nan ya karbo daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karba kuma bai ciyar da ita a barna ko sabo ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fadin Manzon Allah (S.A.W) cewa:”duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka yana kan jagora duk abin da yake kan Annabi (S.A.W)[10].

Misali na hudu

Musulunci ya sanya kusan talauci ya kawu daga dukkan daula da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya, kuma ya kasance labari ne.

Hurrul amuli ya ambaci cewa: Imam Ali (A.S) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa Mene ne haka?

Sai ya ce: ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara.

Sai Imam Ali (A.S) ya yi fushi ya ce: kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rika rayuwa da shi[11].

Wanan kissa tana nuna cewa; talauci ya kusa kawuwa gaba daya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta Imam Ali (A.S) da ya ga talaka guda daya sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al’ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da ba ya riko da musulunci, domin kada a samu talaka a kasar musulmi da zai fito koda kuwa mutum daya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yaki da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yaki da talauci ta kuma daukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu na daga kafirai matukar suna karkashin daular.

Misali na biyar

Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: yayin da Ali (A.S) ya rusa dalha da zubair sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu. Sannan sai uwar ma ta mutu, sai Imam Ali (A.S) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?

Sai suka ce: tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu.

Sai ya tambaye ta waye ya riga mutuwa a cikinsu?

Sai suka ce danta ya riga ta mutuwa.

Sai ya kira mijinta baban yaron mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi ya mutu.

Ya ce: wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara[12].

Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al’ummar musulmi da kuma biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu, wannan kuwa kamar yadda ya zo ne a hadisi cewa: hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza[13]. A wani hadisin ya zo cewa: jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al’umma da yalwa da arziki da kuma lamunce rayuwar al’umma da adalci.

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

www.haidarcenter.com

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

hfazah@yahoo.com – hfazah@hotmail.com

 

 

[1] Kamar humusi da zakka d.s.s.

[2] Da sharadin kada wasu su cinye hakkin wasu.

[3] Da yawa an samu kasashe da sake fama da talauci sakamakon yawan albashin ma’aikata da suke fama da shi, sai suka samu warware matsalar da hana ci gabata ta hanyar rage ma’aikata, karancin ma’aikata yana daga cikin abin da musulunci ya kwadaitar da shi, amma abin takaici wasu kasashe suna amfani da wannan yayin da musulmi suka yi jifa da shi.

[4] Kamar ciniki na halal, ko sharadi cikin ciniki.

[5] Littafin Addamanul ijtima’I fil islam, na Ayatul-Lahi Sayyid Sayyid Ja’afar Sadik shiraz.

[6] Tafsiri nurus sakalain: mujalladi 4, shafi: 240.

[7] Wasa’ilus Shi’a, mujalladi 13, shafi: 151.

[8] Mustadrikul wasa’il, mujalladi 2, shafi: 490.

[9] Mustadrikul wasa’il, mujalladi 4, shafi: 490.

[10] Mustadrikul wasa’il, mujalladi 4, shafi: 492.

[11] Wasa’ilus Shi’a.

[12] Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa’il, mujalladi 17, shafi: 446.

[13] Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100.

Check Also

32-Kwace, Dukiyar Al’umma

  Dukiyar mutane hurumi ce babba da shari’a ta tsananta haramcin tabawa ba tare da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *