JIGON ILIMIN FALSAFA

Jigon magana (subject) a ilimin Falsafa ya gabata shi ne samuwa, sai dai abin nufi da samuwa a nan ita ce samuwa ta bai-daya, ko samuwa kamar yadda take, kuma muna iya kiran ta samuwa a dunkule (unibersal) ba kebantacciyar samuwa (non-unibersal) ba. Misali Ilimin Falsafa yana bahasi kan samuwa a tunani (mental edistence) ko a waje (edternal edistence), samuwa daya (unit) ko mai yawa (multiple), samamme a yanzu (actibe) ko nan gaba (potential), samamme na wajiba (necessary being) ko ba wajiba ba (possible being), ko samamme maras yiwuwa (impossible), samamme maras farko (pre-eternity) ko mai farko (temporal), samamme mai tabbata (affirmed) wanda ba ya samun canji ko motsi, ko mai motsi (mobement), samamme mai samarwa (cause) ko wanda aka samar (caused), samamme maras jiki (non-material) ko mai jiki (material), samamme mai zaman kansa (Independent) ko maras zaman kansa (dependent), samamme maras damfaruwa (substance) ko mai damfaruwa kan wani (accident), samamme a hankali (intellect) ko a zahiri (actual), ko bahasi da bayanai game da abu maras samuwa (non-edistence) ko mai samuwa (edistence). Mafi girman bahasi shi ne bahasi kan samuwa (edistence) da zatin samuwa (kuiddity) a matsayin asasin bahasin Falsafa a matakin farko.

Akwai daruruwan bahasosi karkashin wannan jigon bahasi wanda a cikin tsawon binciken Falsafa zamu kawo wasu in Allah (s.w.t) ya tsawaita mana rayuwa da bayar da lokaci. Don haka a nan ne zamu gane cewa misali Falsafa ba zata yi maka bahasi kan wani mutum daya ba kamar Ali, sai dai zata yi maka bahasi kan mutum; samuwarsa, zatinsa, hakikarsa, wajabcinsa ko rashin wajabcinsa. Ba zata yi maka bahasi kan halin Ali ba misali, amma zata yi maka bahasi kan halin Mutum ta fuskacin samuwarsa.

A nan ne zamu ga bambancin jigon da Irfani yake magana a kansa wanda ya hada duk samuwa ko a dunkule ko a daidaku sabanin na Falsafa. Sai jigon binciken Irfani ya zama (mutlakul maujud) domain babu wani abu da ya fita daga cikinsa ko da kuwa kwayar zarra ce, amma na Falsafa kuwa ya kasance (al-maujudul mutlak) domin yana kallon samuwa a bai-daya ne.

Sannan babu wani ilimi da ya isa ya yi magana har sai Falsafa ta tabbatar masa da samuwar Jigon da yake bincike a kansa, don haka ne ma ake kiran Falsafa Uwar ilimomi baki daya sakamakon hakan. Kamar yadda babu wani ilimi da ya isa ya fada fagen kafa hujja da dalili na hankali sai ya koma wa dokokin Mantik wannan lamari ne ya sanya ake kiran ilimin Mantik da Uban duk ilimomi, kuma hatta da ilimin Falsafa da duk wani ilimi dole ne su yi amfani da dokokin tunani da ya assasa a bahasinsu don kai wa ga yakini.

Jigon bahasin Falsafa sakakke ne ba ya zama kayyadajje mai kaidi ko kebantauwa da wata samuwa ta daidaiku. Ilimin Falsafa a misali yana bahasi kan jiki sakakke na bai-daya maras wani sharadi da dabaibayi (obsolute body) wanda ya hada da jikin mutum, dabbobi, tsirrai, ma’adinai, jiki a tunani (Mathematical Body). Amma ba ya kebantuwa da bincike kan kowane dayansu dalla-dalla domin aikin wasu ilimi ne, don haka idan Falsafa ta tabbatar da samuwar jiki da iyakokinsa ne, sai kuma sauran ilimomi kowanne ya dauki bangaren Jigon bahasin da yake bayani kansa.

Misali jikin mutum da dabbobi, yana zama mahallin bahasin likitanci (physic), idan ka hada su da jikin tsirrai su duka sun zama jiki a zahiri (natural body) sai su samar da mahallin ilimin rayayyu (Biology), tsirrai kawai suna iya zama mahallin jigon binciken ilimin tsirrai da shuka (Agriculture). Shi kuwa jiki a tunani (Mathematical Body) sai ya kasance mahallin binciken ilimin Fasahar kere-kere (Technology) a matsayinsa na jiki hadadde ko kuma adadi hadadde (continuous kuantity) kamar yadda ake kiran sa a ilimin Falsafa, idan kuwa ya kasance jiki rababbe ko kuma adadi rababbe (discrete kuantity) kamar yadda ake kiran sa a ilimin Falsafa, sai ya kasance mahallin jigon bahasin ilimin Kidaya (Mathematic and Arithmetic).

Siffofin Jigon Falsafa

Falsafa ilimi ne da yake bincike kan sakakkiyar samuwa ko kuma muna iya cewa sha’anonin samuwa na-baidaya, su mas’aloli ne da jumloli da suka shafi samuwa kamar yadda take. Bahasin samuwa kamar yadda take kuwa ba a iya tabbatar da shi a wani ilimi. Samuwa a matsayinta na samuwa abu ce da sirrin halittar da Allah ya yi wa mutane suke riskar ta, don haka ba ta bukatar dalili don tabbatar da ita.

Da wani bayanin mafi sauki babu wani dalili da ake iya kawo wa don tabbatar da Jigon bahasin ilimin Falsafa domin shi jigo ne mai tabbata da kansa. Da kuwa ya bukaci wani dalili, da bai kasance asasin duk wani jigon wani ilimi ba. Idan muka kaddara cewa wani ilimi ne zai tabbatar da jigon bahasin Falsafa, shi kuma wancan ilimin a lokaci guda yana bukatar Falsafa don tabbatar da jigon bahasinsa wannan ya zama gewayo ke nan wanda yake mustahili ne.

A dunkule mun fahimci cewa babu wani ilmi da ya isa ya kafa dalili don tabbatar da jigon bahasin Falsafa domin shi jigo ne mai tabbatuwa da kansa. Samuwa wata abu ce wacce riskarta yake cikin sirrin halittar mutum, babu wani wanda ba ya riskar samuwa ta bai-daya ko da kuwa bai taba karatu ba. Hatta da sabon mutum sabuwar haihuwa yana da wata riskar samuwa a wani mikidari gwargwadon samuwarsa, haka nan sauran halittu.

Sannan jigon bahasin Falsafa ba ya karbar wani salon bincike sai na hankali, ilimin Falsafa ilimi ne da yake kan tsarin bincike na salon hankali. Ilimi ne da ya doru kan salon binciken hankali da yake shi ne kawai zai iya amfani a fagen Falsafa, kuma a bisa gaskiya na bi duk wani bahasin da addini ya kawo shi kan samuwa ban taba ganin ya yi bahasi kan samuwa ba yana mai dogaro da nakaltowa. Kur’ani da yake gabanmu hujja ce kan hakan, bai taba yin bahasi kan samuwa ba yana mai kama hujja da nakaltowa tare da cewa ya zo daga ubangijin talikai, sai dai yana yin bahasin samuwa ne bisa salon hankali.

Ilimomin gwaji da nakaltowa ba sa iya kai mu ga yakini a kan kore samuwar wani abu ko tabbatar da shi. Ilimomi ne da ba zasu iya tabbatar mana da asasin samammu ba, ba a fagen samuwar ubangiji maras iyaka ba, ba kuma a fagen samuwar halittar hankula da shari’a ta ke kiran su da mala’iku, ko fagen samuwar mala’ikun kasa da muka fi sani da rauhanai, ko fagen samuwar rayukan mutane da sauran halittu, ko kuma a samuwar aljanu a matsayinsu na samammu masu jiki mai taushi.

Duk wani abu da yake maras jiki kamar ubangijin talikai ko mala’iku, ko rayuka, ko kuma ya kasance mai jiki mai laushi kamar aljannu ba sa iya karbar tabbata ko korewa ta hanyar gwaji balle kuma su kai mu ga samun yakini. Sakamakon haka ne zamu ga babu wani ilimi da zai iya wannan binciken ya kai mu ga yakini sai ilimin da yake aiki da salon hankali da tunani mai yakini.

Salon binciken hankali fage ne na ilimin Falsafa da Mantik da mathematics, sai dai da yake Mantik da maths suna bahasi ne kan dokokin hankali da tunani ne da muna iya kiran su samuwar ma’anoni ko samuwar da take cikin tunani da wata ma’anar, shin wannan ma’anar tana da samuwa ta zahiri a waje ko kuwa babu wani abu da yake siffantuwa da ita a samuwar zahiri.

Sai fagen samuwa ya kebanta da bahasin Falsafa, yayin da Mantik da maths suka mike kafa wurin samar da tunanin kwakwalwa da zai kai dan’adam ga yakini a duk inda ya yi amfani da shi. Shin an yi amfani da dokar ne a salon binciken hankali ko kuwa an yi amfani da ita ne a salon binciken gwaji, muhimmi dai shi ne wadannan ilimomi guda biyu suna  baje kolinsu wurin yin hukunci kan duk wata doka ta hankali da kowane ilimi yake bukatar ta don cimma hadafinsa.

Amma Falsafa ta baje hajar kasuwarta ne a fagen bahasin yakinin samuwa da samammu da siffofinsu da halayensu na bai-daya, sai aka kira ilimin Falsafa da falsafar farko domin a ware ta daga Falsafa ta biyu mai bincike kan abin da ya shafi gwaji. A nan ne zamu gane sirrin bahasin Falsafa gun ‘yan falsafar farko, da bahasin Falsafa gun ‘yan falsafar gwaji da muka fi sani da fagen Falsafa na biyu wacce yammancin duniya ya fi dogaro da ita.

Sannan kamar yadda muka yi nuni babu yadda za a iya samun dokokin da suke yin hukunci kan jigon bahasin Falsafa sai dai akasin haka ne kawai zai iya kasancewa. Ilimin Falsafa shi ne kawai ilimin da zai iya tabbatar da samuwar jigon da sauran ilimomi suke bahasi kansu, da tabbatar samuwa jiki da duk nau’o’insa ne ilimin Falsafa ya tabbatar a jigon da a kansa ne sauran ilimomin bahasin rayuwar samammu suke magana.

Kuma har ila yau da ilimin Falsafa ne zamu iya tantance samuwar gaskiya da abin da yake ba samamme ba, sai wannan lamarin ya kai ga sanya wannan bahasin daga cikin mafi girman hadafin Falsafa. Wannan bangaren bahasi ne muhimmi a Falsafa domin da shi ne zamu iya cimma hadafin asasi na tantance samuwa da sake-saken zuci da ba su da wata samuwa.

Hatta da bahasosin da suka shafi cewa akwai bazata a samuwa ko babu bazata duk bincike ne da suke rassa na irin wadannan bahasosin da zamu ga suna da matukar muhimmanci wurin shata wa dan’adam rayuwarsa, da tasiri mai zurfin gakse a akidarsa. Da wannan lamarin ne darajar wannan bahasin mai zurfi da tasirinsa a samuwa da rayuwar mutum take bayyana.

Haka nan kuma ta bayyana gare mu cewa ba zai yiwu a yi bahasin jigon Falsafa ba a fagen gwaji, misali babu hanyar bahasin mai samarwa da abin samarwa, ko samuwa wajiba da samuwa mai yiwuwa, ko samuwa maras jiki da samuwa mai jiki, a bahasin gwaji. Bahasin sabuba da abin da suke sabbabawa wasu bahasosi ne da gwaji zai iya cimmawa, kuma iyakacin fagen da zai iya kaiwa gare shi ke nan, don haka ba shi da wani mahalli a bahasin Falsafa sai dai a cikin taimakawa a mukaddimar bahasosi.

Da wani yaren muna iya cewa tun da bahasin Falsafa bahasi ne na ma’anoni na biyu na-Falsafa, su kuwa irin wadannan ma’anonin sun dogara ne kan bayani da warwarar hankali kan mas’alolinsu, don haka babu wata hanya ke nan da bahasin falsafar gwaji yake da ita don kasancewa jigo a cikin bahasin falsafar farko da muke magana kanta. Irin wadannan ma’anonin da muka bayar da misalinsu a fakarar da ta gabata, babu yadda za a iya gudanar da gwaji don tabbatar da su ko kore su.

Da wannan ne muke rufewa da cewa:

1- Bahasin Falsafa bahasi ne da ya dogara kan salon hankali  tsantsa wurin tabbatar da mas’alolinsa, da ya kunshi bayanin martabobin samammu, da tantance su.

2- Falsafa ce take daukar nauyin tabbatar da ginshikan bahasosin sauran ilimomi da kuma tabbatar da samuwar jigogin da suke bahasi kansu.

3- A bahasin Falsafa ne muke iya samun yakini kan hakikanin samuwar abu ko rashin samuwarsa, da kore duk wata shubuha a kan hakan har mu kai ga yakini.

4- Ma’anonin Falsafar Farko ba sa karbar gwaji, kuma babu yadda za a iya samun su ta hanyar gwaji, ke nan kuwa babu wata hanyar bincike kansu sai ta hanyar hankali.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *