Mummunan Zato

Haske da duhun rayuwa

Rayuwar mutum gaurayen zuma da madaci ce. Kowane daya daga cikin wahala da nishadi kan iya daukar wani bangare na rayuwar dan adam a wannan duniyar. Kowane mutum ya kan dandani daci da zakin rayuwa kuma ya kan zamo abin farautar su saboda mishkilolin rayuwa da masifun ta. Wannan shine hakikanin al’amari mara dadi wadda rayuwar mtum take kaiwa da komowa a tsakanin wahala da jin dadi daidai dashi.

Mu ba zamu iya jirkita wannan tsarin rayuwa na tun fil azal har ya zamo ya dace da yadda ran mu ke so ba. Amma bayan mun gane hakikanin wannan rayuwa zamu iya mai da hankalin mu akan kyawawan abubuwan ta kuma mu kau da kanmu daga munanan al’amuran ta. Duk zamu iya yin haka a wannan yalwataccen fage wanda ke cike da kyau da hikima wanda kuma ya hada kome da kome na tausasawa ta musamman wadda aka halitta musamman saboda shi. Ko kuma muna iya juya baya mu mance da al’amuran rayuwa masu haske da haskakawa mu fuskanci al’amura masu duhu da muni kawai a rayuwa. A takaice dai kowa soja ne, malamin kan sa kuma yana iya fuskantar da fikirar sa zuwa duk kusurwar da yaso kuma yana iya rina rayuwar sa da duk irin launin da ya ga dama.

Wajibi ne a kan mu, muyi shiri dan fuskantar duk abin da bai dace damu ba wanda yake toshe mana hanyar rayuwa, domin kada mu kasa kintsa kanmu a rayuwa. Idan kuwa ba haka ba to zamu yi kazamar hasarar da ba za mu iya murmurewa ba, mai yiwu wa ne ma mu durkushe a gaban gaggan al’amuran rayuwa.

Mai yiwu wa ne wasu suyi tsammanin cewa idan har dai al’amura sun kasance suna gudana ta wata fuska dabam, to da sun ci nasara, alhali kuwa ba anan take ba. Babu abin da ya hada rashin nasarar su da yadda al’amura ke faruwa, illa iyaka dai ya shafi yadda suke fuskantar al’amuran ne. Irin hanyar da mutum ya bi ta kan iya samun tasiri a ruhin sa har ta canja shi, hasali ma zai iya cin nasara ta wannan hanyar.

Wani daga cikin fitattun marubuta yace:

“Tunanin mu da’iman yana juyawa ne a tsakanin kiyayya da rashin gamsuwa. Duk halin da muke ciki, sai munyi gunaguni, mun koka kuma mun aibata. Dalilin wannan kuka da gunaguni kuwa a zukatan mu yake. Mu an halitta mu ne ta yadda duk wani abu da bai dace da jikkunan mu da ruhin mu ba, zai azabtar damu. Kullu yaumin ka gan mu, muna buri muna sa rai ga sabon abu sau da yawa ma bama fahimtar abin da muke so. Tsammani muke yi wasu har sun riga sun ci nasara har muke hassada gare su ko muke yi musu kyashi muna azabtar da kanmu. Mu kamar shagwababben yaro muke, wanda zai kakalo kuka babu gaira babu dalili ay yi ta rusawa, ran mu in ya yi dubu sai ya baci saboda kuka da kururuwar wannan yaro. Ba za a huta daga kururuwar wannan yaro ba, har sai mun sa shi ya gane hakika, alhali a da babu abin da ya sani illa shirme, sai mu hana shi shirmen da zuciyar sa ke so, domin saboda abin da zuciyar sa ke so ne, ya zama baya ganin wani abu illa mummuna.

Dan haka wajibi ne mu bude idonsa ya ga bangaren alherin wannan rayuwa. Wajibi ne mu fahimtar dashi cewa wanda ya bude idonsa ya duba lambun wannan rayuwa, zai ci nasarar tsinkar furanninta. Wanda kuma ya makance, to babu abin da zai samu illa kayar lambun. Idan muka kau da kanmu daga tsanani da mummunan zato, muka duba da idon basira zamu gane cewa, a kowane zamani, hatta a wannan zamanin namu da ya kama hanyar lalacewa, wanda kuma a kowace sa’a guda, rayuwarmu take yin juyin waina a cikinsa, lafiyayye da majinyaci kuma suke cudanya, nagari da mugu kuma suke cakuda, za mu ga cewa a ko’ina cikin lambun wannan rayuwa akwai furanni masu jan hankalin masu kallonsu a kowane zamani”.

Tunani yana da tasiri mai zurfi a samun sa’adar mutum. Hasali ma abu daya kawai da yake da tasiri a sa’adar mutum shine karfin hankali da zurfin tunanin sa. Bakon al’amari wanda ba a saba da shi ba, babban bala’i ne gagara juriya a gurin mai mummunan zato. Amma mutum mai yiwa rayuwa kyakkyawan zato, sia ya yiwa al’amarin zaton alheri. Shi ba ya kasa yin gwagwarmaya kome tsananin masifa da bakin ciki, ba ya ketare haddin adalci da daidaito da kame kai da hakuri.

Wadanda suka yi imanin cewa su karfa ne, kuma kwawanyar sharri ta kewaye su dan ta auka musu, to ba zasu taba rayuwa ba illa cikin kunci da tsanani da duhu, kuma a al’amura da yawa za suyi hasarar kuzarinsu da kwazon su a banzar-bazara. Da sannu babu saninsu za su mance da duk wasu baiwa da albarkatun wannan duniya wadanda suka kewaye su.

Wani masani yana cewa:

“Duniya da mutum, cin tuwon kishiya suke yi, duk abin da ya yi mata shi zata yi masa, idan kayi mata dariya za ta dara maka, idan ka turbune mata ta turbune maka, in kayi aiki da tunani sai ta sada ka da masu tunani, in kai mai rangwame ne, mai abota za ka sami mutane kewaye da kai masu kaunar ka, sun bude maka abin da ke zukatansu na taskokin kauna da soyayya”.

Ko da yake a zahiri tsanani wani ciwo ne mai radadi amma yana da sakamako na musamman ga ruhi da tunani. Kwazon ruhin mutum ya kan bayyana sosai da sosai a lokacin da yake cikin tsanani. Hankali da ruhin mutum su kan kammala ne a cikin halin sadaukar da kai mai dorewa, da yin kokari da’iman da kuma kaiwa da komowa har su kai ga kololuwar kamalar ‘yan Adamtaka.

Illolin Mummunan zato

Mummunan zato yana daya daga cikin cutukan ruhi masu hatsari. Shine tushen kowace hasara da bata da fandarewa da tabewa. Shi sharri ne mai ciwo mai azabtar da ruhin mutum. Mummunan tasirin sa kuma baya gushewa daga mutuncin mutum.

Radadi da bala’i abubuwa ne masu saurin taba zuciya wadanda zai yiwu su haifar da mummunan zato saboda tunzura da harzukar zuciya.

Irin mummunan zaton da ke kankama a tunanin mutum ta wannan hanyar yana yin tasiri mai muni a zuciyar mutum, wanda ba a amince da shi ba.

Duk wanda madubin ruhin sa ya dunane da kurar mummunan zato, ba zai taba ganin kyawun halitta ba. Ba ma wannan kadai ba, hatta alheri ma zai bayyana a gare shi a halin an jirkita kamanninsa, ya zamo cuta da fandarewa, kuma ba zai taba iya ganin kyawun aikin kowa ba saboda mummunan zatonsa. Duk wadanda tunaninsu ya rikide ya zamo na sharri, to babu wani kazar-kazar na alheri da zai saura a gare su. Su ne da son ransu suke haifar wa kawukansu irin mishkilolin da suka so kuma suke dakushe kwazonsu da tuntuntuni game da al’amuran da ba su auku gare su ba tukuna, kuma mai yiwu wa ba za su taba aukuwa gare su ba.

Kamar yadda tasirin kyakkyawan zato da hali nagari ke yaduwa su shigi wanda yake kusa, ya raya ruhin kyakkyawan zato a zuciyar sa, to hakanan mummunan zato ya kan harbi na kusa ya zuba masa zugi da radadi da firgita, kuma da sannu zai raba shi da hasken kyakkyawan zato wanda ke haskaka hanyar rayuwa ga masu tafiya.

Tasirin mummunan zato ba wai ga ruhi ya tsaya ba kawai, ga jiki ma ya kan yi tasiri har ya jinkirta warkewar cututtuka.

Wani daga cikin manyan likitoci yace:

“Yin jinyar mutum mai munana zato ga kowa da kome, yafi ceto wanda ya jefa kansa a rijiya da nufin kashe kansa, wahala. Bayar da magani ga wanda da’iman yake cikin kunci da damuwa a rayuwa kamar zuba ruwa ne a cikin tafasasshen man da ke kan wuta. Kafin wani magani ya yi amfani, babu makawa sai zuciyar marar lafiyan ta amince kuma ya nutsu”.

Wanda cutar mummunan zato ta kama shi za a gan shi kuru-kuru yana kauracewa da tsoron zama tare da jama’a. Saboda da irin wannan hali abin ki, da sannu zai wargaza irin shirin da ke zuciyarsa na ci gaba, kuma da sannu rayuwarsa za ta zama ba abar yarda ba. Mummunan zato na daya daga cikin abubuwan da ke sa mutum ya kashe kan sa. Kudirar aniyar kashe kai galibi ta kan tsiro ne daga mummunan zato dangane da rayuwa.

Idan muka duba halin da jama’a ke zama tare da juna a al’umma, za mu ga cewa yawancin abubuwan da ke aukuwa a junansu na rashin jituwa, mummunan zato ba tare da yin bincike da tunani bane yake jawo su. Duk da cewa su masu rauni ne wajen aunawa da hukumta al’amari, amma sai kawai su yanke wa wasu hukumci kafin ma su gane kai da gindin lamari, sai kawai su gaskata abu ba tare da lissafi ba, za a iya gane manufofin su ta irin maganganunsu. Wannan aibi mai girma ya kan jawo lalacewar hadin kai. Har ila yau ya kan hana mutane amincewa da junansu, ya bata dabi’unsu nagari hatta ruhinsu.

Da yawa kiyayya da gaba da juna masu cutar da jama’a da al’umma baki daya, mummunan zato sabanin hakika da gaskiya ne yake jawo su. Mummunan zato ya kan bazu a tsakanin kowane bangare na mutanen al’umma, wani lokaci ma har ya kan kama tunanin malamai da masana falsafa. A tarihin al’ummu daban-daban za mu sami wasu malamai sun yi mummunan kuskure saboda mummunan zaton su. Maimakon su amfani al’ummar mutum da ilminsu sai suka gina ra’ayoyinsu akan asasin suka da kididdigar aibobin tsarin halittar duniya, sai suka zubawa ruhinal’umma gubar wannan ra’ayi nasu da mandikinsu na kuskure, suka dinga kushe asasin kyawawan halaye da akida suna izgili da su. Tsoro da bakin cikin da wasunsu suke yi game da yawan jama’a da talauci da bala’i ya kai su hatta ga halatta duk wani abu mai yiwa zuriyar mutum barazana, sun halatta yake-yake da zubar da jini. Idan da mutane sun daka ta rawar irin wadannan, to da a yau ba a sami ko alamar ci gaban mutum ba.

Abul Ala Almauri yana daya daga cikin masana falsafa masu mummunan zato. Shi ya kasance yana ganin cewa rayuwa baki dayanta wahala da azaba ce, ya kuma kasance yana haramta saduwa da mata da haihuwa, domin wai zuriyar mutum ta kare, kada na baya su sha azaba. Yayin da yazo mutuwa sai ya yi wasiyya da a rubuta wasu baitoci daga cikin wakensa a kan kabarinsa kamar haka:

“Wannan shine zunubin Babana gare ni.

Ni kuwa ban yiwa kowa zunubi ba.

Gargadi

Alkur’ani ya bayyana karara cewa mummunan zato zunubi ne, kuma ya gargadi musulmi da suyi nesa da yi wa junansu mummunan zato.

“Ya ku wadanda suka yi imani, ku nesanci ywancin zato, domin wani zaton zunubi ne”. (surar Hujuratu: 12)

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:

“Jinin musulmi ga musulmi haramun ne, da dukiyarsa, da kuma yin mummunan zato game da shi”.

Sahih Muslim, Kitabul Birri, babi na 32, da Musnad Ahmad Juz’i na 2, shafi na 277, Juz’i na uku shafi na 491 da Tirmizi Kitabul Birri babi na 18.

Kamar yadda musulunci bai yardar wa wani haka kawai sarmadan ya dauki dukiyar wani ya bawa wani ba, kazalika ko kadan bai yarje wa kowa ya munana zato ga wasu ba tare da tabbatar da gaskiyar al’amarinsu ba. Ya zo a Nahul Balagha shafi na 174cewa Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Yanke wa wanda aka amince da shi hukumci a kan zato ba adalci ba ne”.

Har ila yau kuma ya yi kyakkyawan bayani a kan irin illoli da barna da cutarwa daban-daban da mummunan zato yake yi wa zuciya da ruhi, inda yake cewa:

“Ka kiyayi kanka da mummunan zato, domin mummunan zato yakan bata ibada kuma ya kan kara yawan laifi”.

littafin Gurarul Hikam shafi na 154

yin mummunan zato ga mutanen kwarai wani nau’i ne na zalunci. Inda yake cewa:

“Munana zato ga mai aikin kwarai shine mafi sharrin laifi, har wa yau kuma shine zalumci mafi muni”.

Littafin Gurarul Hikam shafi na 434

Aiki da mummunan zato a tsakanin abokai kuwa ya kan raunana dangantaka kuma ya kan zamo sanadin tabarbarewar abota da jawo yanke kauna. Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Duk wanda mummunan zato ya yi galaba a kan sa, to babu sauran zaman lafiya tsakanin sa da abokin sa”.

littafin Gurarul Hikam shafi na 698

Bayan kazamar illar da mummunan zato yake yi wa hali da rayuwar mai mummunan zaton, har ila yau ya kan iya shafar halaye da zukatan wasu mutane. Idan har aka yi wa wani zargi alhali bai ji ba bai gani ba, to wannan yana iya sa shi ya kufula ya kauracewa halayen kwarai ya fandare ya shiga fasadi da aikata miyagun ayyuka da rashin mutunci. Imam Ali (a.s) ya ci gaba da cewa:

“Mummunan zato yana bata al’amura sa’annan ya jawo ashararanci”.

littafin Gurarul Hikam shafi na 433

Mummunan zato da zargi sukan yi sanadinbacinayyuka kuma su jawo lalata da kaskanci.

Dr Marden ya rubuta cewa:

“wasu attajirai su kan yiwa barorin su mummunan zato har su zarge su da yi musu ‘yan sace-sace a kantunansu alhali kuwa ba haka ba ne. A karshe kuwa sai yaran nasu su tsiri yi musu satar kamar yadda aka zarge sun. Dalili shi ne domin mummunan zato ko da ba a furta shi da baki ba ya kan ratsa zuciya ya bata ta, har ya kai su ga yin satar”.

Littafin Pirozi Fikr

Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Ka kiyayi zargi a inda bai dace ba, domin yin haka ya kan sa cuta ga mai lafiya, kuma ya sa kokwanto ga wanda ba shi da aibu.”

Littafin Gurarul Hikam shafi na 152

Haka nan ya sake cewa wanda ya kamu da wannan cuta ta mummunan zato, to shi kam ya yi sallama da kwanciyar hankali.

“Mai kokwanto ba ya taba samun lafiya.”

Littafin Gurarul Hikam shafi na 835

Dokta Carl yace:

“Akwai wasu dabi’u wadanda suke raunana karkon rayuwa. Al’adar kushe kowane abu, da yin mummunan zato ga komai, kiciciyar halaye ce mai daddage zuciyar mutum har ila yau kuma tana iya bata ayyuka ta nakasa gabobi.”

Littafin Rah wa rasm zendegi.

Dokta Marden kuma yace:

“Mummunan zato ya kan taba lafiyar jiki kuma ya kan bata halayen kwarai. Lafiyayyiyar zuciya har abada ba ta tsammanin sharri, da’iman alheri take saurare domin ta san cewa alheri har abada ba ya shudewa. Sharri kuwa ba wani abu ba ne illa rashin alheri, kamar yadda duhu ba wani abu ba ne illa rashin haske. Saboda haka ku kama hanyar neman haske domin yana kore duhu daga zuciya.”

Littafin Pirozi Fikr

Mutumin da zuciyarsa ta cika da mummunan zato zai kasance yana tsoron mutane. Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Wanda ba shi da kyakkyawan zato zai kasance yana jin tsoron kowa.”

Littafin Gurarul Hikam shafi na 712

Dokta Farmar kuma ya ce:

“Duk mai kin bayyana ra’ayinsa ko furta abin da ke zuciyarsa a cikin taro alhali kowa yana bayyana manufarsa, da kuma wanda yake kin bin manyan titunan cikin gari, yake kauracewa matattarar jama’a dan tsoron gamuwa da ‘yan uwa da abokan arziki, ba wani abu ba ne yake sa shi haka ba illa wahami da mummunan zato.”

Littafin Raz khushbakhti.

Bacin rai da tsanani su kan taru su cika zuciyar mutum har su kai shi ga halin mummunan zato ba tare da ya yi la’akari ba.

Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Zukata suna da wasu mugayen kudurori wadanda hankula suke jin tsoron su.”

Littafin Gurarul Hikam shafi na 29

Dakta Haleem yace:

“Mutanen da ba su amince da kansu ba sun fi saurin harzuka. Dan tsananin da bai taka kara ya karya ba, sai ya damu, sa’annan su dinga tuna shi dindindin har sai ya yi musu illa kwarai ba tare da sun sani ba. Sai su zamo masu kunci ko dacin rai, ko masu mummunan zato, kuma ba za su iya gane sanadin wannan cuta da ta kulle zuciyarsu ba. Munanan ra’ayoyi masu cutarwa a boye suke a cikin zukatan mu, kuma ba sa bayyana a cikin sauki. A wani kaulin kuma, mutum a bisa dabi’a ba ya kaunar abubuwa marasa dadi. Dan haka ba ya son in ya mance da su ya tuno su. Amma makiyin boye, wanda ba zai bar kulla mana makirci da danyen aiki ba, sai ya yi ta juya zukatanmu da ayyukanmu da halayen mu yadda yake so. Sai mu dinga aikata wasu ayyuka ko fadar wasu maganganu wadanda suke ba mu al’ajabi domin mu da kanmu da kuma sauran jama’a mun san cewa ba a bisa tafarki suke ba. Idan muka koma cikin hankalinmu muka yi nazari sai mu gane cewa sakamakon munanan ra’ayoyinmu da ke kulle a cikin zukatanmu ne.”

Littafin Rushd shakhsiyyat

Mutum mai mummunar dabi’a da’iman ya kan sanya kansa ma’auni ne da zai dinga auna dabi’ar wasu kuma irin munanan halayen da yake da su yake gani a jikinsu. Imam Ali (a.s) yana cewa:

“Asharari ba ya zaton alheri ga kowa, domin ba ya ganin kowa sai da irin dabi’arsa.”

Littafin Gurarul Hikam shafi na 80

A lokacin da Manzon Allah (s.a.w) ya yi hijira daga Makka zuwa garin Madina sai wani mutumin Madina ya nufo shi ya ce masa: “mutanen garin nan mutanen kirki ne dan haka ya yi kyau kwarai da ka kaurato zuwa gurinsu.” Sai Manzon Allah (s.a.w) yace: “ka yi gaskiya.”  Daga baya kuma sai wani ya lallabo ya ce wa Manzon Allah (s.a.w): “mutanen garin nan masharranta ne, inama ba ka yiwo hijira ka zo cikinsu ba.”  Sai Manzon Allah (s.a.w) yace: “ka yi gaskiya.”  Sai wani sahabi ya tambayi abin da ya sa ya ce duka sun yi gaskiya. Sai ya ce: “kowane daya daga cikin su ya fadi yadda zuciyarsa take ne, dan haka kowannensu ya yi gaskiya.”

Abin nufi kowane daya daga cikin su ya fadi gaskiya ne game da abin da ke cikin zuciyarsa.

Ya kamata a gane cewa mummunan zato tabewar tunani ce da kuma kafewa a kai, abin da aka haramta a nan shi ne yin aiki da mummunan zaton. Domin tunani da wahami al’amura ne da ke cikin zuciya da kwakwalwa, mutum kuma ba shi da iko a kansu, kuwa ba shi da mafita kenan kuma babu wani takalifi game da su a shari’a.

Kamar yadda aka bayyana a can baya cewa wannan cuta tana sabauta kunci da rashin ribar rayuwa lalle a yi nazari cikin tsanaki dan a gano sanadinta. In har an gano abin da ke jawo mugun zato sai a magance shi ta hanyar sanadin.

KYAUTATA DABI’U

Sidi Mujtaba Musawi Lari

Fassarar: Yakubu Abdu Ningi

Editoci: Yusif Saleh Gwani da Muhammad Awwal Usman Kunya

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

***

Check Also

45-Halayen Imam Mahdi

  Kowane imami shi ne mafi kamalar mutane a zamaninsa, Imam Mahdi (a.s) shi ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *