Armashin Rayuwar Ma’aurata

A wannan bangaren (BANGARE NA GOMA) muna son mu yi nuni da cewa: Bayan ma’aurata sun shiga rayuwar tare tsundum suna bukatar sanin abubuwan da zasu karfafi wannan alakar tasu a dalilin haka ne a nan bangaren muka kawo bayanin abubuwan da zasu karfafi alakar ma’aurata da suka shafi badini da zahirin rayuwarsu, da siffofin da suka dace ma’aurata su siffantu da su, da kiyaye duk wani abu da yake damfare da rayuwarsu na gida ne ko na waje, ko kuma abin da ya shafi jikinsu da tufafinsu da sauransu, don haka sai a biyo wadannan bayanai kamar haka. Ana son ma’aurata su rika kula da abin da ya shafi juna ta kowace fuska, Musulunci ya yi kira ga ma’aurata su taimaki juna kan aiyukan alheri, idan mace tana aikin alheri kamar tana da kyauta ko sadar da zumunci, haka nan ma miji, to sai su taimaki juna kan hakan. Su taimaki juna kan sadar da zumuncin juna, taimakon makota, idan ta iya magani ko ya iya sai su rika zuwa tare suna taimaka wa makota. Idan mai kudi ne ko ita mai kudi ce suka ji wata matsala ta samu wani daga danginsu ko makotansu to sai su tafi tare su taimaka musu.

ARMASHIN RAYUWA

Mutum yana da bangare biyu masu muhimmanci bangaren rai da bangaren jiki, kuma kowanne ana son ya zama ya daidaitu ya kyautatu. Kuma babu wani wanda zai iya taimaka wa juna kan hakan fiye da mutanen da suka fi kowa kusanci da juna, sannan babu wasu mutane da suka fi kusanci da juna fiye da ma’aurata, ke nan babu wasu da suka fi cancantar taimaka wa juna fiye da ma’aurata. Ubangiji madaukaki ya yi umarni ga mutane mazansu da matansu da kiyaye ‘ya’yansu da iyalinsu daga wuta, bai kebanci wannan da maza ba kawai kamar yadda wasu mafassara suka dauka, wannan bangaren ya shafi gyaran rayuka da taimakon juna kan yin aiyuka nagari don kare su daga fadawa wutar lahira. Sai kuma bangaren zahiri na jiki da zai taimaka wa wancan bangaren samun nasara, nutsuwar rai ce take samar da matakin farkon neman lahira, idan zahiri ya samu hakkinsa to sai badini ya samu nutsuwar kusantar ubangijinsa da imani da aiyuka nagari.

Abincin Mutum

Abin da ya fi muhimmanci a matakin farko shi ne abincin halal da yake narkewa a cikin jikin mutum sai ya zama tsoka, kashi, jijiya, da jinin mutum, idan miji da mata suka samu damar taimakon juna kan neman halal da cin halal to sun dasa asasin farko na kamalar ma’aurata da Allah yake nufinsu da ita. Kuma mata suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wurin karfafa mazansu haka ma maza su karfafa matansu wurin sanin neman hanyar halal don samun abincin da ba zai gurbata masu jini ba.

Sannan a wurin cin abinci, sai su kula da laduban cin abinci na wanke hannu da farko, da yin basmala, sai kuma ba wa junansu abinci, har sai cokalin miji ya zama lomar matarsa, cokalinta ya zama lomar mijinta. Idan an gama cin abinci sai a yi godiya ga Allah madaukaki, a nade ledar abinci, idan wani ya zuba a kasa nan take sai a share wurin a goge.

A nan ne yake da muhimmanci a kebanci wani wuri na musamman kamar kicin ko dakin cin abinci ta yadda abinci ba zai fita daga wurin ba balle ya zuba kasa ya jawo kwari da tururuwai ko cinnaka da sha-zumama cikin gida. Sai dai wannan yana ga mai yalwar yin hakan ne, amma wanda ba shi da yalwar hakan to sai ya kiyaye duk inda zai a jiye abinci ya zama akwai tire ko leda da idan wani ya zuba zai fada a kai ne.

Sannan kuma idan aka gama cin abinci yana da kyau a kiyaye wanke kwanuka da farantai da kofunan da aka yi amfani da su. Shari’a ta yi nuni da cewa ka da a bari kayan abinci su kwana da datti, domin shedan yana kwana a cikinsu. Masana sun yi nuni da bibiyar da aljansu suke yi wa kwanuka da suke kwana da dattin abinci, masu ilimi kuwa sun kawo yadda kwayoyin cuta suke taruwa a kwanuka masu datti har suka fassara ma’anar shedan da wadannan kwayoyin.

Tsaftar Jiki

Sai kuma kula da tsaftar zahiri da ta shafi jiki, tufafi, gida da duk bangarorinsa har da ban daki, kayan gida, kayan abinci, rariyar ruwa. Sai miji da mata su taimaka wa juna tun a matakin farko na tsafta da ya hada taimaka wa wurin wanka, cudanya bayan juna, busar da jiki da tawul, sanya tufafi, shafa mai, sanya turare.

Yana da muhimmanci matukar gaske mu kula da tsaftar jikinmu, ma fi muhimmancin tsaftar da ya kamata mu kula kanta ita ce wacce a matakin farko muke iya cutar da mutane idan ba mu kiyaye ta ba, da farko zamu ga warin baki da na hammata sun fi damun mutane, kuma suna nuna mana kimar mutum da darajarsa a matakin farko.

Idan ma’aurata suna son samar da gida mai nishadi da zama abin koyi a cikin al’umma to sai su kiyaye wannan tsaftar hatta a cikin gidajensu, su kiyaye wanke bakinsu da burash da makilin, su goge hakoransu da harshensu kowace safiya, su shafa body spray a hammata bayan wanka, idan akwai hali sai su hada da turare a tufafinsu. Su kula da yankan farshe, aske gashin gaba, gyara fuska, kawar da fason kafa, gyaran gashi ko kitso ga mace, kayan shafe-shafe da jan baki ko farce ga mace, da sauran abubuwan da zasu ba ta ado ga mijinta.

Ma’aurata suna iya yi wa junansu askin duk wani bangare na jikinsu da ya hada da gabansu da hammatarsu da yanke wa juna farce da makamantan hakan. Tsaftar jiki ita ce asasin farko na nishadin rayuwar mutum shi kansa balle kuma idan yana tare da mutane, ballantana kuma abokan taraiya a rayuwar duniya kamar miji da mata. Duk wani wari da yake fita daga jikin mutum yana da matukar gudummuwa da yake bayarwa wurin dasashe kaifin tunanin mutum da hazakarsa, sau tari mutanen da suka rayu suna shakar wari ya kasance sakamakon dakelewar tunaninsu. Hada da cewa wari yana haifar da cututtukan da suke halakar da mutum ko yada cututtuka wasu ma masu wuyar magani, ko kuma ya haifar da cutar da ba a san maganinta ba.

Gashi wuri ne da yake boye cututtuka don haka ne shari’a ta yi umarni da aske gashi musamman gaba da hammata a duk sati, haka ma farce wuri ne da cututtuka suke labewa don haka yanke shi yake da muhimmanci ta wannan fuskar. Gashin namiji yana bukatar tajewa lokaci-lokaci, haka ma gashin mace yana bukatar gyara ko kitso a lokaci-lokaci, gashi wuri ne da duk wata dauda take labewa, don haka gyara shi ya ke nuna darajar mutum da kimarsa.

Haka ma tsaftar sauran gabobin mutum take da muhimmanci; warin kunne, ko hanci, ko baki, mutuwa ke nan. Wari ne da suke misalta jahannamar duniya kafin barzahu, idan mutum yana da warin kunne ko hanci ko baki ya yi gaugawar samun likita don kawar da wannan bala’in da yake kawar da duk ni’imomin rayuwa. Rayuwar mutum ta yi ban kwana da nishadin rayuwarsa da ta abokin zaman rayuwarsa matukar yana da warin kunne, baki, hanci, da sauransu, kuma ya yi ban kwana da samun sukuni a cikin al’umma. Idan dai akwai adalci ga kai ko ga abokin ko abokiyar rayuwar tare to mai wannan cutar zai gaugauta koma wa likitoci don kawar da wannan cutar.

Wanke duk wani abu da yake iya yin wari idan ba a wanke shi ba yake da muhimmanci, sai a goge baki sosai da hakora da harshe kafin da bayan bacci ko cin abinci. A wanke bayan kunne yayin wanka, a goge cikinsa da auduga a cire duk wata daudar kunne. A kula da hanci ka da a bar shi da majina ko tasono ko wani abu da zai sanya shi wari. A yayin wanka a kiyaye sosai a wanke wasu bangarori masu rike dauda da boye ta, sai a kula da wanke tsakanin cinyoyi, kasan nono ga mace, hammata, wuya, kafafu, tsakanin ‘yan yatsu, wurin faso, da sauransu.

Tsaftar Tufafi

Tufafin da mutane suke sanyawa suna bambanta sakamakon al’adu mabambanta, sai dai muhimmi shi ne tsaftar tufafin da saurin wanke su idan sun yi datti ta yadda kayan wanki ba zasu sanya gida yin wari ba, goge su don su yi kyawun sanyawa cikin ado, sai kuma tsara su cikin kwabar ajiyar kaya. Miji da mata ne suka fi kowa sanin yadda ya kamata su shirya kuma su tsara lokutan yin wankin tufafi, ko dai su rika yi tare ko kuma su tsara shi bisa taimakon juna, ko kuma idan akwai hali su rika kai wa masu wankin kaya da guga.

Sai kuma kayan ado da mai gida yake saya wa matarsa don ta yi masa ado da su da wannan ma ya danganta da karfin namiji ne, idan kuwa matar tana da karfin yi wa kanta to komai yawansa gare ta ba ya cutarwa. Da bukatar taimaka wa mace da kayan ado da zata rika yi wa mijinta ado da su, adon da mace zata rika yi wa mijinta a cikin gida wani muhimmin lamari ne da yake sanya shi shaukin zama cikin gida da tunanin matarsa da kawar da kansa daga kallon wasu matan.

Mafi girman gudummuwar da miji da mata zasu yi wa junansu ita ce ba wa juna shawarar kaya da zasu sanya ta fuskacin tsafta, idan mace ta ga mijinta ya sanya kaya masu dauda zai fita to sai ta gaya masa don ya sauya kayansa, haka ma namiji yana iya taimaka wa matarsa ta wannan janibin. Kuma namiji yana iya shawartar matarsa idan ya sanya kaya don ta gaya masa sun yi ko kuwa?.

Lamarin Gida

Amma tsaftar gida da kula da kayan gida lamari ne mai muhimmancin gaske da ya kamata ma’aurata su sanya hannu tare don kiyayewa. Matakin farko shi ne tsaftace gida da yi masa fenti duk shekara daya ko biyu don kiyaye tsaftarsa, wanke bangonsa, gyaran simintin kasa idan ya fashe, cire yanar gizo daga sili da bango, da sauran abubuwa. Tsaftar ban daki, kicin, dakin wanka, dakin tarbar baki ga wanda yake da shi, tsakar gida, kofar gida, rariyar ruwa, da sauran bangarorin gida.

Tsaftar kayan gida da suka hada da share ledar rumfa da falo da ta dakuna, ko kafet da ake sharwa da gogewa ko wanke shi duk wasu watanni ko duk lokacin da ya yi datti, ko kula da tsaftar tayel da darduma idan su ne a gidan. Sannan kuma sai kula da tsaftar labulayen gidan baki daya, da zannuwan gado, da barguna ko mayafan rufa, da rigar filo wato matasan kai. Kula da tsaftar gado da share karkashinsa kowace rana, da goge kujerin kushin, da teburan zama na karatu ko na cin abinci, ko na komfita. Sai kuma kula da esin sanyaya gida, ko hitar dumama shi, da furij, da gas kuka, da gilasai, tagogi, kofofi, da sauran abubuwan da suke da alaka da bango da garun gidan.

Duk wani datti da yake samun wani abu daga cikin wadannan abubuwan da muka kawo yana da muhimmanci a kula da shi sosai, kuma da zaran abu ya yi datti ne ake goge shi ba sai an jira ba. Misali idan mace tana dafuwa sai miya ta zuba kan gas kuka to da zarar ta gama abinci sai ta share wannan miyar da ta zuba kansa.

Wanke-wanke yana daga cikin abin da yake yi wa mata wahala da ya kamata namiji ya taimaka musu musamman idan babu yara a gida ko ‘yan aiki masu taimakawa. Haka ma dafa abinci yana daga cikin abin da yake bukatar sanya hannun ‘ya’ya ko masu aiki idan da halinsu, domin wasu aiyuka ne da suke iya dauke lokacin mace baki daya su hana ta yin ko da nazarin wasu littattafai don ta karu a ilmance. Idan mace ta samu tallafi da taimako a wannan fagagen to takan samu sukunin yin wasu aiyukan da ma ibadojin da zasu zama masu amfani gare ta. Shi yin aiki barinsa baki daya ga mace cuta ne domin yana da hadari ta zauna ba ta motsi a kowace rana, haka ma idan ya yi yawa sai ya haifar mata da sukewa daga rayuwar wahala mai daci. Ke nan a komai tsakaitawa ce mai amfani ga kowane abu.

Tsaftar kicin da kula da tukwane da kwanukan abinci da furiji da abin dafuwa suna da muhimmanci, mafi muhimmanci a nan shi ne rufe duk wani abu ta yadda wani kwaro ko bera ba zai iya kaiwa gare shi ba. Sai kuma samar da abin da zai rika kansasa kicin ta yadda idan an shiga za a ji kanshinsa.

Ban daki wuri ne da wasu suka dauka dole ya yi wari alhalin ba haka ba ne. Da farko duk wani wanda zai yi fitsari ko kashi sai ya fara zuwa ruwa kan tangaran din idan na tangaran ne misali, sannan da ya gama ya yi fuloshin. A sanya masa abin kansasa ban daki, a kuma wanke shi da hodar wanke ban daki mai kashe wari da kwayoyin cuta. Sai kuma sabulu da ake ajiyewa domin duk wanda zai fito daga cikin ban daki ya wanke hannunsa tukun.

Kula da Yara

Idan ma’aurata suka kiyaye duk wata tsafta amma ba su kiyaye ta yara ba to kamar ba su yi wani abin azo-agani ba, kwarewar taimakon juna da kiyaye asasin rayuwar dan’adam a yin tsafta tana cikin tsaftace yara ne. Yaro mutum ne sabo da babu ruwansa da abin da ya shafi kansa, kuma ba shi da wata kwarewa ko wani darasi na rayuwa ko ilimi game da abin da ya dace da wanda bai dace ba, don haka ne ‘ya’ya suke bukatar duk wani taimako daga iyaye a kowane abu. Yaro yana bukatar taimaka masa, kuma wannnan taimakon dole ne sai iyaye miji da mata sun hada hannu. Yana bukatar tarbiiya da ta fi komai wahala wacce sai sun hada hannu su biyu sannan zasu iya kai wa ga natija mai kyau. Wannan janibin yana bukatar bayani mai yawa da zamu kawo su a cikin littafinmu na “Tarbiiyar Yara”.

Yara suna bata mahalli cikin sauki, idan suka yi wasa sai su yi wurgi da komai a ko’ina, idan suka ci abinci sai su watsa shi ko’ina, idan suka cire tufafi sai su wurgar da shi duk inda suka ga dama. Domin su saba da tsara komai a mahallinsa yana bukatar yawan luraswa har su taso suna masu sabawa da kiyayewa, idan iyaye suka gajiya kan yi musu magana to wannan laifin iyaye ne. Maimaicin magana, da kula da kiyayewa, sai kuma aikin da su iyayen suke yi suna tasiri matukar gaske kan yara. Sai kuma iyaye su yarda da cewa ba su kadai ba ne zasu iya, akwai abokansu da ‘yan’uwansu da danginsu da ma makotansu duk suna sanya hannu don tarbiiyar yaransu ta yi kyau. Wasu iyayen suna cutar da kansu ta hanyar jin haushin mutanen da suke yi wa ‘ya’yansu fada, daga karshe sai kowa ya daina yi wa yaran fada, sai a ga suna yin munanan aiyuka babu mai yi musu magana, da wannan ne sai su cutar da ‘ya’yansu.

Tsaftar da ya kamata a kula da ita game da yara ta hada da yi musu aski ko taje musu gashin kai, wanke musu hannu kafin da bayan cin abinci, yi musu wanka da dirje musu jikinsu tun daga kai, bayan kunnuwa, da ma duk sassan jikinsu, wanke musu bakinsu da burash mafi karanci da safe, share musu majina, yanke musu farce, da sauransu. Sai kuma abin da zasu sanya da suka hada da wanke musu hula, riga, wando, da goge musu takalman da zasu sanya. Ka da a bari kayan yara su yi dauda da yawa har su taru, sai a rika yi musu wanki akai-akai, a goge musu kayan, a goge musu takalma kullum, da kula da fitar su don ka da su fita ba takalma.

Kamar yadda ake kula da su a cikin gida, haka ma za a kula da su a waje, sai a kula da abokansu, wuraren da suke zuwa wasa, da me suke wasa, da su wa suke wasa. Sai a bar su don su walwala a wurin lilo, da cikin kasa, amma a kula don ka da su ci. Da zarar sun dawo sai a sake duba jikinsu, idan wani kaya ya yage sai a ware shi don dinkewa, idan wani ya yi kasa ko ya yi dauda ko ya samu datti, sai a ware shi don wankewa.

Kula da lafiyarsu duk sa’adda suka yi rashin lafiya ba shi da bambanci da kula da abincinsu duk nauyi ne da ya yake kan iyaye. Haka nan kula da sanya su makaranta da fitarsu zuwa ajin karatu da dawowarsu, da duba abin da aka koya musu kowace rana, da tambayarsu yadda makaranta ta kasance, duk suna da muhimmanci matukar gaske. Sai kula da wuraren kai su don shakatawa da wasanni, da sayo musu kayan wasa, da tsara musu lokutan karatu da na wasa, da sauran bangarorin rayuwarsu. A takaice muna iya cewa; kula da yara shi ne babban asasin rayuwar ma’aurata.

Kansasa Gida

Ruwayoyi sun zo cewa manzon Allah (s.a.w) yana kashe wa sayan turare kudin da ba ya kashe wa abincin da zai ci. Wasu ruwayoyin sun yi nuni da cewa an so wa manzon Allah (s.a.w) abu uku a wannan duniyar, mata, turare, da yin salla. Da wannan ne zamu fahimci cewa turare da abubuwan da suke kansasawa suna da muhimmanci matukar gaske. A wannan zamanin an samu sauyi matukar gaske a komai tun daga sabulun wanka, omon wanki, zamu samu masu kansasa jiki da tufafi, sannan akwai turaren da ya dace da jiki akwai na tufafi da kuma na wuta wanda ake turara kaya ko gida da shi.

Akwai kayan shafe-shafe na mata da sukan sanya su laushin fata da a yau suna amfani da shi don kansasa jikinsu da gyara fatarsu har ma yana iya mayar da fatar tsohuwa ta dawo kamar ta budurwa. Kanshin jiki yana daga abin da ya fi komai jan hankalin miji zuwa ga matarsa ko mata zuwa ga mijinta, idan mace tana amfani da turaren da zai sanya jikinta kamshi mijinta zai so zama tare da ita da kusantar ta, da jin dadin hira da ita, wannan yana daga sirrin kamshin jikin mace.

Sai kuma kula da kamshin tufafin sawa, turare wani abu ne mai sirri matukar gaske, akwai da yawan maza da suka auri mace saboda kamshin da take yi kawai, ko kuma suka aure ta sai kamshin ya dada musu soyaiya da ita. Mutum mai kamshi yana da soyuwa a zukatan mutane, wasu saboda kamshinsa suke son rabuwa kusa da shi, haka ma namiji ko mace idan suna kamshi sukan so kusantar junansu. Kamshi wani abu ne da yake faranta ran mutum, yake kawar masa damuwa da bakin ciki, yana sanya nishadi da walwala, don haka ma’aurata ne suka fi dacewa da zama cikinsa kamshi.

Idan muka waiwayi kamshin gida kuwa zamu ga cewa ana amfani da turaren wuta, da air freshner, da sauran kayan kamsasa wuri domin a kamsasa dakuna, falo, kicin, ban daki, da sauran wurare. Muhimmi a kamsasa wuri shi ne irin wanda mutane suke so, domin wasu kamshin suna sanya tashin zuciya, ko sanya damuwa, to sai mace ta kula da irin kamshin da ya fi dacewa da dabi’ar mutane da soyuwa gun su. Kuma duk gidan da yake da kamshi zai kasance abin soyuwa wurin ubangiji madaukaki da bayinsa, ubangijinmu mai kyau ne kuma yana son duk wani abu mai kyau. Allah ya sa mu dace.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

45-Hajjin Tamattu’i 3

  Hajjin tamattu’i shi ne bangare na biyu da yake farawa daga ranar Arafa har …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *