MATSAYIN FALSAFA

A bahasin da ya gabata mun yi bincike kan Jigon bahasin Falsafa wato Take da Jigon abin da take magana kansa, a nan kuma muna son magana a takaice game da mas’alolin da take bincike kansu. Idan mun kula zamu ga mun yi bahasin a fakarorin da suka gabata kan cewa Jigon bahasin Falsafa ba ya karbar gwaji sai dai dalilin hankali, to haka nan ma mas’alolin Falsafa wato jumloli da take magana kansu ba sa karbar gwaji domin mas’alolin duk suna kunshe da bayanin jigon bahasin ne.

Domin wannan mas’ala ta fito a fili muna iya tambayar cewa: Shin idan mutum ya mutu yana ci gaba da rayuwa ko kuwa shi ke nan rayuwarsa ta kare? Kuma shin idan rayuwarsa ba ta kare ba to zai yiwu ke nan ya tashi da wannan jikin ko kuwa wani jikin ne daban?.

Irin wadannan tambayoyi da makamantansu babu wani ilimin gwaji da zai iya amsa su domin ba mahallin bincikensa ba ne, ba mahallin bahasin ilimin dabbbobi ko tsirrai ko duniya ba ne. Haka nan ma wasu ilimomin da suke na hankali tsantsa kamar lissafi (mathematics) da Mantik (logic) duk ba zasu iya amsa wannan tambaya ba domin suna bahasi kan ma’anonin Mantik na biyu da bayaninsu ya gabata. Sai lamarin irin wannan bahasin ya rage a ilimin da yake bahasin ma’anonin Falsafa na biyu da muka yi bayani a baya.

Binciken yana iya kasancewa karkashin ilimin Akida (da yake bahasi mai salon nakalto abin da ya zo a shari’a da karfafar shari’a da hankali) ko Falsafa (mai bahasi mai salon hankali tsantsa), kuma ilimin rai a Falsafa shi ne ya fi kowane ilimi ba wannan bahasin hakkinsa. Sai ya yi mana bayanin mutum cewa shin ya takaita da wannan jikin ko kuwa? Idan kuma yana da rai shin ransa mai wanzuwa ce ko mai lalacewa ce bayan mutuwa?.

A fagen ilimin halaye da siyasa da sauransu ma muna bukatar Falsafa a wasu mas’alolin kamar mas’alar sanin hakikanin sharri da alheri, ko kuma sanin kyau da muni a ilimin halaye da ake binciken cewa ayyuka suna siffantuwa da kyau da muni na hankali ko kuwa na shari’a ne kawai? Da kuma bahasin ma’aunin sanin ayyukan da suka dace da wadanda ba su dace ba mene ne yake ayyana hakan?

A nan ne zamu san kimar ilimin sani da muka yi bayanin sa a baya wanda yake lamunce mana bincike kan nau’in ilimomi, fagagen da suke bincike, iyakacin abin da suke amfani da shi wurin bincike, da kuma iyakacin yakinin da suke bayarwa ko rashinsa. Da wannan ne zai bayyana gare mu cewa kamar yadda sauran ilimomi suke bukatar Falsafa ita kuma tana bukatar ilimin sani don warware matsalolin ilimi na bai-daya. Sai dai ka da a manta cewa a bayaninmu game da ilimin sani mun gabatar da cewa shi ma wani bangare ne na Falsafa da aka ware shi don muhimmancinsa sai ya tashi wani ilimi mai zaman kansa kamar dai yadda aka fitar da mas’alolin Lissafi (Mathematic) daga Mantik (Logic).

Sai mas’alolin suka kasance wasu na biye wa wasu kamar yadda wasu suke dogara kan wasu. Idan muna bincike kan samuwar Allah da siffofinsa da kamalarsa a zatinsa da aikinsa baki daya da suka hada da halittar mutum, raya shi da kashe shi, ba shi da lada ko azaba, da sauran ayyukansa zamu samu sun doru kan ilimin sanin Allah kebantacce. Su kuwa wadannan mas’alolin sun dogara kan ilimin samuwa na bai-daya da aka fi sani da Falsafa. A ilimin Falsafa ne ake bincike kan samamme mai canjawa da maras canjawa da siffofinsu, da na samammu mai tasiri da mai tasirantuwa, mai jiki da maras jiki, mai samarwa da abin samarwa, wajibin samuwa da mai yiwuwar samuwa. Irin wadannan bahasosin babu mahalli ga salon gwaji a cikinsu sai dai salon hankali.

Sannan idan muka nutsa sosai muka sanya hankali zamu sake ganin cewa irin wadannan mas’aloli suna dogara kan ilimin sani (epistemology) domin sai an yi fandeshan (foundation) sannan ake gini. Sai an tabbatar da yiwuwar sani da yarda da riskar abubuwa da sauran bahasosin wannan ilimin sannan za a iya motsawa don bincike kan hakan. Sannan da wannan ne zai bayyana gare mu cewa ba kowace mas’ala ba ce hatta a ilimin  Falsafa da ma’anarsa kebantacciya (Ilimin sani Allah da siffofinsa da ayyukansa) za a iya bahasinta ba dole sai an dogara da Falsafa da ma’anarta mai fadi ta bai-daya (ilimin samuwa bai-daya).

Kamar yadda muka yi bayani kan jigon da ilimin Falsafa yake bincike kansa (samuwa) a baya cewa babu wani ilimi da zai iya tabbatar da shi domin shi mai samuwa ne da kansa ba ya bukatar tabbatarwa a wani ilimi, haka nan ma mas’alolin ilimin Falsafa babu wani ilimi da take jingina da shi don ya tabbatar masa da su sai dai idan ma’anoni da ake riskar su ta hanyar mariskai guda biyar da Falsafa zata yi amfani da su a matsayin matashiya don yin bahasinta. Amma sauran ilimomi suna bukatar wasu ilimomin da zasu tabbatar da mas’alolinsu don su yi bincike kansu, misali likitanci yana bukatar tabbatar da samuwar jiki domin ya yi bahasi kansa, kuma tabbatar da samuwar jiki yana kasancewa ne a wani ilimi ba a ilimin shi kansa likintancin ba, amma Falsafa babu wani ilimi da take jira don ya tabbatar mata samuwar samamme maras jiki wanda mariskai biyar ba sa iya riskarsa.

A cikin abin da muka kawo maka akwai wadatarwa ga mai lura sai ka karanta ka tashi sama! Sai kuma mu waiwayi bahasin “Hadafin Falsafa” a nan gaba. Allah ya yi maka lutufinsa.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

3 comments

  1. Ahmad Aliyu Al-Kashnawiiy

    Ameen mlm.Mun gode sosai.Ya kamata a ware mana lkc ai mana bayani kan ilmin Mantiq(LOGIC).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *