Mas’aloli Game Da Annabi – 2

Kafin mu yi nisa cikin bayanin annabawa yana da kyau mu leka mu ga bayani game da annabin rahama da ya fi kowane mutum kamala a cikin halittar Allah kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslim da suke babbar madogara gun ‘yan’uwanmu ‘yan Sunna.

Imanin Iyayen Annabi

A bayanan da suka gabata an dan yi nuni game da annabawan da suka gabata a mahangar Buhari da Muslim, a nan kuma muna son magana game da rayuwar annabi kafin annabci da bayan annabci cikin bayanai kamar haka:

Kafin Annabci

Daya daga cikin mafi munin abin da ya zo a cikin sahih Muslim shi ne batun kafircin iyayen annabi (s.a.w) da ya zo a kitabul imani, babi na 88, da yake bayanin cewa duk wanda ya mutu kan kafirci to yana wuta a Hadisi na 203, ibn majah ma ya kawo shi a juzu’i na daya Hadisi 1572, da Abu Dawud a Juzu’i na 2, babi 18. Cewa wani mutum ya zo wurin annabi ya tambayi inda iyayensa suke sai ya ce suna wuta, amma saboda wannan mutumin ya tafi sai annabi ya kira shi ya ce masa: Da babana da babanka duk suna wuta.

Har ila yau a kitabul jana’izi a babin neman izinin annabi ya ziyarci kabarin babansa a ruwayar Abuhuraira haka nan yana kawo cewa annabi ya nemi ya nema wa babarsa gafara ba a ba shi izini ba, amma ya nemi izinin ziyarar babarsa sai aka ba shi izini. Wannan kuwa yana nuni da cewa ta rasu kafira kuma bai halatta a yi wa kafiri addu’a ba ko a nema masa gafara!.

Na daya: Sai dai tarihin gidan Banu Hashim yana karyata wannan ruwayoyi masu danganta kafirci da mutuwar jahiliyya ga iyayen annabi (s.a.w), domin gidan su sun kasance masu bautar Allah madaukaki masu kadaita shi, ba su taBa yin shirka ba kamar yadda ya zo a tarihin wannan gidan.

Na biyu: Ruwayar da Asbag dan Nabata ya karBo daga Imam Ali (a.s) yana rantsuwa da Allah cewa ba a taBa samun wani mai kafirci ko shirka ba daga kakanninsa yana cewa: Wallahi babana ko kakana ko Hashim ko Abdumanaf ba su taBa bautar gumaka ba sam. Sai aka tambaye shi me suke bautawa? Sai ya ce: Suna salla zuwa dakin ka’aba ne a kan addinin Ibrahim, suna masu riko da shi[1].

Haka nan idan muka duba babun Nawadir a littafin “Manla yahdhuruhul fakih” zamu ga manzon Allah (s.a.w) yana karfafa wannan maganar cewa kakanninsa sun kasance sun nesanta daga tawassulin shayarwa da gumaka ko bautar gumaka, kuma ba su taBa cin naman da aka yanka da sunan gumaka ba.

Idan mun duba Masnad Ahmad bin Hambal, da Tabakat na Ibn Sa’ad, da wasu littattafai duk zamu ga sun kawo cewa akwai wasu mutane da suke bautar Allah kafin aiko manzon Allah (s.a.w). Daga cikin wadannan gidajen masu tauhidi akwai gidajen Baun Hashim kuma su suka fi shahara da wannan, idan mun duba a fili zamu ga cewa su ne suka fara yin imani da annabcinsa, kuma su ne aka fara aika musu shi. Wannan ne abin da ya yi daidai da juyawar manzon Allah cikin tsatson tauhidin masu sujada ga Allah madaukaki kamar yadda Kur’ani ya saukar.

A bisa hakika umayyawa sun so su kaskantar da darajar manzon Allah (s.a.w) da wannan ruwayoyin ne, sakamakon cewa sun fito daga tsatson kafirci, don haka gidan umayyawa mai gaba da hashimawa babu wani abu da zai yi don hucewa sai Bata sunan annabi da kaskantar da darajarsa don ka da aibobin su keBanta da su. Sai dai ba banu umayya ne abin mamaki ba, wasu daga cikin al’ummar musulmi da suka yi imani da wannan lamarin sun fi ban mamaki, yayin da suka shiga fadan umayyawa da hashimawa kuma suka goya wa umayyawa baya don gaba da gidan annabi (s.a.w).

Cin Naman Haram

A ruwayar Abdullah dan Umar sun ruwaito cewa manzon Allah (s.a.w) ya kasance ya hadu da Zaid dan Amru dan Nufail a dutsen Baldah, har ma ya gabata wa Amru da abinci har da nama, sa Amru ya ki cin naman ya ce masa: Ba na cin naman da kuka yanka da sunan gumaka da mutum mutumi, ni ina cin naman da aka yanka da sunan Allah ne kawai.

Wannan ruwayar da ta zo a Buhari juzu’i na bakwai, babin abin da aka yanka da sunan gumaka, tana nuna mana cewa:

Masnad Ahmad yana ruwaito cewa manzon Allah da Abusufyan ne suke cin abin da aka yanka da sunan gumaka, sai Zaid ya ki ci, ya zarge su da cin yankan gumaka, sai tun daga wannan lokacin manzon Allah (s.a.w) ya bi shi ya yi alkawarin zai daina ci, kuma bai sake ci ba har aka aiko shi.

1- Zaid dan Amru ya kasance yana kan tauhidi da kadaita Allah kafin aiko annabi.

2- Annabi (s.a.w) ya kasance yana rayuwa kamar sauran mushrikai yana cin yankan gumaka.

Babban hadafin wannan ruwayar shi ne don a nuna wa duniya cewa akwai wanda ya fi manzon Allah (s.a.w) tauhidi da sanin Allah tun kafin a aiko shi, kuma idan bautar Allah da kin cikin yankan gunki da kadaita Allah falala ce, to akwai wanda ya fi annabi ke nan. Wannan shaidanar ta kaskantar da manzon Allah (s.a.w) tana daga cikin tsarawar da umayyawa suka yi wacce ta yi tasiri a akidun musulmi, har sai da ya zama umayyawa sun dasa wa masu biyayya ga tafarkinsu da riko da kayarwarsu cewar wasu daga sahabbai a aikace sun fi Annabi daraja!.

Hadafin kawo wannan falala ta Zaid domin a nuna cewa kabilar Umar dan Khaddabi ma ta riga Hashimawa sanin tauhidi hatta da annabin kansa, Zaid ya kasance dan ammin Umar bn Khaddab, kuma baban matarsa ne. Sau da yawa kabilu suka kirkiro wa kawukansu falaloli domin su nuna hashimawa ba su fi su da komai ba, sai dai mafi yawan irin wadannan ruwayoyin da ake kagowa zamu ga suna taBa mutunci da darajar annabi da nuna rashin falalarsa kan wasu mutane ko ma kaskantar da shi kansu kamar yadda akwai daruruwan hakan a littattafan mutanen, sai dai gudun tsawaitawa ba zamu iya kawo dukansu ba.

Tsaga Kirji

Daga cikin abin da ya zo a Buhari da Muslim akwai batun tsaga kirjin annabi a lokuta daban-daban, lokacin da yake karami da lokacin da ya zama annabi (s.a.w). Muslim ya kawo shi a cikin babin yin Isra’i da annabi a j 1, h 163, haka nan masu rubuta tarihi sun kawo wannan lamarin, Anas mai ruwayar yana cewa yana ganin shatin tsagar a kirjin annabi (s.a.w). Da yawa mun samu masu fassara suna kawo cewa manufan ayar farko ta surar sharhi cewa: “Shin ba mu yalwata maka kirjinka ba” tana koma wa ga batun tsaga kirjinsa ne. Sai dai yana da kyau mu duba wannan ruwayar mu ga me ye yake gewaye da ita domin mu san rauninta da rashin ingancinta kamar haka:

1- SaBanin Zamani

SaBanin da ruwayoyin suka kawo game da tsaga kirji yana da yawa, domin wata ruwayar tana cewa yana yaro yayin wasa da sauran yara, wasu kuwa suna kawo cewa yana babba lokacin annabci da ya kasance bayan tsaga kirjin ne sannan sai aka yi sama da shi don yin mi’iraji.

2- SaBanin Wuri

Wata ruwayar tana cewa yana harami a Hujru Isma’il, wata ruwayar tana cewa yana kan hanyar daji, wata ruwayar kuwa tana cewa yana gidansa ne. Wata tana cewa an kawo ruwa a kwano daga rijiyar zamzam, wata kuwa tana nuna cewa yana gefen rijiyar zamzam. Zamu ga a fili yake cewa babu wani takaimaimai wurin da yake tabbatacce guda daya inda aka tsaga kirjinsa.

3- Karo da Isma

Wani babban lamarin da zai raunata wannan ruwayar shi ne kasancewa manzon Allah (s.a.w) ma’asumi ne, ba shi da bukatar fitar da rabon shedan daga gare shi domin shedan ba ya yin tasiri a kansa, kuma hadisin cire rabon shedan daga gare shi kai tsaye ya saBa da ismarsa don haka ya rushe ke nan.

4- Sharri da Tsoka

Sannan kasancewar mutum ya kasance mai sharri ko maras sharri, mutumin kirki ko maras kirki, ba shi da wata alaka da tsokar zuciya balle cire wani abu ya yi wa mutun tasiri wurin gyaruwa ko lalacewa. Idan da za a canja wa mutum mai imani da Allah zuciya a sanya masa ta wani mutum maras imani da Allah babu wani tasiri da hakan zai yi masa. Haka ma zuciyar mai kyawun hali da maras hali nagari, ko zuciyar malami da jahili, ko na wata kabila da ta wani dan kabilar, babu wani tasiri da zata yi. Don haka batun a cire rabon shedan domin ya kasance ya samu yalwar kirji ko nisanta daga shedan babu wata ma’ana ga hakan.

5- Anas Kawai

Sannan don me ya sa kawai Anas ne zai ga tabon tsagar kirjin ban da sauran matan annabi (s.a.w), da ‘yarsa sayyida Zahra (a.s), da matarsa Khadija, da sauran matansa. Yaya kawai Anas ne yake ganin kirjinsa ban da sauran mutane da suka fi kowa kusanci da shi. A yanzu wannan zai zama karBaBBe a hankalce da al’adance da ilmance!.

Ma’anar Yalwar Kirji

Ma’anar yalwar kirji a bisa zahiri ita ce ta jawo kirkiro wannan ruwayar sai aka yi amfani da wannan ma’anar kamar yadda aka yi amfani da sauran wurare don haifar da shedanar umayyawa ta neman rusa annabin Allah (s.a.w) domin su nuna shi ma ba don an tsaga tasa zuciyar an fitar da wani rabon na shedan ba, da babu wani abu da zai bambanta shi da su da kuma sauran mutane, da shi ma ya yi saBo kamar sauran mutane, don haka ke nan suna da uzurin nasu yin saBo saboda ba a tsaga tasu zuciyar ba. Wannan ce mummunar natijiar da umayyawa suke son su cimma.

Idan mun duba a fili zamu ga addu’ar annabi Musa (a.s) da yake cewa: “… Ubangiji ka yalwata mini kirjina …”, da sauran ma’anoni irin wadannan da suka zo a Kur’ani mai daraja babu wata ma’anar tsaga kirji cikin wannan addu’ar. Da ya kasance ma’anar yalwar kirji tana nufin a tsaga kirji da wannan addu’a tana nufin Allah ya tsaga kirjin mai yin ta ke nan lamarin da zai kasance ba shi da wata ma’ana. Balle ya kasance rokon hakan ya zo daga shugaban masu hankalin duniya irin annabi Musa (a.s).

Ruwayoyin Tsaga Kirji

Ruwayoyin tsaga kirjin annabi (s.a.w) sun zo da yawa a littattafan Hadisi da tarihi a wurin ‘yan’uwanmu ‘yan Sunna, sai dai lamari ne da malaman Shi’a suka kasu gida biyu kansa, wasu suka yi shiru kansa wasu kuma mafi yawa suka yi inkarinsa saboda abubuwan da suke gewaye da shi, musamman ma da yake babu wani abu da ya zo daga Ahlul-baiti da yake nuni da faruwar wannan abun, alhalin sun yi bayanin mafi karancin muhimmin abu game da rayuwar annabi (s.a.w). Da ya kasance yana da inganci da sun yi nuni da hakan.

Wasu kuwa sun yi kokarin kawo cewa ko dai ana nufin tsaga kirji na ma’ana da yake nufin yalwar ilimi da hakuri da juriya da mutane. Sai dai, da haka hadisin yake nufi da babu maganar an kama shi har yara sun gudu sun gaya wa Halima kuma an dawo an same shi cikin wani mummunan hali. Sannan da haka yake nufi da Anas bai ce yana ganin kufan tabon tsaga ba a kirjin annabi (s.a.w).

Kokwanton Annabta

Daga cikin mafi munin dukan da Musulunci ya sha a hannun umayyawa da malamansu musamman kiristocin da suka musulunta kuma suka ba su damar bayar da karatu da fatawa da ruwaya akwai mas’alar nan da take nuni da cewa Annabi (s.a.w) ya yi kowanton annabcinsa[2].

Ruwayar tana cewa manzon Allah (s.a.w) ya fara da ganin mafarki kusan wata shida ne, kuma duk sa’adda ya ga mafarki sai ya kasance kamar wayewar gari wato sai ya tabbata da safe. Sannan kuma sai marhalar zuwa mala’ika a kogon Hira da saukar wahayi da matsar da mala’ika ya yi masa da firgicin da ya samu, har ya dawo gida yana neman a lulluBe shi, sai matarsa ta kwantar masa da hankali, ta lulluBe shi kamar yadda ya nema amma ya ci gaba da ganin mala’ika, ta bude gashin kanta sannan sai mala’ika ya gudu. Sannan sai ta kai shi wurin Kirista Waraka dan Naufal daga cikin jikokin Abdul’uzza wanda shi ne ya kwantar masa da hankali ya nuna masa cewa mala’ikan da yake zuwa ga Musa (a.s) da Isa (a.s) ne ya zo masa, don haka sai tsoronsa ya kawu, kuma ya koma yana neman mala’ika ya zo masa sakamakon maganar Kirista Waraka wanda ya ci burin a ce yana raye don ya taimaki annabi sakamakon wahalar da zai sha daga mutane. Annabi ya tambaye shi wace wahala kuwa? Sai ya gaya masa cewa: Ai babu wani mutum da zai zo wa al’umma da irin abin da ka zo da shi sai an yake shi. Wannan kissara a takaice ke nan.

A ruwayar Tabakat daga Ibn Sa’ad[3], ya ruwaito cewa annabi (s.a.w) ya yi tsammanin shi boka ne ko mahaukaci. Yayin da Tabari[4] ya kawo cewa annabi ya yi tsammanin shi hauka ya same shi ko ya koma mawaki sakamakon saukar surar Alaki gare shi, kuma ya kasance mawaki ne mafi munin mutum a wurinsa, don haka ne ya so ya kashe kansa, sai da ya hau kan dutse domin ya jefo kansa sai ya ji wata murya tana cewa: Ya Muhammad! Kai annabi ne!.

Raddin Ruwayar

Yawancin raddin da za a yi wa wannan ruwayar yana komawa zuwa ga Buhari da Muslim ne da su suka dauke ta a matsayin ingantaccen abu:

1- A yanzu zai yiwu Allah ya aiko mafi darajar annabawansa amma bai nuna masa cewa annabci ba ne karara sai ya sanya shi shakkun cewa shin hauka ne ya same shi ko bokanci, har ma ya nemi kashe kansa daga karshe! Lallai wannan yana daga mafi munin abin da malaman Shi’a suke kyamarsa saboda rusa asalin wahayi da annabta da ya kunsa. Tare da abin da yake nufi na rusa kimar annabi (a.s).

2- Ta yaya annabawan da suka gabata hatta da wadanda suke annabawa tun suna yara kamar annabi Isa (a.s) suka san cewa su annabawa ne kai tsaye, sai fiyayyen halitta ne shi zai shiga kokwanto bai san cewa shi annabi ba ne, ko boka, ko mahaukaci.

3- Yaya aka yi ya kasa gane annabcinsa sai ta hanyar wani Kirista wanda zai nuna masa hanya, ashe ke nan shi wannan kiristan ne ya fi cancanta da annabta ba shi ba. Haka nan matarsa ma da ta fi hikima da nutsuwa fiye da shi ita ce ta fi cancanta da annabta fiye da shi.

4- Nuna cewa annabi ba ya fahimtar abubuwa da wuri ta yadda ya kasa ganewa har sau uku, mala’ika yana cewa da shi karanta amma yana cewa ni ba mai karatu ba ne. Yayin da mala’ika yake karanta masa yana nufin ya karanta shi ma abin da ya ke karantawa. A ciki akwai muguntar cewa annabi bai fahimta ba sai a na uku, wannan kuwa ya saBa da sha’anin matsayinsa mai daraja.

5- Me ake nufi da matsar da Jibril yake yi masa haka yana cutar da shi babu wani dalili, don me ya sa zai cutar da shi? Me ya sa zai Bata masa rai, kuma me ya sa sauran annabawa ba a yi musu hakan ba.

Kuma wurin masu wannan ruwayar don me ya sa ba a ba wa annabi karfin da aka ba wa Musa (a.s) ba yayin da ya mari mala’ikan mutuwa wanda daga nan ne mala’ikan mutuwa ya gudu ya ji tsoronsa bisa wata kissa maras tushe da ta zo a Littattafan Sunnawa bisa dasisar Umayyawa. Ya kamata su ba wa Annabi (s.a.w) wannan karfin shi ma ya mari Jibril (a.s) don ya ji tsoronsa ya gudu. Sai ya zama a daidai lokacin da mala’ika ya ke jin tsoron Musa (a.s), amma shi manzon rahama ne yake jin tsoronsa!. A cikin wannan lamarin akwai rashin adalci mai ban al’ajabi ga annabin daraja da daukaka!.

6- Babban hadafi shi ne bayar da uzuri ga halifofi da sauran masu mulkin da suka ba wa kiristoci damar bayar da ilmi da koyarwa a cikin masallatai domin a nuna wa al’umma cewa annabi ma ya koma wurinsu yayin da ya rasa yadda zai yi, har sai da ya samu amsa gamsassa a wurinsu. Kuma wannan yana iya zama wata shimfidar da za a taka don samun wani abu sama da hakan wanda yake kunshe da hadafofi masu hadarin gaske.

A yau mun ga yadda makiya annabin Allah suka yi amfani da wannan kissa wurin jingina rashin hankali ko farfadiya ga fiyayyen halitta, da ba wa malaman Kiristoci kima ta musamman a matsayin makomarsa yayin da bala’i ya fi karfinsa.

Kuskure a Salla

Bahasin rafkanwar annabi (s.a.w) a salla yana daga cikin abin da aka ruwaito a cikin Buhari da Muslim, wannan lamarin ya saBa da ismar annabi da kasancewarsa mai samun kariya daga rafkana daga Allah madaukaki. Ba zai yiwu annabi ya yi mantuwa ko rafkanwa ba ta yadda salla mai raka’a 4 zai yi ta da raka’a 2, ko saBanin hakan, wannan yana saBa wa da kasancewa ba ya gafala.

Buhari ya nakalto wannan lamarin a ruwayar Abuhuraira daga kitabus salat, babin “Tashbikul asabi’i fil masjid”, da babus “Sahwi fis salat” da sauransu cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya yi rafkanwa a cikin salla har sahabbai suka kasa yi masa magana saboda abin ya yi musu nauyi, sai Zulyadain ne ya iya yin magana yana tambayarsa cewa ya ma’aikin Allah ka yi mantuwa ne ko kuma an rage salla ne?. Sai manzon Allah (s.a.w) ya yi nuni da cewa ba a rage ba kuma ban yi rafkanwa ba. Bayan Zulyadain ya dage ne sai ya tambayi sahabbai ko Zulyadain ya yi gaskiya sai sahabbai suka ce haka ne ya yi gaskiya. Sai manzon Allah (s.a.w) ya sake yin wani sahun ya yi kabbara suka yi raka’a biyu, suka yi sallama, sannan sai ya zo da sujadar rafkanwa. Idan mun duba wannan ruwayar zamu ga;

1- Wannan ruwayar tana nuna mana cewa annabi (s.a.w) bai fi karfin shedan ya zo masa ba cikin salla har ya sanya shi yin rafkanwa, wannan ya saBa da ismar annabi (s.a.w) mai daraja da daukaka da zaBi wurin Allah (s.w.t).

2- Me ake nufin da fushin da manzon Allah (s.a.w) ya yi har ya sanya wasu ‘yan yatsu cikin wasu saboda fusata yana mai jingina da wata bishiyar a wajen masallaci yana mai sanya hannunsa na dama kan na hagu. Abuhuraira ya nuna yadda komai ya gudana da yake nuni da cewa yana wurin.

Abin mamaki a nan Zulyadain da aka fi sani da Zusshimalain ya yi shahada a Badar kafin Abuhuraira ya musulunta da kusan shekaru biyar ke nan. Wannan lamarin yana da ban mamaki ke nan, yaya Abuhuraira kawai ya san wannan ya faru, yaya ya ji magana daga mutumin da bai taBa gani ba kawai ya ji labarinsa ne!.

A fili yake wannan ruwayar ta kasance kage ce ke nan!.

3- Sannan ya ya sallar da ta Baci sai kuma a zo a karasa ta maimakon sake sabuwa!. Mun sani cewa idan mutum ya yi abin da yake Bata salla to babu batun kuma gyara, a nan sai dai ya sake ta. Wannan ya zama jingina jahilci ga fiyayyen halitta ke nan ta hanyar nuna cewa shi ya zo da hukuncin salla amma shi kuma bai san hukuncin ba.

4- Yanayin da aka nuna annabin rahama a wannan ruwayar ya saBa wa matsayin annabi (s.a.w), mance rabin salla ya yi hannun riga da matsayin mafi kamalar halittun Allah wanda babu wani abu da yake iya shagaltar da shi daga ubangijinsa ko da kiftawar ido balle kuma a salla har ya mance da raka’o’i har biyu.

5- Wannan ruwayar ta rusa manzon Allah (s.a.w) ta nuna wa duniya shi a matsayin mai yin karya da musu!  a daidai lokacin da aka nuna cewa ya musanta kuskurensa kuma ya nuna bai manta ba, kuma ba a rage salla ba, sai ga shi kuma a lokaci kankane ya karBi cewa ta ragu da rafkanwarsa!. Wannan lamarin ya yi muni game da matsayin annabi mai daraja, hatta da mutane masu karancin daraja ba zasu yi irin wannan halin ba balle kuma fiyayyen talikai.

Wannan lamarin a fili yake nuni da cewa wannan ruwayar akwai warin umayyanci cikinta da suka yi kokarin karanta darajar annabi ta kowane hali da shaidanar da babu masu gane ta sai masu hankali da ilimi daga tsatson annabin rahama.

Salla da Janaba

Yin salla da janaba yana daga cikin mafi munin abin da aka jingina wa annabi (s.a.w).

Buhari ya kawo ruwayar Abuhuraira da ke babin fara kiran salla, Muslim kuma ya kawo ta a babin mai janaba da yake salla da mutane yana mai mantawa cewa: Annabi (s.a.w) ya fito yana mai janaba zai yi salla da mutane, har sai da ya fito zai tayar da salla sai ya ce da su ku dakata a wurinku. Sai ya shiga ya dawo jikinsa yana zubar da ruwa saboda wankan da ya yi na janaba, sai ya yi kabbara ya yi salla limanci gare su.

A littafin Umdatul Kari[5] Badruddin yana cewa: Wannan ruwayar tana nuna cewa annabawa ma suna iya yin mantuwa cikin ibadarsu.

Abin mamaki duk da cewa wannan ruwayar tana da mummunan sakamako a akida, kuma babu wanda ya ruwaito ta sai Abuhuraira da Abubakar, amma ‘yan’uwanmu sauran musulmi masu bin tafarkin ‘yan Sunna sun dauki ruwayar a matsayin ingantaccen abu ba tare da duba zuwa ga hadarinta a akidar musulmi ba.

Idan aka ba wa annabin Allah wannan mummunar siffa to fa kokwanto ya shiga baki dayan addini ke nan, domin zamu samu tambayar cewa matukar yana mantuwa ya gafala to me zai sanya mu samu nutsuwa da shari’a cewa da yawa a wasu wuraren ko ya yi mantuwa ko gafala ne.

Sakamakon cewa manzon rahama ya bar mana littafin Allah da alayensa ne a matsayin wasiyyar da zamu bi bayansa, kuma tun da su alayensa satsonsa sun barranta da irin wadannan ruwayoyin sun kore masa su, to mu ma mun kore masa wannan shirmen kuma muna tare da alayensa masu daraja.

La’anar Muminai

Abuhuraira yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ya Allah! Ni mutum ne kamar sauran mutane da nake fushi, kuma ni na yi alkawari da kai wanda ba zan karya ba, don haka duk wani mumini da na cutar ko na zaga, ko na la’anta, ko na dake shi da bulala, to ka sanya wannan aikin ya zama kaffarar kurakuransa da kusanci da kai[6].

Abin mamaki wannan ruwayar wani lokaci Buhari ya kawo ta a babi mai zaman kansa da sunan “Babin wanda annabi ya la’ance shi bai cancance ta ba”.

Haba mai ruwaya! A yanzu wannan lamarin ya inganta daga wurinka cewa annabi (s.a.w) zai yi wannan ayyukan da duk wani mai takawa da hankali ba zai iya yin su ba balle annabin Allah!?. Sai dai mun san umayyawa sun yi duk wadannan abubuwan, don haka suke son nuna annabi (s.a.w) a matsayin wani mutum ne irinsu don haka ba su da wani laifi ke nan. Wannan ita ce siyasar kawai!.

Yayin da aka yi mamakin maganar Abuhuraira sai aka tambaye shi cewa: Shin ka ji wannan daga annabi (s.a.w) kuwa?. Sai ya ce: Wannan daga jakar Abuhuraira ne. A nan ma ba zamu iya ganewa ba ko wannan ma daga jakarsa ce. Idan mun duba wannan ruwayar zamu ga tana da hadarin gaske ta wasu fuskoki da suka hada da cewa:

1- Ta nuna cewa Manzon Allah (s.a.w) mutum ne da ba shi da bambanci da sauran mutanen masu rafkanwa da saBo irina da irinka (wal’iyazu bil-Lah!), don haka ke nan ba shi da wata kima da daraja sama da ni da kai.

2- Yana fushi ba tare da wani hakkin shari’a ba sai ya cutar da musulmi, ya zage su, ya la’ance su, ya doke su. Wannan halin bai dace da irina da irinka ba, balle kuma manzon Allah (s.a.w) mai daraja. Don haka irina da irinka da suke sanya hankali a magana don su tantance ke nan sun fi shi daraja da hankali (wal’iyazu bil-Lah!) mahallin kuka!.

Wannan mummunar sifa ta nisanta daga manzon Allah (s.a.w) kuma ya barranta daga gare ta, ta ci karo da Kur’ani mai girma da ya yabe shi da tsananin tausayi ga muminai da siffofi madaukaka. Ta ma ci karo da abin da ya zo a Buhari kansa a jildi na takwas, babin “Adab” da cewa: “Annabi bai kasance mai alfasha ko mai yin alfasah ba. Hada da cewa hatta da yahudawa zamu ga yayin da uwar muminai A’isha ta tsananta musu a magana sai da ya hana ta, ya nuna mata ba ki ji ni raddin da na yi musu ba!, tare da cewa fa yahudawan sun gaya masa bakar magana ne da sunan gaisuwa!.

Idan halinsa ya kasance kamar haka ne ga wanda ba musulmi ba, ina ga musulmi da Allah ya yi masa shedar cewa shi mai tsananin tausayi ne gare su. Kai yana kusa kashe kansa ma saboda tsananin bakin ciki don kafirai ba su yi imani ba alhalin yana ganin imani ne shiriyarsu da tsiransu balle muminai.

3- A wurare da yawa Muslim da waninsa ya nakalto cewa hatta la’anar dabbobi ko zaginsu manzon Allah (s.a.w) ya hana da hani mai tsanani. Yana hana hawa dabbar da aka la’anta ko cin namanta[7]. Ga kuma shaidar da ya yi wa kansa a Muslim din a wannan babin dai cewa: Ni ba a aiko ni mai la’ana ba, sai dai an aiko ni ne don rahama.

4- Idan mun yarda cewa duk abin da manzon Allah (s.a.w) ya ke yi daga wahayin Allah ne, kuma wannan shi ne akidar da Allah ya saukar mana, ke nan ko dai ya kasance bai yi la’anar da zagin ba wanda yake shi ne batun gaskiya. Ko kuma ya kasance ya yi sai ya zama da umarnin Allah ne ke nan. Don haka idan ya kasance ya yi da umarnin Allah ne in mun kaddara hakan ya faru to don me ya sa zai kasance isar da sakon Allah da ya yi ya zama zunubi gare shi.

Don haka duba zuwa ga wadannan abubuwan lura, babu yadda za a yi manzon rahama (s.a.w) mafi kamalar halittar Allah ya kasance da wannan mummunar sifa.

Dalilin Ruwayar

Babu wani dalili kan kago wannan ruwayar sai bayar da kariya ga Mu’awiya da babansa da dan’uwansa da manzon Allah ya tsine musu lokacin da babansu yake hawan rakumi danyansu yana ja dayansu kuwa yana korawa, da kuma sauran Banu Umayya makiya Allah munafukai da suka musulunta don kare rayukansu ko rusa Musulunci ta ciki. An kirkiro irin wannan don a kare Mu’awiya daga mummunar addu’ar da annabi ya yi masa cewa: “… ka da Allah ya kosar da cikinsa…”[8]. Sannan kowa ya san wannan addu’ar da annabi ya yi masa ya yi masa ita ne saboda annabi ya kira shi ya zo har sau uku amma ya ki zuwa da sunan cewa wai yana cin abinci ne.

Idan ka ce: A nan ke nan Hadisin Abuhuraira ya zama gaskiya domin manzon Allah (s.a.w) ya yi wa Mu’awiya addu’a mummuna ke nan kuma shi ma musulmi ne.

Sai mu ce: Annabi (s.a.w) bai taBa yarda da cewa musuluncinsu na gaskiya ba ne, kuma ya kira su da munafukai, da tulaka’, da fi’atul bagiya, kuma shajara mal’una (bishiya la’ananna) kuma duk wannan da umarnin Allah ne, don haka babu batun ya yi zagi, ko la’ana, ko dukan musulmi ba bisa hakki ba ke nan!.

Annabi (s.a.w) ya kira Mu’awiya da  jagoran jama’a azzaluma da zata kashe Ammar dan Yasir. Ya kira babansa, da shi, da wansa Yazid yayin da yake jan rakuma, Abusufyan yana kanta, wansa Yazid yana turawa da cewa: Allah ya la’anci mai hawa, da mai ja, da mai turawa. Haka nan ma zamu ga sauran umayyawa sun samu wannan la’anar, saboda Allah ya ba wa annabinsa umarnin hakan, kuma ya isar wa musulmi. Kuma ya yi umarni ga musulmi idan kuka ga Mu’awiya kan mimbarina ku kashe shi. Sai dai musulmi ne suka takaita da ba su yi ba, sai ma suka bi shi a matsayin halifan annabi (s.a.w), ya kashe duk wani mumini a zamaninsa. Bahasi ne mai tsawo sai ku koma wa tarihi!.

Wannan ruwayar ce ta bayar da lasisin rusa annabi (s.a.w) don kariya ga Mu’awiya kuma da man wannan ne hadafin ruwayar. Kuma ku duba me suka ce kan wannan lamarin:

1- Muslim, da kuma fadin Ibn Hajar Makki cewa: Mummunar addu’ar da annabi (s.a.w) ya yi wa Mu’awiya falala ce gare shi ba suka ba ne, domin Hadisi ya zo cewa duk wanda manzon Allah (s.a.w) ya la’ana kuma bai cancanta ba, to wannan zai zama masa gafara da kusanci da Allah[9].

Sai dai tambaya ga Ibn Hajar, shin kana shirye kai ma kuma kana son annabi (s.a.w) ya la’ance ka domin hakan falala ce?. Ko kuma ka yarda duk wata la’ana da ya yi wa mu’awiya ta same ka, ko ta koma kanka?.

2- Shamsuddin Zahabi[10] ma ya soki Nisa’i saboda Nisa’i ya soki Mu’awiya kan cewa manzon Allah yayin masa mummunar addu’a. Sai Zahabi ya ce: Wannan ni a wurina falala ce ga Mu’awiya, sai ya kawo wannan hadisin ya kare Mu’awiya da shi.

3- Hakan nan dai zamu ga Ibn Hajar Makki ya sake kare umayyawa kamar Hakam da dansa Marwan da annabi (s.a.w) ya la’ance su, kuma ya haramta musu shigowa yankin Hijaz ko bayan mutuwarsa, amma Usman dan Affan yana zama halifa sai ya dawo da su ya mika musu ikon baki dayan dukiyar al’ummar musulmi.

Sai Ibn Hajar yake cewa su ma wannan la’anar da annabi ya yi musu duk falala ce, saboda annabi mutum ne kamar kowa yana fushi yana la’ana babu wani hakki, kuma duk wanda ya la’ana to gafara ce gare shi[11].

A nan nake cewa: Ibn Hajar Makki ka yarda ka dauki irin wannan la’anar tasu kai ma ko kuwa?, idan a shirye kake da daukar irin wannan la’anar to Allah ya isar da ita gare ka?!.

Sannan kuma idan annabi kamar sauran mutane yake don me ya sa ka yarda da annabtarsa har ka karBi maganarsa kana kafa hujja da ita a cikin rubuce-rubucenka?!.

Yaya zaka ce game da ayar nan da take cewa: “Ba ya maganar son rai, sai dai wahayi ne aka yi masa”. Idan ka yi imani da wannan ayar to dole ne ka yarda cewa la’anar Mu’awiya da sauran umayyawa umarnin Allah ne, in kuwa ba ka yi imani da ita ba to ka kafirce wa littafin Allah ke nan!.

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com

 

[1] Biharul Anwar: j 15, s 144.

[2]  Wannan hadisin ko mu ce ruwayar Buhari a babin farawar wahayi j 1, da j 4, h 3066, da sauran wurare kamar kitabut Tafsir. Haka ma Muslim: a babin farawar wahayi; j 1, h 160. Da sauran littattafai masu yawa gun ‘yan Sunna masu naqalto wannan ruwayar.

[3] j 1, shafi 129-130.

[4] j 3, shafi 1142.

[5] j 5, s 156

[6] Duba Buhari: j 4, kitabud da’awat; h 6000. Da Muslim: j 8, kitabul barri wassila, h 2601.

[7] Muslim: J 9, kitabul barri; babin hanin la’anar dabbobi, h 2595 – 2596.

[8] Muslim: j 8, kibatul barri; “babu man la’anahun nabi wa laisa ahlan li zalik” h 2599.

[9] Tathirul jinan, a hashiyar sawa’iqul muhriqa: s 59.

[10]  Tazkirtul Huffaz; j 2, s 699.

[11] Sawa’iqul Muhriqa: s 108.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

3 comments

  1. Allah yashiga stakaninmu da shi’a, daman yahudawane da nasu makircin kuma jahilai, kafurai Suka kirkirota, Dan tozarta Manzon Allah, to dik Wanda Yabiye masu ya tabe, tabewa ta har abadan

    • Da zai yi kyau ka fadi yadda yahudawa suka kirkiro biyayya ga littafin Allah na Kur’ani da alayen annabin rahama (S)?.

    • Yana da kyau ka san me ake nufi da shi’a kafin ka ce Allah ya shiga tsakaninka da ita, domin biyayya ga Ahlul-baiti da kaunarsu da son su ne ake ce wa shi’anci. Manzon Allah (s) ne ya zo da wannan a matsayin kamalar addininsa. Duba tafsirai ka ga albishir din da Annabi (s) ya yi wa shi’awann Ali (s) karshen surar Bayyina. Allah ya shirya mana al’ummarmu ya taimaka mata wurin kawar da son rai da jahilcin da yake damun ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *