Tauhidi A Buhari Da Musulim – 2

Dariyar Allah

Duk wata siffa da Allah zai siffantu da ita dole ne ta kasance tana da kamala da babu wata tawaya gare shi da ta kunsa, idan muka samu ruwaya ta zo da siffar tawaya da iyaka da nakasu ga Allah (s.w.t) to nan take zamu yi hukunci da rashin ingancinta da shaidawa da rashin zuwanta daga ubangijin talikai da manzonsa mai hikima da daukaka.

Idan muka ba wa Allah wata sifar tawaya to yana nufin mayar da shi cikin ababan halitta da suka rasa kamala, rasa kamala kuwa yana nufin ke nan ya bukaci mai cika shi domin duk mai tawaya yana da mai cika shi wanda ya jingina da shi don samun kamalarsa, don haka sai ubangijin talikai ya tashi ba Ubangiji ba ke nan, alhalin shi ne ubangijinsu.

Dariya tana daga cikin abin da ruwayoyin da suka zo daga ingantattun litattafan ‘yan Sunna da suka tabbatar wa Allah madaukaki. Wannan lamarin na dariya ya zo a cikin ruwayoyi mabambanta tun daga Buhari da Muslim da sauran litattafai da suka kunshi batutuwa kamar haka:

Batun mamaki da dariyar da Allah ya yi wa wasu mutane kan ayyukan da suka yi. Batun dariyar da Allah (s.w.t) ya yi wa wani wanda ya yi masa wayo har ya samu Allah ya shigar da shi aljanna. Batun dariyar da ya yi wa mai kisa da wanda aka kashe saboda wanda ya yi kisa shi ma daga baya ya tuba ya shiga aljanna. Ya kai ga Abuzariin yana cewa ya tambayi manzon Allah (s.a.w) shin Allah ma yana dariya. Sai ya ce: Ba mu rasa ubangijin da yake dariya ga alheri ba[1]. Hadisan sun tattara abubuwa da suka ci karo da kamalar Allah da girmansa kuma hankali kuButacce ba zai karBe su ba, da suka hada da:

Cewar Allah yana mamaki ya yi dariya kamar mutum. Yana yaudaruwa da har bawansa zai ta yaudare shi har sai ya kai shi cikin aljanna. Sannan wane Ubangiji ne mai rahama da zai sharadi da bawansa ka da ya tambaye shi rahamarsa! Kuma me ye na karya wannan alkawarin da Allah yake yi ya sake yin wani sharadin da alkawarin da bawa kuma ya yi ta karyawa duk a matsayi daya kan lamari daya!.

Wane irin lamari ne zai samu bawa har ya gaya wa Allah magana yana ce masa yaya zaka yi mini izgili kana ubangijin talikai?!. Sai Allah ke nan ya kasance a matsayin wanda bawansa yake tuhuma! Kamar dai bawan ya ki yarda da Ubangiji yana ganin shi ma zai iya yaudararsa kamar yadda ya yaudari Allah ya yi masa wayo!.

Wannan shi ne sakamakon abin da zai kasance a irin wadannan ruwayoyin da suka saBa wa littafin Allah da sunnar annabinsa mai inganci.

Cirata Daga Wuri

Akwai hadisai da aka samu a cikin Buhari da Muslim da suke nuni da samuwar wuri ga Allah madaukaki, wadannan ruwayoyin suna nuna yana saukowa daga sama zuwa kasa a kowane dare. Wadannan hadisai dukkansu suna komawa zuwa ga ruwayar Abuhuraira da zamu ga suna kunshe da wasu bayanai kamar haka:

Allah yana sauka a kowane sulusin dare na karshe don tambayar mutane bukatunsu domin ya biya musu ita.

A wata ruwayar ya zo cewa daga karshe sai Ubangiji ya bude hannayensa ya ce: Waye zai ba wa Allah rance[2].

A ruwayar uwar muminai A’isha ya zo cewa: Ubangiji yana kusantowa kusa da bayinsa ne a ranar Arfa fiye da kowace rana![3].

A cikin dukkan wadannan hadisai idan mun hada su zamu ga sun kunshi wasu abubuwa kamar haka:

1- Ba wa Allah jiki; 2-Bukatar Allah ga wuri; 3-Bukatuwarsa ga jiha; 4-Ba wa Allah iyaka.

Ruwayoyin sun zo da sura daban-daban wasu ma sun yi nuni da cewa yana saukowa ne bayan wani Bangare na dare ya wuce. Sai dai abin da duk yake cikinsu yana saBa wa abin da yake na yakinin hankali da koyarwar littafin Allah mai inganci[4].

GABOBIN ALLAH

A cikin Buhari da Muslim akwai ruwayoyin da suka zo suna nuna cewa Allah yana da gaBoBi kamar dai wani samamme da yake da jiki, kamar wani mutum da yake da Bangarori da gaBoBi kamar fuska, hannu, dan yatsa, da sauransu. Idan mun duba a fili zamu ga bahasosin da suka gabata sun yi nuni da wannan ta yadda zamu ga wasu sun yi nuni da samuwar gaBa ga Ubangiji madaukaki.

Fuskar Allah

Buhari da Muslim sun ruwaito hadisai da suke ba wa Allah madaukaki fuska da kama, wannan fuskar ta yi kama da fuskar mutum, a cikin hadisin da Abuhuraira ya karBo an siffanta Allah (s.w.t) da cewa yana da sura irin ta annabi Adam (a.s) da ya halitta mai tsawon zira’i sittin. Ruwayar tana nuna cewa a ranar lahira duk wanda zai shiga aljanna ma zai kasance da tsawon annabin Adam (a.s) ne, kuma tun lokacin annabin Adam (a.s) mutane suna rage tsawo ne har yau.

Ruwayar ba wa Allah fuska ta maimaitu a wata ruwayar da take hana wani zagin wani mutum saboda surarsa irin ta Allah ce, domin Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa sura da kama irin tasa. Haka nan ta maimaitu a cikin ruwayar wanda ya mari wani mutum sai aka hana shi marin fuska domin Allah ya halicci mutum da kama irin tasa ne[5][6].

A cikin wadannan ruwayoyin zamu ga akwai ba wa Allah sifa, sura, kama, da fuska irin ta mutum wacce take lizimta siffanta shi da jiki.

Sannan abin mamaki gare su da fitar da hukunci daga wannan kamannin da yake ganin tun da fuskar mutum ta yi kama da ta Allah madaukaki to bai kamata ba a mari mutum ke nan.

Haka nan tsawon Adam (a.s) zira’i sittin ne, kuma fadinsa zira’i bakwai ne, kuma tun da yana kama da Allah to zai kasance ke nan tsawo da fadin Allah madaukaki ya zama sananne ke nan.

Idan da mutum na farko yana da tsawo da fadi haka don me ya sa duk mutanen da ake hakowa masu tsawon tarihi tun lokacin annabi Adam (a.s) aka same su da tsawo irin na wannan al’ummar babu wani bambanci, ko bambanci kadan.

Idan da annabi Adam (a.s) ya kasance da tsawon zira’i sittin ne, to abin da tsawon hannunsa ya kamata ya kasance shi ne zira’i sha bakwai da kashi daya cikin bakwai na tsayi ba zira’i bakwai ba domin ya yi daidai da tsarin halittar tsayin mutum. Idan ya kasance kamar yadda ruwayar ta kawo to zai kasance mutum mai muni matukar gaske alhalin Kur’ani mai daraja yana cewa: “Lallai mun halicci mutum cikin mafi kyawun kirar halitta”[7].

Idon Allah

Ruwayoyin da suka zo a Buhari da Muslim suna nuni da cewa Ubangiji madaukaki ba makaho ba ne kamar Dujal, domin shi Dujal idonsa na dama makaho ne da ya yi kama da kwayar inabi[8].

A sakamakon wadannan ruwayoyin ne ‘yan Sunna suka tafi a kan cewa Ubangiji yana da idanuwa masu gani. Kuma kiyasin idon Allah da na Dujjal ba abin da yake nuni sai da hakan. Abu mai muni a cikin wannan ruwayar yadda take kawo Dujjal tana kamanta Allah da siffofin da suka saBa da nasa.

Kafadar Allah

Ya zo a cikin Buhari da Muslim da Ibn Majah cewa Ubangiji yana dora kafadarsa kan ta bawansa sai ya gaya masa cewa ka tuna zunubi kaza da kaza da ka yi a duniya, to ni na suturta maka su a duniya yau kuma ina gafarta maka su.

Wani mutum ya tambayi Abdullahi dan Umar kan wannan lamarin sai ya ce haka ne, na ji annabi yana fada, sai ya kawo wannan ruwayar[9].

Hannun Allah

Hadisan Abuhuraira da Abdullah dan Umar da suka zo a Buhari da Muslim da wasu Sunan sun ba wa Allah madaukaki hannu suna nuni da cewa hannunsa na dama a cike yake, amma hannunsa na hago yana dauke da ma’auni ne da yake rage rabon wani da shi ya kara kason wani da shi.

Daya ruwayar kuwa tana nuni da cewa zai dauki sammai da kassai da hannunsa sai ya rika jimke hannunsa yana budewa yana cewa ina masu jiji-dakai! ina masu takama! Har manzon Allah ya kasance yana yin dama da hagu a kan mimbari. Da sauran ruwayoyi da suka zo da wannan lamarin suna masu siffanta Allah madaukaki da hannaye[10].

Yatsun Allah

A cikin ruwayar Abdullahi dan Umar game da zuwan malaman yahudawa gun annabi (s.a.w) sai suka ce Allah zai dauki sama, kasa, ruwa, shuka, kasa, kowanne a kan wani dan yatsansa kamar yadda suka samu a littafin Attaura. Ya ce sai manzon Allah ya yi murmushi har hakoransa suka bayyana yana karfafa hakan, sai kuma aya ta sauka tana gaskata hakan[11].

Tabbatar wa Allah ‘yan yatsu kamar sauran gaBoBi lamari ne mai ruwayoyi masu yawa a cikin Buhari da Muslim da kuma sahihai da sunan na litattafan ‘yan Sunna. Wannan maganar tana lizimta siffanta Allah da iyaka da gaBoBi da jiki, lamarin da zai mayar da shi mabukaci mai iyaka.

Kwankwanson Allah

Wasu ruwayoyin Buhari da Muslim suna tabbatar wa Allah kwankwaso. Ruwayar Buhari da Abuhuraira ya karBo tana cewa lokacin da Allah ya yi halittu sai zumunci ya tashi ya cakumi kwankwanson Allah, sai Ubangiji ya ce masa yi sannu dai. Sai zumunci ya ce: Me ye matsayin wanda ya yanke zumunci. Sai ya ce masa: Ba ka yarda da in sadar da wanda ya sadar da kai ba, in kuma yanke wanda ya yanke ba. Sai ya ce: Na yarda. Sai ya ce: Haka yake[12].

Kwaurin Allah

Ruwayoyin ganin Allah sun gabata a bahasin ganin Allah da suka zo a littafin Buhari da suke nuni da cewa muminai zasu ga kwaurin Allah ranar kiyama kuma da shi ne zasu gane ubangijinsu. Wasu ruwayoyin sun yi nuni da cewa da Ubangiji ya yaye kwaurinsa sai kowa ya fadi ya yi masa sujada, babu wanda zai kasa sai mai riya da son jin yabon kansa[13].

Abin da ya fi komai mamaki a hadisan siffanta Allah madaukaki da kwauri shi ne cewar idan muminai suka zo ba sa gane shi, har ma suna yin musu da shi kan cewa shi ne Allah ubangijin bayi, daga nan ne sai ya bude kwaurinsa da ya rufe da bargon takama da mayafin ji da kai, sai su gane shi ne ubangijinsu sannan sai su yi sujada.

Mummunar fassarar da aka yi wa ayar nan mai cewa “…ranar da za a yaye kwauri…” ta sanya jingina wa Allah wannan gaBa. Maimakon mayar da wannan ma’anar ga harshen larabci da take nufin marhalar tsananin tsoro da firgici da fuskantar hadari. Larabawa suna fadin haka da nufin an kai marhalar da mutum zai dage zaninsa don ya gudu domin babu wata mafita da ta rage sai hakan. Don haka duk wata marhala da ta kai tsananin wahala to suna kiran ta da “… yaye kwauri…” domin idan ba a yaye shi ba to gudu ba zai yiwu ba.

Kamar dai fadin nan na larabawa cewa “قامت الحرب على ساق” wanda yake nuni da yaki ya kai matukar wahala da tsanani. Don haka yaye kwauri yana nuni da abin da muka kawo. Idan mun duba zamu ga kowane yare yana da kinayar da yake amfani da ita wurin isar da sakon sa.

Da Kur’ani ya sauka da yaren Hausa da bahaushe zai ji an ce masa “… ranar da aski zai zo gaban goshi…” ne. Kuma da masu wannan kanzagin da wuce gona da iri sun yi kokarin siffanta Allah da cewa yana da gashi mai yawa a kansa, kuma a wannan ranar ne za a kusa gama askin don haka aska ta zo gaban goshi ke nan. Ta yiwu ka samu wasu masu shisshigi su kirkiro hadisai da suke nuni da cewa ta keyarsa aka fara askin ko ta gefan kansa.

Don haka wannan karkata da kauce wa hanya madaidaiciya game da siffofin Allah madaukaki ta fada wa al’umma sakamakon nisantar su da wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ta biyayya ga littafin Allah da alayensa a bayansa.

Kafar Allah

A game da hadisin da ya zo yana bayani kan neman da jahannama take yi na a kara mata mazauna sai ruwayar take cewa ba zata cika ba har sai Allah ya sanya kafarsa cikinta sai ta ce ya isa!. Ruwayar ta zo da cewa jahannama ba zata koshi ba, don haka za a yi ta zubawa har sai da Allah ya sanya kafarsa a ciki sai ta cika ta yi magana cewar ta cika hakan nan.

Ruwayoyin da suka zo da wannan lamarin a cikin Buhari sun yi amfani da lafazin kafa, wasu kuwa sun zo da lafazin tafi ne. Kuma ko dai me ye ya kasance; kafa ce ko tafi, ba wa Allah madaukaki jiki da gaBoBi da wannan ruwayar ta yi shi ne babbar matsala[14].

Ba mamaki wasu mutanen su ce don me ya sa ba za mu yi tawilin wadannan hadisan ba don a samu wata mafita da wata ma’ana mai kyau da zasu bayar ta yadda zamu fassara su da bayanin da zai kore samuwar jiki ga Allah madaukaki?. Kamar mu fassara ma’anar yaye kwaurin Allah da wahala da tsanani da hadari da ake fuskanta, ko mu fassara ma’anar ganin sa da sauraron ni’ima kamar yadda gani yake da ma’anar sauraron wata ni’ima a harsuna masu yawa. Misali da harshen Hausa idan wani ya zo ganin wani babba a ofishinsa, to gani a nan yana nufin zai nemi wani abu da yake son samu wurinsa, ba kawai ya kalle shi da ido ba!.

Sai dai hakan ba zai yiwu ba a irin wadannan hadisan domin ‘yan Sunna ba su ruwaito wasu hadisai da za a fassara wadannan hadisai da su ba, don haka zamu lura da wasu abubuwan kamar haka:

1-Da an samu wasu wurare da suka ruwaito hadisai da suke nuna ba za a ga Allah da idanuwa ba misali, to a nan sai mu fassara hadisin ganin Allah da ido da waccan ma’anar, domin sai mu gane cewa ke nan wancan ganin ba na ido ba ne, yana nufin na sauraron ni’ima ne. Amma ba mu samu hadisai masu kore ganin Allah ba daga ‘yan Sunna, don haka babu wata hanyar tawili ke nan.

2-Ruwayoyin da suka ruwaito masu ba wa Allah jiki da Bangarori zamu ga suna karfafa ma’anar zahiri karara ba tare da sun bar wata hanyar da za a iya yin wani tawili ba. Misalin mutumin da aka hana marin sa saboda Ubangiji ya yi kama da shi, a nan da wane irin tawili za a fassara wannan ma’anar ta yadda zata fita daga ma’anar zahiri. Haka nan ganin Allah kamar yadda ake ganin wata daren sha biyar, ita ma yaya za a iya bayanin ta da ma’anar da zata saBa wa zahirin kalmar da take nufi?.

3-Idan mun duba wadannan ruwayoyin zamu ga ba tun yau suke ba, domin sun bayyana ne lokacin Buhari (w 256) zuwa Nisa’i (w 279) kuma su ne dai har yau muke karantawa a littattafan Sunna, don haka ba sababbi ba ne. Kuma a lokacin Imam Bakir, Imam Sadik, da Imam Ridha an kawo wadannan ruwayoyin an karanta a gabansu amma ba su nuna ingancinsu ba, balle kuma su yi tawilinsu, sai suka yi inkarin su kai tsaye, suka yi nuni da karya ce aka jingina wa manzon Allah (s.a.w). Da sun inganta daga annabin rahama (s.a.w) kuma suna iya karBar tawili da mun samu hakan daga jawabinsu.

4-Idan ma muka yi tawilinsu to zamu ga su malaman ‘yan Sunna da suka ruwaito su sun hana duk wani tawili kansu, suna masu kore duk wani bayani da zai yi tawilinsu ko ya kawar da su daga ma’anarsu ta zahiri. Don haka babu wata ma’ana ga wanda shi bai yarda da ingancinsu daga annabin rahama ba kuma bai yarda da abin da suka kunsa ba ya shiga yin tawilinsu. Masu ruwaito su suna ganin duk wani inkarinsu ko yin tawilinsu to saBa wa addini ne, wasu ma suna ganin sa zindikanci ko kafirci da fita daga mazhaba.

RA’AYOYIN ‘YAN SUNNA

Tayiwu wasu ruwayoyi su zo a littattafan Shi’a da zamu ga kamar suna da wata ma’anar bayar da jiki ko yiwuwar gani ga mahalicci da muke iya gani a Buhari da Muslim da sauran litattafan ‘yan Sunna, don haka wasu zasu iya cewa ke nan abin bai keBanta da malaman ‘yan Sunna ba. Sai dai akwai muhimman abubuwan da za a yi la’akari da su a nan kamar haka:

1. SaBanin Mahanga kan Ruwayoyi

Daya daga cikin muhimmin saBani tsakanin malaman ‘yan Shi’a da malaman ‘yan Sunna shi ne cewar malaman Sunna sun yarda da cewa duk abin da ya zo a cikin Buhari ko Muslim to ya inganta babu wani kokwanto. Kuma idan ma wani ya rantse kan cewa duk abin da yake ciki maganar annabi ce to babu kaffara kansa don rantsuwar ta inganta!. Amma malaman Shi’a ba su taBa yarda da samuwar wani littafi da duk abin da yake cikinsa ya inganta ba hatta da littattafai hudu nasu shahararru, don haka ne suke ganin wasu hadisan sun inganta wasu ba su inganta ba.

Don haka ne ma samuwar wasu hadisai marasa yawa a cikin wasu litattafansu ba ya damunsu sakamakon cewa a wurinsu ba su inganta ba kamar yadda malamansu suka yi nuni da hakan.

2. Hadisan Tauhidi

Idan mun duba litattafan hadisan Sunna zamu ga dukkansu suna da nuni zuwa ga sanya jiki ga Allah madaukaki kuma ba mu samu wani Hadisi daya ba wanda yake karyata wannan lamarin. Don haka ne zamu ga koyarwar da take cikinsu in ban da sanya jiki da gaBoBi ga Allah (s.w.t) babu wani abu da suke kunshe da shi. Amma a litattafan Shi’a akwai daruruwan hadisai da suke suka kuma suke kore duk wata magana da take nuni da samuwar jiki ko wata gaBa ga Allah madaukaki.

Akwai ma babobi da fasaloli da suke da “Take” kai tsaye kan wannan, kamar “Babin kore ganin Allah”, “Babin hani ga siffanta Allah da jiki ko wata sura ko motsi ko cirata”, “Kore kamantuwa”, da zamu ga irin wadannan kan bayanan fasaloli da babobi game da Allah madaukaki[15].

3. Hadisan Tauhidi gun Shi’a

Hadisan da suke kore duk wata sifa ta jiki ko gaBa ko kamantawa ga Allah (s.w.t) da suka zo a litattafan Shi’a sun bayani karara ta yadda babu wani kokwanto da ya rage ga wani daga malaman Shi’a kan wannan lamarin. Sun zo da sanadodi da bayanai masu karfi da dukkan maruwaita na ‘yan Shi’a suka sallama suka karBe su baki daya, kuma su ne kashin bayan tafiyar akidar shi’anci, kuma duk wata ruwaya da ta saBa musu to ba ta da wani matsayi ko kima gun malaman Shi’a balle har ma a yi magana kan ta.

4.Kirkirar Ruwaya

Idan muka duba ruwayoyin da suka zo da wani abu mai kama da hakan a cikin litattafan Shi’a zamu ga cewa ba su da wani sanadi mai kwari, wasunsu ma ruwaya ce ta wani malami daga malaman ‘yan Sunna mai imani da jiki ga Allah kamar Mukatil dan Sulaiman sai ya jingina ta ga jagororin Shi’a da suka gabata.

Don haka duk wani abu na akida game da sanin Allah da siffofinsa dole ne a koma wa maganar manyan malaman wannan mazhaba don tabbatar da me suke imani da shi. Kamar dai yadda ake koma wa litattafan Sunna da malamansu don sanin abin da suka yi imani da shi game da Ubangiji madaukaki.

Misalan Hadisan Shi’a

Hadisan shi’anci sun karfafa da yawan gaske cewa; ba a lissafa Allah da wuri da zamani, don haka bai halatta ba wani ya yi tambaya kan ina Allah yake ko yaushe ya kasance, domin wannan tambaya ce da za a iya yin ta ga wanda yake da dabaibayi da zamani da wuri. Haka nan ba a siffanta Allah da motsi ko tafiya, ko cirata daga wuri zuwa wani wurin domin Allah yana ko’ina da zatinsa, wani wuri ba shi da bambanci gunsa da wani wurin, sai dai ya sanya shamaki ga mutane gwargwadon yadda ya ajiye komai mahallinsa ne.

Don haka duk wani abu da yake siffantuwa da zamani, ko wuri, ko motsi, ko rashin motsi, ko cirata, duk suna daga cikin siffofin halittunsa ne masu iyaka masu bukatuwa zuwa wannan abubuwan. Domin zamani yana hawa kan abin da yake motsi ne, idan abu ba shi da motsi ba ya cirata to babu ma’anar zamani ko wuri gare shi. Allah kuwa ya barranta daga dukkan wadannan siffofin na masu iyaka masu bukatuwa zuwa wuri da zamani.

Abubasir ya karBo daga Imam Sadik (a.s) cewa: Ba a siffanta Allah madaukaki da zamani ko wuri, ko motsi ko cirata, ko rashin motsi, shi ne dai ya halicci zamani da wuri da motsi da rashin motsi, Allah ya barranta daga abin da masu zalunci suke fada[16].

Hatta da ayoyin Kur’ani masu yawa da suka zo bisa ka’idar luga da aro da kinaya kamar yadda zamu gani suna da kyakkyawar fassara da Ahlul-baiti suka yi musu. Misalin ayar nan ta “… Al’arshinsa ya kasance kan ruwa…”. Zamu ga Imam Sadik yana cewa da Dawud Rakki, me suke cewa ne?. Sai Dawud ya ce: Suna cewa: Al’arshi yana kan ruwa, shi kuwa Allah yana kansa. Sai ya ce: Duk wanda ya raya hakan ya yi karya, domin ya sanya Allah abin dauka ke nan, kuma ya siffanta shi da siffofin abubuwan halitta, kuma ya lizimce shi cewa abin da ya dauke shi ya fi shi karfi ke nan[17].

Ya’akub Sarraj yana cewa da Imam Sadik (a.s) daga cikin abokanmu akwai wadanda suka dauka cewa Allah yana da kama da mutum, yana da fuska, wani saurayi ne mai nadadden gashi. Yayin da Imam Sadik ya ji wannan magana sai ya yi sujada sannan sai ya dago kansa ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, babu wani abu da ya yi kama da shi, idanuwa ba zasu iya riskar sa ba, ilimin mutum ba zai iya sanin hakikaninsa ba, ba ya haihuwa balle a samu kamarsa domin kowa yana kama da babansa. Ubangiji ba shi da uwa da uba balle ya yi kama da wasu da suka gabace shi, ba shi da wani tsara a cikin halittu baki daya, kuma ya fi karfin ya siffantu da siffofin ababan halitta[18].

Yusuf bin Zanyana ya kai kukan abin da ya ji a majlisin Maliku cewa: Wasu suna cewa; Allah yana da fuska da jiki. Wasu ma suna cewa; yana da hannaye saboda ya ce da Iblis: “… Me ya sa ka ki yin sujada ga abin da na halitta da hannayena…”. Wasu kuwa suna cewa; Allah saurayi dan shekara talatin ne. Me zaka ce game da wannan magana tasu.

Sai Imam Sadik (a.s) ya yi raddin dukkan wadannan maganganu daya bayan daya. Ya jingina ya yi yabo ga Allah sannan sai ya yi kakkausan suka kan wadannan ra’ayoyin yana mai neman afuwar Allah da barrantar da shi da siffantuwa da wadannan siffofin a cikin wani Hadisi mai tsawo.

Hadisai game da tsarkake Allah daga dukkan wasu siffofin tawaya na halittu suna da yawa, kuma imamai daga alayen manzon Allah (s.a.w) sun yi bayanai masu yawa da suka zo a ruwayoyi masu yawan gaske da ba sa kirguwa kan wannan lamarin. Don haka duk wata tawaya da take komawa zuwa ga abin halitta da siffarsa shi’anci ya barrantar da Allah daga gare ta.

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] Buhari: j 5, h 3578. J 4, h 4707. Muslim: j 6, kitabul imara; b 35, h 1890. Muslim: kitabul a’ayan: b 83, h 273. Sunan Ibn Majah.

[2] (Muslim: j 2, Kitabu salatil musafirin; babut targib fiddu’a wazzikr, Hadisi: 758).

[3] (Musulim: j 2, kitabul hajj; b fadhlul hajji wal umra wa yaumu arafa.).

[4] Umdatul qari: j 7, b 14, sh 196 – 197.

[5] Buhari: j 8, h 5873. Muslim: j 8, h 2841. Muslim: j 8, h 2641.

[6] Buhari: j 8, h 5873. Muslim: j 8, h 2841. Muslim: j 8, h 2641.

[7] Tin: 4.

[8] Buhari: j 4, h 3256 – 3257. J 5, h 4141. Muslim: j 8, h 2933. Buhari: j 9, h 6983.

[9] Buhari: j 6 kitabut tafsir; aya 18, h 4407. J: 8, b 60, h 5721 – 5722. Muslim: j 8, h 2766 – 2768.

[10] Buhari: j 9, b 22, h 6983. B 19, h 6976, h 4407. Ibn Majah: j 1, b 13, fima an karat aljahmiyya. D.s.s.

[11] Buhari: j 6, b 297, h 4533 – 4534. Da wasu babobi masu yawa. Muslim: j 8, kitabu sifatul munafiqin, b sifatul qiyama wal janna wannar, h 2786.

[12] Buhari: j 6, kitabut tafsir: b 1, h 4552.

[13] Buhari: tafsir, b 24, h 7001, h 4635.

[14] . Buhari: j 6, b 33, h 4567 – 4568.

[15] (Kafi, Tauhidus saduq, Biharun anwar).

[16] Tauhid: Saduq; j 1, b 2, da b 8, sh 7- 31, da 9-107, da biharul anwar: b 13, da 14, sh 287, sh 309.

[17] Tauhid Saduq: Babul Arshi wal Kursiyyi.

[18] Tauhid; Saduq: babu nafyul jism wassura.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *