Tauhidi A Buhari Da Musulim

WASU MAS’ALOLI A BUHARI DA MUSLIM

Yanzu lokaci ya yi da ya kamata mu leka cikin Buhari da Muslim don mu ga wasu mas’aloli a mahangar koyarwar musuluci sahihiya musamman abin da ya zo daga gidan Ahlul-baiti zuriyar annabi (s.a.w). Wannan mas’aloli sun hada da na akida da na furu’a kamar haka:

TAUHIDI A BUHARI DA MUSULIM

A addinin Musulunci bisa koyarwar Ahlul-baiti Allah ba jiki ba ne, kuma ba shi da siffofin masu jiki, “babu wani abu da yake kama da shi” ingantattar koyarwar Musulunci ta nesanta Allah madaukaki da dukkan kama da wani abu daga bayinsa, don haka ba shi da jiki ko sura ko shakali ko kala ko halaye na bayinsa. Kura’ni ya karfafi wannan koyarwar ne kuma ya yi umarni da riko da ita saBanin litattafan da suka gabata da suka samu munanan fassara kan siffofin Allah. Idan mun duba zamu ga akidar sanya jiki ga Allah a littafin “Attaura”[1] a matsayin wata halitta mai jiki da yake saukowa duniya ya shiga hemar Yakub (a.s) don ya yi fada da shi, irin wannan akida ce Musulunci ya kore da harshe mai kaifi.

Amma sai ga shi muna samun akidar bayar da wuri da zamani ga Allah a Buhari da Muslim, har ya kasance Ubangiji yana rayuwa kan al’arshi ne kuma yana saukowa a wani yanki na dare zuwa wannan duniyar. Ga akidar yiwuwar ganin Allah da idanuwa, yana da siffofi irin na mutum kamar idanuwa, kunne, kafa, hannu, kuma wadannan siffofi nasa ba sa karBar wani tawili balle a yi musu wata fassarar a bisa mahangarsu.

Hadisin da yake nuni zuwa ganin Allah da idanuwa yana da yawa da sanadodi daban-daban, wannan hadisin ya zo a babobi masu yawan gaske da Buhari, duba kasa ka ga bayanansu masu yawan gaske[2].

1-Wannan hadisin ya kunshi abubuwa masu yawa da suka hada da Allah yana jirkita da wata siffa ba ta sa ba har muminai su yi musun sa shi kuwa sai ya fito musu da siffarsa ta gaskiya, wannan lamarin a bias gaskiya wasa ne da Allah ya barranta daga gare shi.

2-Ana ganin Allah da shakalinsa har ma ya yi hira da bawansa da zai ta jayayya da shi har da wayo ya shiga aljanna.

3-Ganinsa ga kowa zai zama mai sauki kamar yadda ake ganin wata a duniya, kuma dukkan al’umma da ‘yan wuta da aljanna duka zasu gan shi. Ba mu sani ba don me ya sa sai a can ne za a gan shi alhalin ko’ina ba shi da bambanci gare shi inda ana ganinsa!.

4-Yana sanya mayafin Takama da zanin Jiji-da-kai, kuma sai ya yaye zaninsa har sai an ga kaurinsa. Wannan yana nuna yana sanya tufafi ke nan kuma yana da kwauri da kafa da sauran gaBoBi.

5-Sannan wannan ruwayar tana nuna cewa Ubangiji yana cirata daga wuri zuwa wuri, yana da zamani, motsi, tsayi, kwauri, canji, da sauran abubuwan da suke siffofi ne na bayinsa.

Ruwayoyin yiwuwar ganin Allah da idanuwa su ne asasin da malaman ‘yan Sunna suka dogra da su wurin imani da hakan da sanya shi cikin wata mas’ala ta lalurar addini. Kusan dukkan malaman mazhabobin Sunna na furu’a suna karfafa wannan akida ta yadda ya kai ga shafi’i yana ganin idan da ba shi da yakini a wannan duniyar kan cewa zai ga Allah a ranar lahira to ba zai bauta masa ba[3]. Kamar yadda zamu ga a lokacin da Ash’habu ya tambayi Maliku game da kalmar “naazira” da Ahlul-baiti suka tafi a kan cewa tana nufin sauraro, sai Maliku ya ba shi amsa da cewa tana nufin gani ne, domin ya tabbatar da cewar kowane mutum zai ga Allah a ranar kiyama.

Mas’alar ta samu saBani mai yawa a cikin rassanta ta yadda wasu suna ganin cewa ganin Ubangiji ya takaita ne da lahira, wasu kuma suna ganin annabi ya gan shi a duniya a Mi’iraji, wasu kuma sun kawo cewa malamai ma suna iya ganin sa, wasu sun tafi a kan cewa ana ganin sa amma a mafarki har ma suna kawo wadanda suka gan shi a mafarki, wasu sun kawo ruwayoyin ayyukan da mutum zai yi idan yana son ya gan shi a mafarki, da sauran lamura masu ban al’ajabi. Mafi mamaki a nan yadda da yawa suka nuna mata da yara su ba zasu gan shi ba, idan ma zasu gan shi to a lahira ne kawai, wasu kuma suna ganin zasu gan shi duk shekara ne kawai kamar ranakun idi na lahira.

Wasu kuwa sun shiga cikin bahasin cewa shin ganin sa ya takaita da al’ummar annabi ne ko kuwa har da sauran al’ummu, wasu kuma sun shiga mas’alar cewa ‘yan jahannama zasu iya ganin sa ko kuwa sau daya kawai zasu gan shi a ranar lahira. Wasu kuma sun tafi a kan cewa har da muminai ba zasu gan shi ba sai ranar lahira kawai, amma bayan nan to sai dai annabawa kawai su gan shi. Mas’alar ta kasu gida-gida da kowa ya ga dama sai ya kawo ra’ayinsa da tunaninsa a matsayin addinin Allah. Wannan kuwa shi ne sakamakon da yake samun mas’alar da tun farko ba ta da asasi daga Allah ko manzonsa.

Wannan akida ta ganin Allah ta samo asali daga kuskuren tafsirin kalmar “naazira” ne, sai dai kuma kamar yadda muka sha nanatawa duk sa’adda aka samu wani ra’ayi to cikin sauki akan samu wasu su yi masa ruwaya don karfafarsa wanda yake son ya ga wannan lamari ya bincika mas’alolin Musulunci masu yawan gaske don ya gano asalin saBaninsu sannan kuma sai ya koma ya ga ruwayoyin da aka kirkira don kare wadannan ra’yoyin. To wannan mas’alar ta ganin Allah da idanuwa ita ma ta samu wannan yanayin ta yadda aka kirkiro mata hadisai don kare ta.

Mafi munin abu shi ne dokar da suka lizimta wa kansu ta cewa idan Hadisi ya saBa wa ayar Kur’ani to ana jefar da ayar Kur’ani ne a dauki Hadisi. Da wannan dokar ne aka bar mafi yawan ayoyin Kur’ani aka yi watsi da su a jujin tarihi. Idan mun duba zamu ga yadda Kur’ani ya soke duk wani gani na Ubangiji yayin da Allah madaukaki yake gaya wa annabi Musa (a.s) cewa: “Ba zaka taBa ganina ba” kuma ya sanya ganinsa ya ta’allaka da mustahilin abu don dai ya tabbatar da ganin sa cewa mustahili ne. Wato idan lamari na ya bayyana ga dutse na umarnin ya fashe sai kuma dutsen ya ki bin umarnina sai ya ki fashewa to zaka gan ni, sai kuwa Allah ya yi umarni ga dutse kuma ya bi umarnin ya tarwatse don ya tabbatar wa annabi Musa (a.s) cewa ba zai yiwu ya gan shi ba. Wani abu muhimmi a nan shi ne mu lura cewa annabi Musa (a.s) bai nemi ganin Allah da kansa ba, sai dai takurawar Banu Isra’ila da barazanar cewa idan an koma zasu gaya wa mutane babu wani Allah don ba su gan shi ba, wannan ne ya sanya annabin Allah Musa (a.s) ya yi wannan neman don ya nuna musu cewa ganin Allah mustahili ne, amma in ba haka ba Musa (a.s) ya fi karfin ya jahilci hakan. Don haka ne Allah ya sanya tsawa ta gama da su, sai Musa (a.s) ya roki Allah ya dawo musu da ransu, domin idan ya koma wa Banu Isra’ila ya ba su labarin abin da ya faru ba zasu yarda ba, zasu tuhume shi da cewar sai da ya zaBi manyansu baki daya sai ya je ya kashe su don ka da a samu wasu masu fada a ji sai shi kadai kawai, don haka sai Allah ya tausaya masa ya dawo da su, kuma zaBaBBun Banu Isra’ila suka ga ayar da take nuna akwai Allah mai karfi mai iko don haka ba zasu iya musun sa ko da kuwa ba sa iya ganin sa.

Sannan ayar nan ta surar An’am: 103, kai tsaye ta yi magana da cewar “Marsikai ba sa riskar sa” wacce take nuni da duk wasu marsikai na zahiri kamar ji, gani, shaka, taBawa, dandano, ba zasu iya riskarsa ba, haka ma marsikai na badini ba zasu iya riskar sa ba, don haka babu yadda kwakwalwa da zuciya zasu iya sawwala shi. A yanzu akwai wata aya da ta fi wannan lamarin fitowa a fili ta kore ganin Ubangiji (s.w.t).

Sannan ruwayoyin da suka zo daga Ahlul-baiti (a.s) baki daya suna kore yiwuwar ganin Allah madaukaki. Kuma mun san cewa su ne wadanda manzon rahama (s.a.w) da ittifakin ruwayoyin ‘yan Sunna da ‘yan Shi’a duka sun kawo cewa idan al’umma ta yi saBani to su ne zata koma musu. Hasali ma dukkan al’ummar musulmi sun ruwaito cewa manzon Allah (s.a.w) ya bar mana littafin Allah da alayensa a matsayin wasiyyarsa, don haka ke nan babu wani mai hakkin ketare wannan koyarawar tasu.

Idan da wani zai ce an samu karo da juna ke nan tsakanin ruwayoyin wasu malaman ruwaya daga malaman ‘yan Sunna da kuma ruwayoyin da suka zo daga Ahlul-baiti ta yadda ya yi shisshigi ya ketare fadinsu, to sai mu ce sai a koma wa Kur’ani mai daraja da yake nuni da cewa ba za a ga Allah ba. Idan muka koma Kur’ani zamu ga karara ya furta da cewa ba za a iya ganin Allah ba, amma masu cewa za a gan shi suna masu dogaro da ayar Kur’ani zamu ga duk suna riko da tawili ne, idan kuwa akwai bayyanannen dalili to babu wani mai hujjar da zai yi tawilin kalmar da ake saBani kan ma’anarta wanda ya dogara da akidar masu saBani ne don tabbatar da ganin Allah madaukaki. Don haka natija ke nan tana nuni da cewa ba za a iya ganin Allah ba bisa dokar ilimi.

Idan mun duba zamu ga kalmar “naazira” tana nufin mai sauraro, kuma akwai irin ta da yawa a Kur’ani da fadin Allah yake nuni da ita kamar a fadin Bulkis “… ni mai sauraro ce in ga me ‘yan sako zasu dawo da shi…” sai ta yi amfani da kalmar “naazira”. Haka nan zamu ga kalmomin da aka ciro su daga wannan kalmar su ma suna nuni da haka kamar fadinsa “… hal yanzuruna ill ta’awilah…” da fadinsa “… ma yazuruna ill saihatan wahidatan…” da sauran kalmomi masu yawa da zamu ga suna da ma’anar sauraro ne, sai ya zama ke nan wadannan fuskokin suna jiran ni’imar Allah ne, kamar yadda na kafirai suke jiran azaba ne a bisa dokar “mukabala” da masana ilimin Fasaha da Balagar larabci sun san wannan.

Idan mun duba ayoyin guda hudu zamu ga na azaba suna cewa ne “Wasu fuskoki kuwa a wannan ranar sun turBune. Suna da yakini azaba mai karya tsatso za a yi musu”. A mukabalar wadannan ayoyin zamu ga Allah ya rigaya ya kawo fadinsa madaukaki cewa: “Wasu fusaku a wannan ranar suna masu sheki. Suna masu sauraron ubanigjinsu”. Don haka idan da fuskokin muminai zasu ga Ubangiji ne to da sai fuskokin kafirai ya zama su ba zasu ga Ubangiji ba ke nan. Don haka tun da azaba fuskokin kafirai suke sauraro, to fuskokin muminai ma suna sauraron ni’imar Allah ne ba ganin sa ba.

Hada da cewa idan masu wannan ra’ayin suka ce muminai ake nufi zasu ga Allah a wannan ayar, ai kuma sun manta sun ce kafirai ma zasu ga Allah a wannan ranar, ke nan wannan bai keBanta da muminai ba. A nan sai mu tambaye su yaya zaku warware wannan maganar mai karo da juna da kuke yi. Don haka ko dai ku koma wa hakikanin zahirin Kur’ani da ya bayyana a fili na rashin yiwuwar ganin Allah da yin imani da koyawar manzon Allah ta hannun alayensa (a.s), ko kuma ku zama kuna magana mai warwarar juna da ba ku da amsar da zaku iya bayarwa.

Sannan me ye kuma na karfafar wannan mas’alar da mafarkin malamai, idan kuka ce manzon rahama (s.a.w) ya na farki da Allah (s.w.t) yana ganawa da shi a cikin mafarki to wannan yana bukatar dalili ingantacce da idan ya inganta to wani abu ne da za a sallama da shi. Amma da bai inganta ba me ye kuma zai karfafi mas’alar da wasu malamai zasu ce suna ganin Allah a mafarki, yaushe mafarkin da yake saBa wa asasin Kur’ani zai zama gaskiya, don haka mafarkin malamai na cewar sun gan Allah ba zai iya taimaka wa wannan mas’alar ba. Kamar yadda mafarkin Ahmad dan Hambal da Allah ba zai iya samar da wani dalili kan cewa za a iya ganin sa ba, kuma babu wani sako da zai ba wa Ahmad dan Hambal da zai zama hujja kan al’umma sai dai idan masu dogaro da sakon sun ba shi annabta sai su yi mana bayani[4].

Sannan raba wa kowa wuridi da zai yi duk sa’adda yake son ganin Allah (s.w.t) shi ma wasa ne da shari’a kawai[5]. Ubangijin da za a bayar da wuridi don ganin sa wannan wane irin Ubangiji ne? Sannan wadanda suka gan shi zuwa yau ko da wuridi ko ba wuridi wacce siffa ce da shi. Idan suka ce sun gan shi suka ba shi wata siffa guda daya ga take nuni ga iyakarsa, kalarsa, yanayinsa, girmansa, tsayinsa, fadinsa, da duk wata siffa da zasu ba shi, to kai tsaye mun san wadannan masu kage ne masu neman dulmiyar da al’umma da kautar da su daga shiriyar manzon Allah (s.a.w). Idan kuwa ba su ga komai ba sun rusa kansu, domin gani yana lizimta abin gani, idan kuwa babu abin gani to babu gani ke nan, sai ya zama wasa da harshe ne kawai da haifar da rudani cikin al’umma.

Don haka dalilin Kur’ani da ruwayoyin Ahlul-baiti da hankali duk suna goyon bayan cewa mustahili ne a ga Ubangiji madaukaki da mariskai sai dai gani da ma’anar yakinin rai mai haske da yake risker samuwarsa wannan ba ya koruwa gare shi madaukaki. Don haka ne zamu ga lokacin da wani malamin yahudawa ya zo wurin Imam Ali (a.s) yana tambayarsa cewa: “Shin ka ga ubangijinka da ka bauta masa? Sai ya ce: Kaiconka! Ai ba na bauta wa ubangijin da ba na gani. Sai ya ce: Yaya ka gan shi? Sai ya ce: Kaiconka! Idanu (mariskan gani) ba sa riskarsa da ganin kallo, sai dai zukata ne suke ganin sa da hasken imani”[6].

Don haka natijar wannan bahasin tana tabbatar mana bisa yakini cewa ganin Ubangiji kamar yadda ake ganin sauran abubuwan halitta masu jiki mustahili ne ba zai yiwu ba. Idan kuwa ya yuwu to ba Ubangiji ne aka gani ba, domin duk abin da aka gani sai yana daurantar mai gani, da iska a tsakaninsu, da haske da zai sanya hoton abin da ake gani, da fasila, da kasancewarsa jiki mai iyaka, da sauran sharudan gani tsakanin abin gani da mai gani.

Idan kuwa aka ba shi iyaka to a nan an ba shi dukkan siffofin halitta na Bangarori da gaBoBi, da dukkan wata siffa ta abin gani, sai ya tashi ba Ubangiji ba ke nan. Don haka ta kowane hali ba yadda za a yi a ga Allah madaukaki. Allah madaukaki ka girmama karfin mai ido ya gan ka ko ya sawwala ka a tunaninsa. Tsarki ya tabbata ga Allah.

BA WA ALLAH WURI

Duk abin da yake jiki ne yana bukatar wuri da zai ci, halittun da suke da jiki sakamakon suna da iya don haka suna bukatar wurin da zasu kasance a cikinsa. Don haka ne suke iya zama suna da jihar da suke da ita idan an danganta su da wurin ko dai su kasance a samansa ko a cikinsa ko kasansa ko gefensa da sauran jihohi. Siffantuwar abu da cin wuri yana nuni kai tsaye da cewar wannan abin yana da iya da ta iyakance shi, don haka zai karBi nuni da mariskai domin dan yatsa zai iya nuna shi, idanuwa zasu fuskance shi.

Akidar da aka samu daga alayen manzon Allah (s.a.w) ta yi matukar kore wa Allah samuwar wuri domin yana lizimta masa siffantuwa da siffofin bayinsa masu iyaka. Iyaka kuwa tana sanya shi mai bukatar wanda zai kammala shi domin duk mai iyaka yana da tawayar da yake bukatar wani abu daban ya kammala shi. Wannan kuwa yana sanya shi mai tawaya, tawaya kuwa tana kore ubangijintakarsa, sai ya tashi ke nan ba Ubangiji ba alhalin shi ne Ubangiji madaukaki.

Buhari da Muslim sun ba wa Allah iyaka ta hanyar samar masa da wuri, sun sanya shi wani abu ne da ake dauke da shi, ake kewaye da shi, domin idan ya kasance a kan gadon mulki da iko ne kamar yadda suke kawowa to wannan yana nufin yana da iyaka da abin da ya iyakance shi. Kuma yana nuni da cewa shi abin da dauka ne don haka akwai abin da ya dauke shi.

Allah a gaban mai Salla!

Wannan akida mai ba wa Allah wuri ce ta kai Buhari da Muslim imani da cewar Ubangiji yana tsayawa gaban mai salla don haka ke nan da bukatar a sanya wani abu da zai kare mutum daga gittawa ta gaban mai salla, kuma aka samu ruwayoyi a kan hakan da suke neman mai salla ya yi fada da mai gittawa ta gabansa a matsayin cewa shi shaidan ne.

A ruwayar Abdullahi dan Umar zamu ga wasu abubuwa da ba zasu karBu ba ga matsayin manzon daraja (s.a.w) yayin da ruwayar take nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) ya ga wani tofin yawo a gaban wurin da ake salla sai ya fusata ya ce: Idan mutum yana salla to ka da ya yi tofi ta gabansa domin Allah yana tsayawa gabansa yayin da yake yin salla. Kuma ruwayar ta nuna cewa manzon Allah (s.a.w) da aka fi sani ya fi kowa tsafta sai ya sanya wannan tofin cikin rigarsa ya share da ita[7].

Bari in yi nuni da wani muhimmin lamari kan hakan: A lokacin da Abuhanifa ya halarci wurin Imam Sadik (a.s) sai ga Imam Musa Kazim yana salla mutune suna wucewa ta gabansa, sai Abuhanifa ya dauka cewa ya samu hanyar da zai samu tawaya a gidan alayen manzon Allah (s.a.w) don haka sai ya ce yaya haka! Sai Imam Sadik ya yi masa nuni da cewa ya tambayi yaron. Sai ya jira sai da yaron wato Imam Musa Kazim ya gama salla, sai ya tambaye shi cewa: Kai yaro yaya ka bari mutane suna wucewa ta gabanka da ubangijinka. Sai Imam Musa Alkazim (a.s) ya gaya masa shi babu wani abu da ya ke wucewa tsakaninsa da ubangijinsa domin ubangijinsa ba jiki ba ne kuma ba shi da wuri.

Wannan muhimmin lamari yana nuna mana cewa ke nan ruwayoyin da suka zo kan sutura gaban mai salla ba su da wani asasi na inganci domin duk sun dogara kan cewar Allah yana da wuri ne wacce akida ce Batacciya, don haka ke nan duk wata ruwaya da ta ginu sakamakon Batacciyar akida da ta ci karo da Kur’ani ko Sunna da aka yi ittifaki kanta, ko wani dalili na hankali yankakke to ya zama dole a yi wurgi da ita kwandon shara, domin wannan yana nuna ke nan ba daga annabi take ba, kuma barin ta cikin addini zai zama ke nan sanya wani abu cikin addini alhalin ba ya cikinsa!.

Allah a Sama!

Kamar yadda ya gabata cewar duk wani abu da ake dauke da shi to ba Ubangiji ba ne, domin yana nuna bukatarsa ga wannan abin da yake dauke da shi, hada da cewa hankali yana hukunci da cewar wanda ake dauke da shi bai kai karfin mai dauke da shi wanda yake rike da shi ba, don haka idan Allah ya kasance a sama ke nan wannan yana nuni da karfin sama da yalwarta fiye da ubangijin talikai, wannan kuwa lamari ne da yake rushe akidar Tauhidi kai tsaye.

Amma duk da haka zamu ga ruwayoyi masu yawa da suke nuni da cewa Allah yana sama, masu ingantattun litattafai uku da wasunsu sun ruwaito hadisin da yake nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata baiwa cewa: Ina Allah yake? Sai ta ce: Yana sama!. Sai ya ce: Ni waye? Sai ta ce: Kai ma’aikin Allah ne!. Sai ya ce da mai ita: Ka ‘yanta ta domin ita mumina ce![8].

Allah a Al’arshi!

Akwai hadisai masu yawa da suka zo suna nuni da cewar Allah yana kan al’arshi kuma a can yake rayuwa, kuma al’arshin nasa ya kasance kan ruwa yake. Kusan kalmar al’arshi tana daga cikin kalmomin da masu ruwaya suka munana amfani da ita, domin kalma ce da take nufin “karagar mulki” da hausa. Idan aka ce sarki ya hau karagar mulki a shekara ta 2000 ana nufin sarki ya amshi tafiyar da mulki da juya lamurran kasa a shekara ta 2000. Karagar mulki a nan ba ta nufin wani gado ne da za a ga sarki ya dare kansa wanda gani na mariskan zahiri yake riskarsa. Sai dai lamari ne na luga da yare da aka munana amfani da shi, kuma masu kirkiro ruwayoyi suka samu dama kan hakan musamman masu ruwaya daga Yahudawa da Kiristoci da ma’abota kissoshi da suka yi tasiri a koyarwar ma’abota litattafai shida.

A fili yake cewa sau tari zamu ga wasu wurare masu yawa da aka samu irin wannan lamarin mai rudarwa ga wadanda ba su san addini ba, don karkatar da al’umma daga tafarkin sanin shari’a ta gaskiya da akida mai inganci. Kalmomi ne da hadisan manzon Allah (s.a.w) suka yi bayaninsu ta hannun wasiyyansa na gaskiya da suka yi nuni da su bisa yadda suka sauka amma sai aka samu wasu masu kauce wa tafarkinsu suka karBi ma’anarsu daga wadanda ba su san sakon manzon Allah ba. Idan muka duba sosai zamu ga kalmar “al’arshi” da ubangijin talikai ya yi nuni da ita kan cewa al’arshensa yana kan ruwa, zamu ga yana nuni kuma a wani wurin da cewa: “Kuma muka sanya komai yana rayuwa daga ruwa”!. Ashe ke nan al’arshi a nan yana nufin tafiyar da rayuwar komai a wannan duniyar daga ruwa yake. Kuma shi kansa ruwan ba ruwa ne da muke sha yayin kishirwa ba sai dai ruwa ne da yake nuni zuwa ga asasin da komai ya tsayu da rayuwarsa a kansa.

Amma sai ga wasu ruwayoyi masu nuna cewa Allah yana kan wannan al’arshin shi kuwa wannan al’arshin yana kan bayan wasu shanu masu tsananin girma. Wasu ruwayoyin kuwa suna nuni da cewa yana kan al’arshi, shi kuwa al’arshi yana kan wani kogi. Wasu kuwa suna nuni da cewa al’arshi yana kan sammai bakwai, kuma Allah ya yi masa nauyi kamar yadda mahayin rakumin da yake lauta masa kaya yakan sa shi wani kara, to haka ma al’arshi yake samun wannan karar alamar jin nauyi. Wasu kuwa suna nuni da cewa mala’iku hudu ne suke dauke da wannan al’arshin, kuma zai yi musu nauyi don haka zasu komai su takwas a ranar lahira saboda nauyinsa[9].

Allah a Gajimare!

A lokacin da kuma tambaya ta taso cewa to ke nan kafin Allah ya halicci al’arshi ina yake kuma?. A nan ne kuma sai aka samu wata hanyar da za a amsa wannan tambayar maimakon yarda da cewa wadannan ruwayoyin ba su da wani inganci. Sai masu amsawa suka kawo wasu ruwayoyin da suke nuni da cewa yana kan wani gajimare!.

Sai dai masu bayar da amsa sun mance abu guda cewar tambaya ba zata kare ba kuma ba zata gushe ba, domin wata tambayar zata sake fuskantar su cewa to ina Allah yake kafin kuma ya halicci wannan gajimaren. Idan sun kawo wani abu daban ba zasu tsira ba domin shi ma tambaya zata hau kansa. Amma idan sun tsaya kan akidar gajimare to ya lizimta musu ko dai su karBi cewa gajimare fararre ne don haka tambaya zata ci gaba ke nan. Ko kuma su bayar da amsar cewa gajimare maras farko ne wato azali ne kamar Allah sai wannan ya lizimta musu samun alloli da ubangizai masu yawa da ya wuce daya. Da wannan ke nan sun rusa akidar tauhidi mai kadaita Allah tilo.

Don haka matukar masu akidar ba wa Allah wuri suna riko da akidarsu to suna da abubuwa biyu a gabansu; wato tambayar da ba ta iya karewa har abada abin da muka fi sani da tasalsul, ko kuma yarda da kididdigar Allah wanda lamari ne wanda ya rushe Kadaitakarsa kai tsaye. Kuma duka wadannan akidoji guda biyu mustahili ne ga ubangijin talikai!.

***

Da wannan ne zamu ga wadannan ruwyoyin da suka kawo sun nuna samuwar wuri ga Allah madaukaki. Kuma yana cikin gajimare kafin ya yi sauran halittu, sai dai wannan gajimaren Ubangiji ne shi ma? ko kuma shi ma abin halitta ne? Wannan ne lamarin da ba su yi bayaninsa ba.

Kuma ruwayoyin sun nuna cewa bayan Allah ya yi halitta ne ya zaBi al’arshi a matsayin wurin zamansa. Kuma da ya zauna kan al’arshi saboda nauyinsa sai ya rika yin wata kara. A cikin wannan akwai ba wa Allah nauyi alhain ba shi da nauyi kuma ba shi da rashin nauyi duka baki daya.

Sannan wadannan ruwayoyin sun nuna cewa Allah ya canja wuri bayan ya yi halitta daga gajimare zuwa al’arshi. Kuma duk lokacin salla yana canja wuri ya taso daga kan al’arshi ya zo ya tsaya gaban masu salla. Ke nan Allah ko da yaushe yana cikin zirga zirga ne daga wuri zuwa wani wuri.

Wadannan abubuwan baki daya suna nuna mana cewa Allah jiki ne domin al’arshi yana kan kahonin shanu, ko kan kayar kifi, ko kan sarari, ko a hannun mala’iku, ko kuma a kan sammai. Kuma a kan kome ma yake to lallai shi jiki ne ke nan, kuma ubangijin da yake bukatarsa yana zama shi ma jiki ne ke nan.

Malaman ‘yan Sunna daga ma’abota mazhabobi hudu sun tafi a kan cewa Allah yana kan al’arshi abin da yake tabbatar masa da iyaka da jiki da sauran siffofin halittu. Hatta da Ahmad dan Hambal lokacin da ake tambayarsa kan ayar nan da take cewa: “Yana tare da ku duk inda kuke…” sai yake nuni da cewa Ubangiji yana kan al’arshi sai dai wannan ayar tana nufin yana kewaye da komai ne domin dai ya tabbatar da cewa Allah yana kan al’arshi ke nan.

Abuhanifa ma yana karfafa cewa Allah ba ya kasa yana sama ne, kuma Baihaki ya karfafi wannan maganar ta Abuhanifa yana mai karfafa cewa lallai Ubangiji ba ya kasa, kuma lallai yana sama ne[10]. Haka nan Maliku da Shafi’i suna karfafa wannan lamarin na cewa Allah yana sama yayin da suke karfafa cewa Allah yana kan al’arshi ne.

Asalin wannan akidar ta taso ne daga dogaro da ruwayoyin da suka zo da wannan akidar, ruwayoyin da suka zo da yiwuwar ganin Allah da wadanda suka ba shi wuri da suka karBo daga Abuhuraira da waninsa su ne suka haifar da wannan akidar. A bisa asalin da suke dogara da shi maimakon duba ayoyin Kur’ani da koyarwarsa da abin da ya zo daga alayen annabinsa (a.s) sai suka shiga dogaro da wadannan ruwayoyin da tawilin ayoyin Kur’ani don su yi daidai da abin da ya zo a ruwayoyin da suka nakalto[11].

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] Attaura: Kitabut Takwin, fasali 32, jumla 26-30

[2] Buhari: j 1, h 529, h 547. J 6, h 4570, j 9, h 6997, 6999. Muslim: j 2, h 633. Da wasu babobi masu yawa.

[3] Tabaqatus shafi’iyya: j 2, sh 17.

[4] Manaqibu ahmad: sh 434.

[5] Sunan Darumi: j 2, sh 126.

[6] Kafi: j 3, babu ibtalur ru’uya.

[7] Buhari: j1, ba 33, h 397, 398. Muslim: j 2, h 547. Ibn Majah: kitabus salah, b 61.

[8] Muslimi: j 2, h 537. Abu Dawud; j 1, kitabus salah, babu tashmitul atishi. Nisa’i: j 2, kitabul Iman.

[9] Abu Dawud: j 4, babul Jahmiyya. J 1, babi 13. Ibn Majah: j 1, b 13. Da wasu littattafai masu yawa.

[10] Al’uluwwu lil’aliyyil gaffar: sh 101, 103, 120.

[11] Fathul majid: aya 67; kitabut tauhid: sh 213.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *