Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s)

Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin Allah madaukaki a Gadir Khum a inda Annabi (s.a.w) yake nuna wa duniyar musulmi wasiyyinsa wanda yake shi ne makoma bayan wucewarsa yana mai cewa “Duk wanda nake jagoransa to Ali jagoransa ne”, yana mai karawa da cewa: “Ya Ubangiji ka jibanci lamarin wanda ya yi biyayya gareshi, ka tabar da wanda ya ki shi” . Lamari ne mai muhimmanci da yake nuna jagorancin al’umma bayan manzon Allah (s.a.w) ga Imam Ali (a.s).
Wasu sun yi sukan ma’anar kalmar “Wali, Maula” da suka zo a cikin wannan hadisin suna masu nuni da cewa don me Annabi (s.a.w) ya yi amfani da wannan kalma? . Su sani hannun Annabi a bude yake a kan yin amfani da kalmar “Wali, Maula”, domin shi ne ya fi kowa hikima da sanin kalmomin da suka dace don duk abin da ya kawo to daga mahaliccinsa ne. Don haka babu mai iya iyakance masa irin kalmar da zai yi amfani da ita alhalin yana shugaban masu hikima.
Wannan kalmar ta “maula, wali” a sarari tana nuna wajabcin biyayya ga Ali (a.s) bayan Annabin rahama hada da wajabcin soyayya kamar yadda masu nuna cewa ma’anar wannan kalma tana nuna soyayya ne ko taimako ne kawai. Kuma wannan yana nuna halifancin Ali (a.s) kai tsaye ko tantama babu, saboda abubuwa kamar haka:
Na daya: Shin Annabi (s.a.w) zai tara mutane 50 000 zuwa 120 000 bisa sabanin adadi da ya zo a tarihi, a wuri har ya sanya a dawo da wadanda suka yi gaba, a kuma tsaya har na baya su iso a wannan hanya mai zafi da suke cire rawunansu suna sanyawa kasan takalmansu, ga wahalar tafiya…! Domin kawai ya ce musu: Duk wanda nake abin sonsa ne to Ali (a.s) ma abin son sa ne. Ko kuma duk wanda nake abokinsa ko mai taimakonsa to Ali ma abokinsa ko mai taimakonsa ne!. Sai ya zama ke nan duk wani sahabin annabi ko abokinsa ko abin taimakonsa, ko mai sonsa ya zama ke nan sahabi ga Ali (a.s) ko abokinsa ko abin taimakonsa, ko mai sonsa!. Kuma sai ya zama ke nan wannan bayanin na Manzon rahama (s.a.w) ya kasance labari ne yake bayarwa kawai, ba umarni ba ne yake bayarwa! Wato wannan jumlar ta zama labari ba insha’i ba!. Shin wani mai hankali zai yi hakan balle Annabi (s.a.w) da ya fi kowa kamala! Ashe yana bukatar haka bayan ya riga ya gaya wa musulmi gaba daya da cewa su abokai ne masoya juna mataimaka juna . Kai har ma ya ce idan daya ya koka yana gabas ko yamma daya kuma yana gabas ko yamma bai taimaka masa to shi ba musulmi ba ne. Ashe duk bayan wannan sai Annabi ya tara mutane domin kawai ya gaya musu hakan game da Ali (a.s)!
Na biyu: Sannan kuma har Annabi (s.a.w) ya yi addu’a da Allah ya taimaki wanda ya taimaka masa, ya tabar da wanda ya ki taimaka masa, kuma ya kebance shi da wannan banda sauran musulmi. Idan kuwa haka ne, to wannan lamarin yana nufin so kawai zai kebanta da Ali a cikin dukkan sahabbai! Don haka sai ya kasance sauran sahabbai bai wajabta son su ba ke nan, don haka ba laifi idan mutum ya ki su!? Wannan lamarin kuwa su masu musun ma’anar wilayar Ali (a.s) a wannan ruwayar da nufin cewa shi ne jagoran al’umma bayan annbin rahama (s.a.w), ba zasu taba amincewa da haka ba, don haka ya zama dole ke nan su yarda da cewa: Allah ya nada imam Ali (a.s) a wannan ranar ne a matsayin halifan annabinsa kai tsaye bayan wafatinsa!.
Na uku: Bai’ar da aka yi masa (wacce hatta da halifofin farko da suka gabace shi a jagorantar al’umma bayan wafatin ma’aikin Allah (s.a.w) sun yi masa bai’a a wannan wuri) ba ta nuna so kawai, ta hada har da mika wuya ga jagorancinsa. Ga Umar dan Khaddabi bayan ya yi masa bai’a a nan take ya ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, hakika ka wayi gari jagorana kuma jagoran dukkan mumini da mumina .
Da ya kasance kamar yadda masu musunta ma’anar jagora suke yi ne na cewa kalmar “maula, wali” tana nufin kauna da soyayya da bai kebanta da shi ba, da bai’ar da suka yi masa a wannan sahara mai zafi tana nufin soyayya da kauna kawai, da wannan bai kebanta da shi ba, da kuma sai a yi wa kowane musulmi bai’a domin nuna soyayya da kauna gareshi.
Na hudu: Taya murnar da Abubakar da Umar da sauran sahabbai suka yi masa suka ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, ka zama shugabana kuma shugaban kowane musulmi. Ban sani ba ko mai musun jagorancin Imam Ali (a.s) yana nufin Umar bn Khattab da Abubakar da sauran sahabbai da suka yi wa Imam Ali (a.s) murnar zama jagoransu ba su fahimta ba ne. Ko kuma yana nufin cewa suna taya shi murnar cewa dole ne su so shi, alhalin soyayya abu ne wanda yake na tarayya tsakanin musulmi.
Idan ma mun ji cewa an yi masa bai’a domin nuna soyayya da kauna ne, to yaushe ne aka nuna masa kauna da soyayya yayin aka kewaye gidansa da barazanar konawa da wuta, aka cutar da matarsa har ta yi bari, sannan duniyar musulmi ta bi shi da zuriyarsa da kisa a tsawon tarihin al’ummar musulmi, har jikokin manzon Allah (s.a.w) suka rasa matsuguni suna masu gudu nahiyoyi daban-daban domin tsira da rayukansu.
Na biyar: Gabatarwar da manzon Allah (s.a.w) ya yi a farkon hadisin yayin da yake cewa da su: “Shin ba ni ne shugaban kowane mumini da mumina ba, a fili yake cewa ba komai ne karshen maganarsa yake nufi ba sai abin da farkonta yake nufi, dogaro da dokar amfani da karina yayin magana.
Na shida: Maganar da manzon rahama (s.a.w) ya rufe da ita na cewa “Allah ka shaida”! bayan ya gama hadubar, da kuma shaidawarsu. Yana nuna wannan lamari ne mai girma na sakon musulunci da makomarsa, kuma ya kebanci imam Ali (a.s) shi kadai ban da sauran musulmi!.
Na bakwai: Akwai ayoyin Kur’ani da hadisai masu yawa da suke karfafar ma’anar jagora. Kamar ayar “Kawai shugabanku …” , da bayyane take nufin jagora saboda karinar ayar da ta gabace ta, da wacce ta biyo baya kamar yadda ya zo a tafsirai. Don haka Kur’ani mai daraja littafin Allah madaukaki yana tare da ma’anar jagorancin Ali (a.s) ga al’ummar Annabi (s.a.w) bayansa.
Sai dai wannan al’ummar yayin da ta ga ta kauce wa wannan wasiyyar ta manzon Allah (s.a.w) sai ta yi kokarin ganin cewa ta gyara abin da tawiloli da ba su da wani amfani sai neman danne gaskiya, ko neman bayar da uzuri ga wadanda suka saba wa wannan wasiyya mai kima ta Annabin karshe.
Na Takwas: Daga hannun imam Ali (a.s) da Manzo (s.a.w) ya yi a wannan wuri da kuma nuna shi ga al’ummarsa, ba ya nuna komai sai ma’anar jagoranci da shugabancin Ali (a.s) ga al’ummarsa bayan wafatinsa, hada da cewa bayan wannan lamari da ya wakana a Gadir manzon Allah (s.a.w) bai yi wata uku a duniya ba ya rasu. Yanzu wannan lamarin bai iya sanya gane gaskiyar jagorancin imam Ali (a.s) wanda Allah madaukaki ya nada, manzon rahama (s.a.w) ya isar wa al’umma ba?!
Hada da cewa yana mai karfafawa da fadinsa: Kun sheda, suka ce: Mun sheda haka ne!. Sannan ya daga hannunsa sama yana cewa ya Ubangiji! Kana gani dai na isar! A yanzu duk da wannan bai isa mai hankali da basira ya gane gaskiyar lamarin jagorancin da Allah ya nada kan al’umma ba!? Yanzu da wadannan bayanai dalla-dalla, baro-baro har akwai abin da zai buya!?
Wasu sun yi da’awar cewa wannan kawai wata ishara ce Allah ya yi mana da wasicin Ali (a.s) ta hannun annabisa (s.a.w), amma bai yi baro-baro da hakan ba!. Sai mu ce da su: Idan mun kaddara cewa ishara ce, don me ya sa ba su yi amfani da wannan isharar ba!, Ashe ishara ba ta wadatar da yin baro-baro ba ga mai hankali!.
Na Tara: Saukar azaba kan Nu’uman nan take yayin da ya ki yarda da shugabancin Ali (a.s), da musun da ya yi wa Annabi (s.a.w) da cewa yaya zai ce su bi dan amminsa bayansa! Kamar yadda ya zo a tafsirin ayoyin farko na surar Ma’arij . Da ya kasance ba tana nufin jagorancin Ali kan wannan al’umma ba ne, da ba a samu wani tayar da hankali da jijiyar wuyan masu hassada da masu kiyayya da Ali kan wannan lamarin ba!.
Na Goma: Idan muka yi kokwanto kan cewa wannan kalma tana nufin masoyi ko shugaba, to sai mu yi hukunci da dukan ma’anoni tun da suna yiwuwa a hada su, domin babu karo tsakaninsu. Sai ya hada da wajabcin sonsa da mika jagoranci gareshi, da taimaka masa, domin ka’idar ilimin Usul ta komawa ga ma’ana gamammiyya “amm” idan an kasa tantance kebantacciyar ma’ana “khas”. Don haka wannan ya tabbatar da ma’anar shugabancinsa da jagorancinsa kan duk wani mutum bayan wucewar Manzon Allah (s.a.w).
Ilimomin Tunanin mutum kamar Mantik da Falsafa sun karfafi wannan ka’idar yayin da suke cewa: Ma’ana gamammiya “kulli” fuska ce ta ma’ana kebantacciya “juz’i” wato ana iya sanin “juz’i” ta hannun “kulli”, amma ba za a iya sanin “kulli” ta hannun “juz’i” ba, domin har abada ba yadda za a yi “juz’i” ya kasance fuskar “kulli”! Don haka wilaya a nan ta hada ma’anar farko ta jagoranci wacce ita ce ta fi bayyana, da kuma ma’anar soyayya da taimako gaba daya.
Misali hakan; Da zamu yi kokwanto kan cewa wannan abin da muke gani biri ne ko alade zai yi wuya mu iya hukunci da dayansu, domin idan muka ce alade ne ko biri zai kasance mun rinjayar da wani daga ciki babu hujja (wannan idan mun kaddara sun yi kunnen doki a ma’ana gamammiya ke nan), amma idan muka ce dabba ne to wannan yana nufin mun samu amsa daidai, domin idan ya kasance dayansu ne to kowannensu ai dabba ne.
Na Sha daya: Da zamu samu kalmar da take da ma’anoni daban-daban, sai aka yi amfani da ita ba tare da wata karina ba, to a nan sai a dora ta kan ma’anar da ta fi bayyana a fili a matsayin shi ne abin nufi. Kamar da wani mutum zai ce: Kawo mini kwano. To kwano tana da ma’anoni daban-daban; ana amfani da ita a kwanon cin abinci, da kwanon gini, da hular kwano, da sauransu. A nan sai mu ce yana nufin kwanon cin abinci, domin shi ne ma’anarsa da ta fi bayyana a fili gun bahaushe matukar bai yi amfani da wata karina ba. Wannan lamarin haka nan yake game da ma’anar “maula, wali” a larabci da ta fi nuni da ma’anar jagora, kafin ta yi nuni da ma’anar masoyi, ko mataimaki, don haka sai a dora ta kan ma’anar jagora, sai ya zama ke nan duk wanda yake musulmi dole ya riki Ali (a.s) jagoransa bayan manzon Allah (s.a.w)!.
Kalmar “wali, maula” kalma ce da aka yi wa tawili kamar yadda aka yi tawili ga wasu kalmomin da suka zo daga Annabi (s.a.w) don son rai da kauce wa gaskiya. Sau da yawa wasu sukan yi kokarin tawilin wasu abubuwa ne domin gyara barnar da aka yi wa addini wanda wannan cin amanar Allah da manzonsa ne. sannan wannan lamarin ba sabon abu ba ne, domin a zamanin Annabi (s.a.w) an yi wa maganarsa tawili, an yi masa karya inda aka kasa yin tawili, har ma lamarin ya wuce yi masa tawili ko karya, ya kai ga rashin yarda da kin biyayya ga umarninsa a wasu lokuta!.
Idan mun lura sosai zamu ga cewa irin wannan ne ya samu al’ummar da ta gabata har ta samu kanta cikin kauce wa koyarwar annabawa da manzanni (a.s), sai aka bi son rai cikin tawilin abin da suka zo da shi. Amma a ko da yaushe al’ummar da ta tsaya kyam kan biyayyar wasiyyan wadannan annabawa (a.s) su ne suke wanzuwa kan shiriyarsu.
Wannan tawilin ba a gushe ba har yanzu kuma har karshen wannan duniya ana ci gaba da shi, idan mun duba ruwayar da ta yi wasiyya da riko da Littafin Allah da Alayen Annabi (s.a.w) bayansa zamu ga yadda take mutawatira, amma sai wasu jama’ar musulmi suka yi kokarin ganin sun kishiyanci wannan da wata ruwayar mutum daya mai ambaton cewa wasiyyar Annabi (s.a.w) tana cewa Littafin Allah da Sunnar Annabi ne.
Don haka ne zamu ga wasu jama’a ne kadan a ko da yaushe suke tsayawa kan wasiyyar annabin da aka aiko musu, kuma wannan al’ummar ba ta fita daga cikin irin lamarin halin da suka fada ba. Annabi (s.a.w) ya bar mana Littafin Allah da Ahlul-baiti (a.s). Kuma bin su shi ne dawwama kan tafarkin Annabi yardajje gun Allah (s.w.t).
Annabi (s.a.w) shi ne shugaban masu hikima da hankali, sannan kuma ya san babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani wahayi bayan nasa, don haka ya dauki matakai da zasu hana bacewar al’umma da karkacewarta. Idan kuwa al’umma ta ki shiryarwarsa, to ita ta jiyo wa kanta. Don haka wahalhalu da rarraba duk ya faru ne tun farko saboda barin wasiyyoyinsa.
Kuma abin da ya faru ga yahudawa da Kirista shi ne ainihin abin da ya faru ga musulmi kwabo da kwabo, sai dai mu musulmi muna da ludufin Allah (s.w.t) na cewar muna iya bugun kirji mu ce: Duk wanda yake son ya ga sakon manzon Allah (s.a.w) ba tare da wani jurwaye ba to ga shi nan a tare da alayensa (a.s).

Hafiz Muhammad Sa’id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

65-Wasikar Imam Ali ga Malik Ashtar 15

  Wasikar Imam Ali (a.s) ga Malik Ashtar kwamandan yakinsa da ya aika shi zuwa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *