MA’ANONIN (CONCEPTS) FALSAFA

Ma’anonin Kalmomin bincike da Jumlolin da kowane ilimi yake amfani game da su suna da alaka da jigon bahasinsa ko hadafinsa ne. Mafi yawan Ilimomi sun kasu bisa asasin jigo (subject) ne fiye da yadda aka kasa su bisa asasin hadafi, don haka ne jigon bahasi ya kasance shi ne yake ayyana nau’in kalmomi da jumlolin bahasinsa.

Misali tun da ilimin yare yana bahasin ne kan yare, to jigonsa shi ne yare, kuma jumlolin da suke bahasi kan wannan yaren suna duba wannan jigon ne don bahasi kansa. Misali idan yaren larabci ne, to dole zasu duba kalma ce a larabci a matsayin jigon bahasi, kuma zasu duba kashe-kashen kalma, da nau’in kalma, da li’irabinta, daidai sakamakon yanayin da binciken yaren larabci yake da shi.

Amma ilimomin da suke bincike game da nazarin tunanin dan’adam (theoretical concepts) sun kasu gida uku ne. Sai dai hanzari ba gudu ba, kashe-kashen yana kebanta da Falsafar Musulmai ne, wannan wani abu ne da malaman Falsafa na musulmai suka kebanta da shi. Sau da yawa wasu matsalolin tunani da ake fama da su a Falsafar yammancin duniya babu su a cikin Falsafar musulmai saboda suna da warwara kan matsalolinsu. Kuma wannan zai bayyana sosai a lokacin da zamu shiga cikin kiyasi tsakanin tunanin yammancin duniya da na musulmai kan mas’alolin Falsafa.

Wannan rashin wadatuwar da ya fuskanci Falsafa a yammacin duniya ne ya sanya su samun mazhabobin tunanin Falsafa barkatai ta yadda suka rasa wata madafa da wata mahada da zata hada su, kuma da sannu wannan ma zai bayyana a bahasosin da zamu fuskanta nan gaba.

Idan mun dawo kan maganarmu muna iya cewa; ma’anonin Jumlolin da ake amfani da su a binciken ilimin nazari da tunanin dan’adam (theoretical concepts) sun kasu gida uku ne:

a- Ma’anonin da ake samun su ta hanyar fara kallon abin da yake da samuwa a zahiri, sannan sai a yi bincike kansa don a san ma’anarsa, kuma abubuwan da muke riska a zahiri su ne suke siffantuwa da wannan ma’anar. Mutum, doki, bishiya, cokali, zinare, littafi, gida, magani, duk kalmomi ne da zasu iya zama misali a nan.

Idan muna son sanin ma’anar da mutum ta kunsa, sai mu koma wa daidaikun mutane mu ga yaya suke, bisa asasin rayuwar mutum ne zamu tsaya mu yi nazari (analysis), mene ne shi, yaya yake, me ye bukatunsa, a ina ne ya yi tarayya da sauran halittu, a ina ne kuma ya bambanta da su, sannan sai mu samu natija kan mene ne mutum.

A nan da farko mun kalli daidaikun mutane da suke da samuwa a zahiri don gano ma’anar mutum, kuma mutanen da suke rayuwa da muke iya gani su ne suke siffantuwa da ma’anar da aka samu a wannan binciken. To haka nan ne bincike kan wadannan kalmomin mutum, doki, bishiya, cokali, zinare, littafi, gida, magani, da sauransu yake gudana. Ma’anonin da ake samu daga irin wannan binciken ana kiran su da ma’anonin Farko (primary intelligible).

b- Ma’anonin da ake koma wa tunanin dan’adam domin sanin su, da farko zamu samu  ma’anonin Farko da zamu yi tunani kansu (analysis), sai mu duba alakar wannan ma’anar da wasu ma’anoni don gano matsayinta da siffofinta. Wannan lamarin duk yana faruwa a kwakwalwa ne, kuma natijar bahasin tana kallon kwakwalwa ne, don haka samun wannan ma’anar yana farawa da tunani  (analysis), kuma natija ma tana cikin tunani.

Misalin irin wadannan ma’anonin kamar nau’i (species) ko jinsi (genus) da ake amfani da su a ilimin mantik (logic), sai mu ce: mutum nau’i ne, mai rai jinsi ne.

Nau’i shi ne abin da yake abu daya ne yake siffantuwa da shi kamar mutum da daidaikun mutane ne suke siffantuwa da wannan ma’anar kawai. Misali sai mu ce; Ali mutum ne, Zaid mutum ne, Bulkis mutum ce.

Jinsi shi ne abin da abubuwa masu yawa suka yi tarayya cikinsa kamar kalmar mai rai a misalin da muka kawo. Don haka Jinsi shi ne abin da abubuwa mabambanta masu yawa ne suke siffantuwa da shi, kamar doki, zaki, mutum, kare, saniya, da sauransu. Misali sai mu ce: Mutum mai rai ne, doki mai rai ne, kare mai rai ne.

Mantik da Lissafi su ne ilimomin da ma’anoninsu suke haka, don haka suna kallon ma’anonin farko ne tukun da muke da su a tunani ba a zahiri ba, sai kuma su yi tunani kan su don su samar da wata ma’ana ta biyu da ma’anonin farko suke sifantuwa da ita. To wannan ma’anar ta biyu da aka samu  ita ce ma’anar da suke kafa yaren iliminsu a kanta.

Misali idan muka samu ma’anar doki da take ma’ana ta farko, sai mu yi tunani kanta don mu gano cewa ma’anar doki nau’i ce ko jinsi, bayan mun yi bincike kan abin da ta kunsa sai mu ga nau’in abu guda ne yake siffantwa da wannan ma’anar ta doki, daga nan ne zamu gano cewa ma’anar doki nau’i ce ba jinsi ba sakamakon cewa abubuwa masu sabani a nau’insu ba sa siffantuwa da ita sai abu kala daya mai nau’i daya kawai.

Bahasin lissafi ne yake tarayya da mantik a cikin irin wannan bahasin sakamakon cewa lissafi a tun farko mas’ala ce ta Mantik, don haka ne zamu ga bahasin Lissafi (mathematic) yana da yanayi irin na Mantik (logic) ne, saboda haka idan lissafi ya ce: 1 + 1 = 2, zamu ga cewa; 1, +, 1, =, 2, duk babu ko daya da yake da wata samuwa ta zahiri duk baki dayansu a cikin tunanin kwakwalwar dan’adam suke.

Wani abin da isa mamaki game da hakan shi ne kakan samu mutum ya yi masters kan lissafi amma bai fahimci hakan ba sakamakon ya cakuda tsakanin kirga (adadi kamar 1, 2,) da kuma abin kirgawa (ma’adud kamar lemo daya, da biro biyu), sai ya dauka kirga (adadi) shi ne abin kirgawa (ma’adud). Bai fahimci cewa wadannan dokokin na lissafi a tunani kawai su ke ba, sai dai idan ana so a yi amfani da su a zahiri to sai a dauko wadannan dokokin domin yin amfani da su.

Don haka a misalin da muka bayar idan ana son a yi amfani da shi a zahiri sai a samu lemo daya a hada da wani lemo daya to zasu bayar da lemo biyu wannan shi ne abin da zamu iya samu a zahiri, amma lamba daya (1) da lamba biyu (2) da hadawa (+) da daidaito (=) duk babu ko daya da yake waje a zahiri duk a tunani suke kawai.

Ilimin mantik da lissafi  masu irin wannan bahasin ana kiran ma’anonin da suke amfani da su “ma’anoni na biyu na-mantik” (secondary logical intelligibles). A lura sosai ana kiran su da na biyu (secondary) ne saboda suna samuwa ne bayan an yi bincike kan na farko (primary).

Sai a jumlolin da Mantik yake amfani da su zamu ga jigon (subject) na wadannan jumlolin ma’anoni na farko, amma bayanau (predicate) da suke amfani da shi zamu ga ma’ana ce ta biyu (ta-mantik). Wannan bayanin zai fito sosai ne sosai idan da bahasin mantik muke yi, don haka sai a rufe shi ka da a tona sai ranar da bahasin mantik ya gudana.

Bahasin mantik a tunani yake, kuma abubuwan da suke siffantuwa da natijar bahasin su ma a tunani ne kawai suke, babu wani abu a zahiri a waje duk suna cikin kwakwalwa ne. Ko da yake akwai wasu malaman yammacin duniya da suka saba wa wannan ra’ayi, kuma bahasi kan hakan zai zo a lokacin da muka kutsa wa bayanin ilmin Mantik.

c- Ma’anonin da ke samun su ta hanyar tunani kan alaka tsakanin wasu ma’anonin da suke cikin tunani tun farko, misali mu yi tunani cewa duk sa’adda muka samu ma’anoni guda biyu kamar ma’anar wajibin samuwa da mai yiwuwar samuwa, to alaka tsakaninsu zata kasance ta mai samarwa da abin da aka samar, wato wajibin samuwa shi ne mai samarwa shi kuwa mai yiwuwar samuwa shi ne wanda aka samar.

Ko kuma duk lokacin da aka samu wata ma’ana da take cikin tunani da siffofin da ta kunsa, misali kamar mu yi tunanin cewa duk wani abu da muke da shi a tunani to ko dai  ya zama yana siffantuwa da cewa shi mai yawa ne ko guda daya, ko fararre ne ko azalalle, ko samamme ne ko rasasshe.

Duk wani lamari na koma wa tunanin dan’adam domin warware (analysis) mas’alar dalilin hankali domin samun tunani mai inganci da zai kai mutum zuwa ga samun yakini, amma natijar bahasin ana samun wasu abubuwa da suke siffantuwa da ita, to irin wannan bahasin yana kunshe da irin wadannan ma’anonin. Kuma ilimin Falsafa (Philosophy), Akidoji (Ideology), da Irfani (Mysticism), suna amfani da irin wadannan ma’anonin don kawo dalili kan samuwar abu ko kore shi.

Sai dai a lura sosai akwai sabani mai yawan gaske tsakanin Falsafa (Philosophy), Akidoji (Ideology), da Irfani (Mysticism), duk da cewa suna amfani da irin yare daya, sai dai salon bahasinsu ya bambanta matukar gaske, kamar yadda kowannen daga cikinsu yana da irin natijar da yake kaiwa gare ta, sai kuma sabanin Jigo (subject) din bahasoshinsu, don haka ka da a cakuda. Kuma da yardar ubangiji idan mun samu lokaci nan gaba zamu shiga bahasin da ya shafi kwatantawa tsakanin wadannan ilimomi guda uku don mu ga bambance-bambancensu a fili.

Idan muka dauki ma’anar mai samarwa (cause) da kuma abin samarwa (caused) zamu samu cewa ma’anoni ne guda biyu da idan aka kawo su a tunanin dan’adam zamu samu cewa mai samarwa yana da wani tasiri kan abin samarwa, hasali ma samuwar abin samarwa daga mai samarwa take kaco-kaf.

Hankali yana ganin cewa babu yadda za a yi abin samarwa ya samu sai da mai samarwa domin babu bazata (incidence) a samarwa, domin a samuwa ko dai a samu larura -wajabci- (necessity) ko kuma a samu yiwuwa (possibility), don haka bazata (wato samuwar abu ba tare da mai samarwa ba da aka fi sani da (incidence), korarre ne a tunani atafau. Sai hankali ya yi hukunci da cewa duk wani abin samarwa dole ne ya kasance akwai mai samar da shi.

Hankali yana ganin; duk wani abin samarwa babu yadda zai kasance mai dogaro da kansa dole ne samuwarsa ta jingina da wanda ya samar da shi.

Hankali yana ganin cewa;  Duk wani abu na kamala da abin samarwa yake da shi -da ya bubuugo daga kamalar samuwarsa- to wannan kamalar akwai ta da daraja mafi kololuwa a gun mai samar da shi.

Bayan hankali ya gama wannan warwarar (analysis) sai kuma ya duba alakar da take tsakanin samammu na zahiri, sai ya ga misali wuta da zafi suna iya siffantuwa da cewa wuta mai samarwa ce ga zafi, zafi kuwa abin samarwa ne daga wuta, sai ya yi hukunci da cewa ba yadda za a yi zafi ya kasance ko ya wakana sai da samuwar wuta. (a lura sosai cewa abin nufi a nan zafin da yake daga wuta ban da sauran zafi). Daga nan ne sai ya yi hukunci da cewa ba zai yiwu zafi ya kasance ba sai da wani dalili mai samar da shi, sannan duk wata kamala da zafi yake da ita to wuta tana da shi sama da hakan domin komai nasa daga gare ta yake.

A nan zamu ga bahasin ya fara ne daga ma’anoni da kalmomin da suke a tunanin dan’adam, amma daga karshe sakamakon yana koma wa abin da yake da samuwa ta zahiri ne, a kan haka ne bahasosin Falsafa suke tafiya.

Gwani kuma kwararren da ya kamata kowa ya rusuna masa a Falsafa, shi ne wanda yake da gaskiya mai cike da yakini a bahasinsa, wanda ya iya bayanin ma’anonin da suke kunshe cikin wadannan bahasosin, sannan kuma ya iya fassara samuwar samammu kamar yadda take ba dadi ba ragi. Shi ne wanda abin da yake kwakwalwarsa da abin da yake a zahirin samuwa baki daya ya zama kamar madubi ne da surar da take cikin madubin, kamar yadda Mulla Sadara yake kawowa.

Don haka duk wanda ya iya nuna tsarin samuwa tun daga samuwarsa madaukaki (s.w.t) har zuwa samuwar wannan duniya kamar yadda take, shi ne kan gaskiya, kuma dole ne ya kasance bisa yakini a hankalce domin babu zato ko kokwanto a Falsafa, da kokwanto ko zato sun zo, to sun rusa dalilin hankali kai tsaye.

Ma’anonin da ilimin Falsafa yake amfani da su suna da matukar yawan gaske, sai dai mun yi bayanin mafi girman rukunin yadda ma’anonin bahasinsa a fadade yake don ya sauwake wa mai karatu sanin yadda amfani da su a ilimin Falsafa yake gudana. Sannan yana da muhimmanci a san cewa Falsafa da ma’anar da muke bincike ta saba da Falsafa da ma’anar da ake bincike a yau a yammancin duniya, sai dai hakan na iya bayyana ne ga wanda ya san duka biyu, sannan zai sake bayyana yayin da bahasin ya kai mu ga Falsafa a yammacin duniya.

Falsafa ma’ana ce da ake amfani da ita a mas’aloli daban-daban, ana amfani da ita a Hikimar Ilimomi kamar yadda muka kawo a farko misalin Hikimar Siyasa (Philosophy of Politics), Hikimar Rayuwar Al’umma (Philosophy of Sociology), da ake bincike a yau a yawancin jami’o’i  da cibiyoyin ilimi. Ana amfani da ita a ilimin Gwaji (Emprical Sciences), kamar yadda ake amfani da ita a Ilimin Salo (Methodology), wadannan ilimomi ana kiran su da ilimin Falsafa.

Sai dai mu zamu karfafi bincike ne kan ma’ana ta hudu wato duk wani ilimi da ba na gwaji ba, don haka ma’ana ce mai fadi da ta kunshi Ilimin Mantik, Ilimin Sani, Ilimin Samuwa, Sanin Allah, Sanin Rai, Ilimin Kyau, da sauransu domin hannunmu ya zama a bude, sai dai zamu fi karfafar bincikenmu kan ma’anar Falsafa da ma’ana ta biyar da ta kebanta da ilimin samuwa.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

5 comments

  1. Ahmad Aliyu Al-Kashnawiiy

    Slm!Mlm #Hafiz_Muhammad.Dan Allah kai mana cikakken bayani akan ilmin Mandiq(Logic).

    • In Allah ya so.

    • Ilimi ne da yake bincike kan dokokin tunanin mutum don kare shi daga fadawa cikin kuskure yayin tunani ko kafa dalili a hankalce.
      Sauran bayanai sai mun yi nisa a cikinsa. Ka tanadi Telegram a lokacin don jin audio. Amma fa sai an jira.

  2. Ahmad Aliyu Al-Kashnawiiy

    Wai ka gama bayani ne akan ilimin Falsafar?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *