Gyaran Jiki

Da farko miji da mata sai su kiyaye yin abin da junansu suke so, wannan yana fara wa tun daga shirya jiki, kamar yadda muka sani kowane mutum akwai yadda yake son jikinsa ya kasance, kuma mafi girman sirri na farko shi ne yadda mata suke motsa jikinsu gaban mazajensu ko yadda shi ma namiji zai yi wa matarsa. Alakar tana da bangare biyu ne ba kamar yadda mafi yawan marubuta suka sanya hankulansu kan bangaren mace ba. Kuma kowane mutum yana da abin da ya fi burge shi, don haka matakin farko shi ne ma’aurata su san me ye ke burge junansu sai su kiyaye shi. Wata matar dariyar mijinta ce muhimmi da yadda yake yi mata magana cikin sanyin rai, shi ma wani namijin haka yake, wasu ma’auratan sun fi son zaman hira, wani kallo ne yake burge shi, wata kuma yadda ma yake tafiya ya yi mata, wata kuma fagen iliminsa take son ji. Don haka ne abin da ya fi ga kowane ma’aurata shi ne sanin wane irin lamari ne ya fi soyaiya ga juna don kiyaye shi.

Sai kuma kanshin jiki, matukar akwai yalwar sayan kayan kanshi na turarawa ko na fesawa a jiki to suna da muhimmanci matukar gaske. Soyaiya ta sha karfafa ta hanyar kansasa jiki, har ma akan samu mai aure idan wata budurwa tana yi masa yanga yana yi mata gori da cewa ina da wacce ta fi ki, wacce take kanshi ba ke mai warin jiki ba. Kamshin jikin mace yana daga cikin sirrin da yake tsare namiji gun matarsa don zama da ita tsawon lokaci ba tare da gajiyawa ba.

Sai kuma yadda suke son ganin jikin juna, misali yaya yake son gashinta, wace kala ce gashinta yake so sai ya sayo mata abin da zata rina gashinta don ya yi kalar da yake so, ko kuma gashin kari yake so sai ya sayo mata don ta yi kitso da shi. Kuma ya samar mata da kayan shafe-shafe iri-iri tun daga saman kanta, idanuwanta, jagirarta, rinin hannyenta da kafafuwanta, sai kalar da yake son ganin kan faratanta. Sai kuma tufafin sanyawa, wane lokaci ne ya fi dacewa da shiga mai kyau, wace irin shiga ce namiji yake so, wace shiga ce mace take so, kowane mutum yana da irin shigar da ya fi so, misali wani namijin ya fi son mace ta yi masa shiga da kananan kaya, wani kuma da kayan al’adar gargajiya, kamar yadda yake hakan ga mata. Sannan idan dare ne wane irin kaya ya kamta mace ta sanya wa mijinta shi ma ya sanya mata, wannan ma wani bahasi ne mai zaman kansa, kuma duk da akwai nau’in kayan da marubuta suke fada sai dai yana da kyau a lokaci guda mu koma wa ma’aurata don sanin me suke so wa junansu. Wasu mutanen suna muhimmantar da kalar kaya da launinsu, wasu kuma suna muhimmantar da yadi da nau’insa, ko wane gida ya san inda yake yi masa yoyo, don haka kowane mutum ya san abin da ya fi so, kowane gida ya san kalarsa. Kuma kamar yadda ake son mace ta yi wa mijinta haka nan ake son namiji ya yi wa matarsa ado, ruwaya ta yi nuni da cewa Allah ya yi umarni ga maza su yi wa matansu ado kamar yadda ya yi umarni mata su yi wa mazansu ado. Wata ruwayar ta sake yi mana nuni da yadda matan Banu Isra’il suka lalace da son wasu mazajen wasu kabilu da ya kai su ga lalacewa da ha’intar mazansu sakamakon cewa mazan kabilarsu kazamai ne.

Amma akwai wata al’ada maras ma’ana mai ban haushi a kasashen Hausa ta yadda zaka ga mace ba ta yin ado sai don unguwa, idan kuwa a gidanta ne sai ta sanya kaya sai ka ce keso ko tsumma. Wani yana ba mu labarin cewa wani mutum suna zama da abokansa suna hira sai ya hango wata mata zata wuce, sai yake cewa ji wata kyakkyawar mata, sai bayan abokinsa ya kura mata ido sai ya ce wane ai matakar ce, sai kunya ta kama shi saboda bai gane matarsa ba. Adon nan fa ba shi ne dole sai ta kure adaka ba, kayanta masu kyau da jan baki da kayan kanshi da turare da zata sanya, a takaice ma muna iya cewa ta kasance cikin tsafta kawai a gidanta tare da mijinta ya wadatar. Ma’auni shi ne ta san mene ne ya fi so kuma yake gamsuwa da shi ko da kuwa kwalliya ce ta musamman da take dauke hankalinsa zuwa gare ta.

Sai kuma alakar kyautata abinci, kowane mutum akwai abincin da ya fi so a rayuwarsa, a nan ma sai ma’aurata su sanya abin da suka fi so, sai dai akwai nasihar su kula da mai lafiya ba kawai dadin baki ba. Kula da lokacin dafa abinci kan kari, da nau’in dahuwar, da kanshin abinci, da dadinsa, da lafiyarsa, wasu abubuwa ne muhimmai ga mata su san su. Sannan daga karshe kuma yadda za a ci abinci tare, da wurin da za a ci, a gida ne ko a gidan abinci, ko a Pak ne, ko kuma wurin shan askiran ne, da sauransu. Samun fitar tare miji da mata da ‘ya’yansu idan akwai ‘ya’ya ko da sau daya ne a wata wani abu ne muhimmi domin mutum yana son canji ko yaya ne, kuma fita ko sau daya ne a cikin wasu watanni yana matukar haifar da nishadin rayuwa ga ma’aurata.

Sai kuma mafi girman asasin rayuwa don yaduwar dan’adam a duniya da ya shafe dauke bukatun sha’awar juna, a nan yana da kyau ma’aurata su san me ye yake iya burge su, kuma yaya zasu gabatar da lamarinsu, mece ce tawayar da take damunsu, wani lokaci sukan bukaci koma wa kwararru da likitoci don cike tawayar da take damunsu kan wannan lamarin, shi dai wannan lamarin bangare ne mai matukar muhimmanci a matsayinsa na asasin aure.

Adon Mace

Daya daga cikin mas’aloli da ake fuskanta shi ne cakuda dokokin musulunci da al’adu, wani abin mamaki shi ne irin wani sandararren tunani ya yawaita ya karu har a gun wasu da ake ganin kamar sun san wani abu na addini amma sau da yawa idan ka tattauna da su sai ka samu sun ba wa al’adun da suka taso cikinsu rigar musulunci ne, don haka sai suka rika bayar da tunani mummuna ga al’umma ko kuma suka rika kallon abin da yake al’adu shi ne musulunci. Musulunci ba sandararren tunani ba ne da ya haramta adon Allah ga dan’adam, addini ne mai tafiya da kowane waje da zamani, koda yake ka da mu manta cewa ta wani bangaren wannan yana da tasiri da nau’in mazhaba wani lokaci.

Fikirar mazhabin alayen annabi masu daraja (a.s) da ya bar mana su a matsayin makoma bayansa fikira ce rayaiya da ta dace da kowane waje da zamani, kuma malamansa suna da dokoki da a kansu ne suke fitar da hukunci hada da cewa kofar ijtihadi a wannan mazhabin a bude take. Shari’a ta yarda da yin adon mace da sa mai kyau sai dai ta zo da hana adon mace ga ajnabi da zai ja hankalinsa ko yaudararsa, amma adon mace ga mijinta kowane iri ne ko a cikin mata ko wurin da babu ajnabi ya halatta. Haka ma mace tana iya sa turare[1] amma idan zata fito waje sai ta sanya mai karancin kanshi da zai hana jikinta wari ba tare da kanshin yana jan hankalin wasu zuwa gare ta ba.

Kuma tana iya yi wa mijinta ado da duk kayan ado kowane iri ne kamar karin gashi[2], ko janfarce, da jan baki, ko zare, ko zane a fuska don kara kyau, ko sarka da zobe, da awarwaro don ado, da rina gashi da kowane launi domin ado, ko lalle[3], matukar ba ta yi ne don wani ba sai don mijinta[4]. Idan maras aure ce ya halatta ta kara gashi ta aikata sauran abubuwan da muka ambata amma da sharadin ba zata yaudari wanda yake son aurarta ya dauka nata ne na asali ba, wannnan kuwa an hana shi ne ta fuskacin yaudara amma ita a kanta zata iya yin adonta[5]. Haka nan shari’a ke kafa dokoki bisa maslaha da kare zabin mutane matukar ba zai bude musu hanyar fasadi da ta saba wa hadafin halittar dan’adam ba.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1]. Alfikhu lil mugtaribin: ahkamun tata’allaku bi zinatil mar’a, saiyid sistani.

[2]. Alfatawal muyassara: alhiwariiyatul amma assaniya, saiyid sistani. Da kuma; Alfikhu lil mugtaribin: ahkamun tata’allaku bi zinatil mar’a, saiyid sistani.

[3]. Alfikhu lil mugtaribin: ahkamun tata’allaku bi zinatil mar’a, saiyid sistani.

[4]. Abin da ya gabata.

[5]. Abin da ya gabata.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

2 comments

  1. Allah ya saka da hairan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *