Kyawawa da Munanan Halaye

WAJIBAI DA SUKA HAU KAN MUTUM A FIKIHUN MUSULUNCI

Ubangiji yana cewa: “Allah yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma bai wa ga ma’abocin kusanci” . Sai ya lizimta wa mutum musulmi sanin wajibai da aiki da su kuma zamu kawo wasu daga ciki.
Akwai abubuwan da aka wajabta a fikihu a kan kowane mutum, yana da kyau ya zama teburi da mutum yake auna kansa da su domin ya tabbatar da ya kula da su, wanda ya ga bai kula da shi ba sai ya kula da shi, wanda ya ga ya yi sakaci a cikinsa sai ya kara tashi tsaye don kiyaye shi. Wadannan abubuwan sun hada da:

1. Ba wa mace sadakinta ko ladanta
2. Ba wa mai shayarwa ladanta
3. Ba wa mai girbi hakkinsa
4. Ba wa ma’abocin kusanci hakkinsa
5. Bayar da zakka
6. Bayar da dukiyar maraya
7. Tsoro da takatsantsan ga abin da Allah ya hana
8. Rikon ado gun masallaci
9. Rikon abin da Manzo da Ahlul Baiti (A.S) suka zo da shi
10. Bayar da amana
11. Bayar da sheda
12. Bayar da hakkin Allah da na mutane
13. Neman izinin shiga gidan mutane
14. Umarni da kyakkyawa
15. Aikata kyakkyawa
16. Imani da Allah da ranar lahira
17. Kaskantar da kai ga Allah da mutane
18. Barranta daga makiyan Allah da waliyyansa
19. Kin makiya Allah
20. Neman tsani zuwa ga Allah
21. Neman yardar Allah
22. Kin ma’abota bidi’a
23. Kwana gun matarsa ko mijinta
24. Biyayya ga Annabi da alayensa
25. Bin limami a salla
26. Kawar da fasadi
27. Tuba
28. Tabbata kan gaskiya
29. Tabbata a jihadi
30. Nisantar mummnan zato
31. Nisantar bauta ga wanin Allah
32. Nisantar karya da shedar zur da muzik (kida)
33. Karkata zuwa ga sulhu
34. Amsa wa Allah da manzonsa
35. Son Allah da waliyyansa
36. Hijabin mace ga namiji bare
37. Yin aikin Hajji
38. Zantawa da ni’imar Allah
39. Haramta abin da Allah da manzonsa suka haramta
40. Kyautata zato ga Allah
41. Renon ‘ya’ya
42. Kiyaye farji
43. Kiyaye salla da ibadu da alkawura da amana
44. Hukunci da abin da Allah ya saukar
45. Neman yafewar wanda aka zalunta
46. Gaisuwa
47. Tsoron Allah da rusuna masa
48. Kaskan da kai ga muminai
49. Bayar da Humusi
50. Tsoron Allah
51. Addu’a
52. Kira zuwa ga Allah
53. Kariya ga addini da rayuka
54. Kare mummuna
55. Ambaton Allah a kowane hali
56. Tarbiyyar yara
57. Amsa sallama da rubutu
58. Shiryar da mutane zuwa ga gaskiya
59. Yarda da hukuncin Allah
60. Ziyarar Annabi da imamai
61. Mika wuya da tsarkake wa ga Allah
62. Rige zuwa ga gafarar Allah
63. Sauraron Kur’ani mai hikima
64. Tafiya a bayan kasa domin daukar darasi
65. Godiya ga Allah da iyaye
66. Yin Hakuri
67. Soyayyar iyaye da makusanta
68. Gaskiyar magana
69. Gyara tsakanin mutane
70. Azumin wata Ramadan
71. Rama abin da ya jawo lalacewarsa da batansa
72. Ciyar da mai jin yunwa
73. Neman arziki
74. Neman ilimi
75. Biyayya ga Allah da manzonsa da majibinta lamurra
76. Bayyana gaskiya
77. Bayyana ki ga masu sabo
78. Bautar Allah
79. Daukar darasi daga darussan rayuwar wasu
80. Yin Adalci
81. Zama da mata da kyakkyawa
82. Sanin ilimin wajibi na asasin addini da rassansa da kyawawan halaye da ladubba
83. Taimakekeniya
84. Runtse gani daga haram
85. Neman gafara
86. Yin Kishi
87. Matsawa wasu a mazauni
88. Ilimin addini
89. Tunawa da ni’imar Allah
90. Hukunci da gaskiya
91. Tsayar da addini da aiki da shi
92. Fadin kyakkyawa
93. Daidaita al’amura
94. Neman halal
95. Kasancewa tare da masu gaskiya
96. Nisantar wanda Allah ya la’anta
97. Hana fajirai shiga masallatai
98. Nadama kan zunubai
99. Nasiha ga mumini da taimaka masa
100. Ciyarwa a tafarkin Allah
101. Yin Aure
102. Hana mummuna
103. Hanuwa daga abin da Allah da manzonsa suka hana
104. Komawa zuwa ga Allah
105. Niyyar gaskiya da kyakkyawa
106. Yin Tahajjudi
107. Hijira saboda Allah
108. Rushe bata
109. Son ma’abota kusanci
110. Tsentseni a haram
111. Awo da ma’aunin adalci
112. Cika alkawari
113. Kare rai da iyali daga wutar lahira
114. Dogaro da Allah
115. Yakini da Allah da ranar lahira

Dabi’u Mafifita Da Kyawawan Halaye
Akwai dabi’u mafifita abin yabo da musulunci ya yi maraba da su kuma ya yi umarni a siffantu da su, da ya kamata mutum musulmi ya siffantu da su kuma suna da yawa, amma zamu kawo abin da ya samu daga cikinsu:
1. Nutsuwa da alkawarin Allah
2. Yin sannu-sannu a al’amura
3. Kaskantar da kai gun Allah
4. Adalci da fadin gaskiya game da mutane
5. Wadatuwa daga mutane
6. Fifita wasu a kan kansa
7. Ciyarwa a tafarkin Allah
8. Taimakon mutane
9. Saba wa kai da aikata alheri
10. Umarni da kyakkawa
11. Hani ga mummuna
12. Gyara tsakanin mutane
13. Ikhlasi a ayyuka
14. Nutsuwa da Allah
15. Biyayya ga iyaye
16. Kaskan da kai
17. Ziyartar juna
18. Jituwa da juna
19. Tuba daga aikata haram
20. Mika wuya ga umarnin Allah a komai
21. Dogaro ga Allah
22. Tabbata kan al’amura kyawawa
23. Yin Hakuri
24. Aikata Kyawawan halaye
25. Kiyaye hakkin makota
26. Son Allah da wanda Allah ya yi umarni a so
27. Soyayya saboda Allah
28. Kiyayya saboda Allah
29. Jin Tsoron Allah
30. Kaunar Allah
31. Jin Tsoron aikata zunubai
32. Rashin dogaro da ayyuka
33. Cudanya da mu’amala da mutane
34. Magana da kawukanmu
35. Cudanya da iyalinmu da ‘ya’yanmu
36. Yarda da rabon Allah
37. Yin Zuhudu
38. Yin Baiwa da kyauta
39. Sitirta sirrin mutane
40. Gyara aibobin kai
41. Dadada magana
42. Godiya ga mai ni’ima wanda ya yi maka alheri
43. Gyara ga mutane ta hanyar hikima da wa’azi
44. Sakin fuska
45. Yawaita sadaka da taimakon raunanan mutane
46. Sadar da zumunci
47. Yada sallama
48. Bin halaye da raunana da marasa lafiya suke ciki
49. Yin Tsafta
50. Suturta aibobin mutane
51. Daidaituwar zahiri da badini a komai
52. Yin Gaskiya da nisantar karya koda a raha
53. Yin Hakuri
54. Karbar bakuncin muminai
55. Amsa kiran bakuntar muminai
56. Aika wa da kyauta wuraren da suke na alheri da kuma karbarsa
57. Rangwame ga mutane
58. Kame kai
59. Adalci a komai
60. Girmama ma’abota addini
61. Nisantar kaskantattun dabi’u
62. Yin Kishi
63. Son talakawa
64. Mujahada da rai
65. Bayar da rance
66. Biyan bukatun muminai
67. Kame cutar da su
68. Kiyaye sirri da rashin yada shi
69. Ambaton mutane da alheri
70. Gaggauta alheri
71. Yi wa kai hisabi
72. Nasihar muminai yana mai neman shawara ne ko kuwa
73. Yin Niyyar alheri
74. Tsarkake kai da kawar mata munanan halaye
75. Yin Takawa
76. Yin Tsentseni
77. Nisantar shubuha
78. Juriya kan barin sabo
79. Juriya kan bin Allah
80. Ambaton mutuwa
81. Wadatar zuci
82. Jin Kunya
83. Sakin fuska

AMMA A MATAKIN MASANA ALLAH AKWAI WASU LAMURA DA SUKA DUKUFA A KANSU SUNA MASU NEMAN GANIN SUN CIMMA SU TA HANYAR TSARKAKE RAI DA SUKA HADA DA:

1. Farkawa
2. Yin Tuba
3. Yi wa kai Hisabi
4. Komawa ga Allah
5. Yin Tunani
6. Tunatuwa da Wa’aztuwa
7. Kamewa
8. Gudu zuwa ga Allah
9. Motsawa
10. Sauraro
11. Bakin cikin Takaitawa
12. Tsoron Allah
13. Tsantseni
14. Yankewa zuwa ga Allah
15. Kauna
16. Kwadayi
17. Kiyayewa
18. Kulawa
19. Tsarkakewa
20. Dogaro da Allah
21. Aminci da Nutsuwa da Allah
22. Juriya
23. Hakuri
24. Yarda
25. Godiya
26. Kunya
27. Zabin wasu a kan kanmu
28. Kyawun hali
29. Kaskan da kai
30. Shimfida fuska
31. Kyauwatatawa
32. Neman ilimi
33. Yin Hikima da sauraronta
34. Yin Basira
35. Girmamawa
36. Himma
37. Nutsuwa
38. Nufi
39. Azama
40. Ladafi
41. Yakini
42. Nutsuwa
43. Ambato
44. Bukatuwa zuwa ga Allah
45. Kaunar Allah da ma’abotansa
46. Kishi
47. Shauki
48. Kishirya da Yunwa (musamman na azumi)
49. Nutewa a kadaita Allah
50. Tsarkake niyya ga Allah

YA DACE MUTUM YA YI WA KANSA TSARIN DA ZAI RIKA KALLON MUNANAN LAIFUKA DOMIN YA AUNA KANSA YA GA INA YA ISA KUMA A WANE MATAKI YAKE DOMIN YIN KOKARIN NISANTARSU DON KAI WA GA KAMALAR DAN’ADAMTAKA

Abubuwan Da Aka Haramta
Allah yana cewa: “Ka ce ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta muku” . Kamar yadda ya lizimci mutum musulmi ya nemi sanin wajibai haka nan ya lizimta masa neman sanin haram da kuma nisantar ta, kuma mu a nan zamu kawo galibin abubuwan da aka haramta musamman wadanda a na iya cin karo da su kamar haka:
1. Taimakawa ga yin sabo
2. Taimakon azzalumi
3. Nutsuwa da fushin Allah
4. Musun mu’ujiza
5. Musun ranar sakamako da tayar da jikin mutane ko wani daga asasin addini ko na mazhaba
6. Musun larurin addini
7. Kawar da kai daga ambaton Allah
8. Izgili ga muminai
9. Yin Barna
10. Dagewa kan kananan sabo
11. Sanya zoben zinare ga namiji
12. Jawo mani: kamar da hannunsa ko da na wani, amma idan ta hannun matarsa ne to ba komai
13. Cutar da muminai
14. Kauce wa hukuncin shari’a
15. Amfani da kwanon zinare da azurfa koda don ado ne
16. Wulakanta musulmi
17. Yada sirrin wanda bai yarda a yada ba
18. Yada sirrin juna tsakanin miji da mata
19. Rashin biyayyar mace ga mijinta cikin abin da yake wajibi ne ta bi shi
20. Rashin biyyar ‘ya’ya ga iyayensu
21. Wasa da kayan caca tare da sanya kudi
22. Bayyana sabo
23. Yada alfahasha
24. Ci a Ramadan ko ranar azumin wajibi ba tare da wani uzuri na shari’a ba
25. Boye kaya
26. Rashin nisantar bawali da najasosi
27. Rashin yarda da Allah a cikin kaddararsa
28. Umarni da mummuna
29. Cutar da makwabta
30. Karbar lada a kan wajibi ayyananne
31. Karkata zuwa ga azzalumai
32. Jefa kai cikin halaka
33. Jingina yaro ga wanda ba babansa ba
34. Fitar mace ba tare da izinin mijinta ba
35. Sumbuntar namiji ko mace ga bare
36. Sumbuntar mutum waninsa don sha’awa sai dai miji da matarsa kawai ko baiwarsa
37. Bidi’a cikin addini
38. Mutum ya auri Muharramarsa
39. Mummunan zato da gini a kansa
40. Yin Kage
41. Bayan gida tare da ba wa alkibla baya ko gaba
42. Girman kai ga barin bautar Allah
43. Adon namiji da zinare
44. Duban taurari
45. Girman kai
46. Barin salla wajiba
47. Barin kowane irin wajibi
48. Jinkirta hajji daga shekarar da ya samu iko
49. Karyata wani abu na Kur’ani ko hukuncin shari’a
50. Yin Barna
51. Jinkirta salla har lokacinta ya fita
52. Kai hukunci gun azzalumi ba larura
53. Halartar wajen shaye-shaye
54. Mace ta yi ado ga namiji bare
55. Hore rohani ko aljani da sauransu
56. Sanya bacci na maganadisu
57. Boye aibin kaya da algus
58. Jinkirta rama Ramadan har wani Ramadan din
59. Barin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
60. Barin ladabtar da yara da zai kai ga fasadi
61. Haramta halal
62. Halatta haram
63. Leken aibobin mutane
64. Tsoratar da mumini
65. Barin takiyya wajen da yake dole
66. Kamantuwa da kafirai a shiga da adon kai da sauransu
67. Ji wa wani ciwo ko dukansa ko zaginsa ko yanke masa wata gaba
68. Rashin amsa sallama
69. Hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba
70. Tsare hakkin Allah
71. Tsare hakkokin mutane
72. Tsare wani babu wani hakki
73. Sanya tufafin alhariri ga namiji babu wani uzuri na shari’a
74. Hassada da kuma aiki da ita
75. Tozarta hakkin mutane
76. Kiyaye littattafan bata da jaridu ko mujallu na bata da sayar da su da sayansu da koyar da su da koyonsu da yada su
77. Cin dukiyar maraya
78. Shan abu mai sanya maye
79. Cin mushe
80. Cin naman alade
81. Cin naman dabbar da aka haramta
82. Cin naman dabbar da ba a ambaci sunan Allah ba wajen yanka ta ko ta rasa wani sharadi na yanka
83. Cin tabo ko sauran abubuwan da aka haramta
84. Yin Ha’inci
85. Kayan kide-kide da muzik, kamar sayar da su da sayen su da kuma ajiye su da amfani da su bisa hanyar haramci
86. Yin Yaudara
87. Neman auren mace mai miji ko kuma mai idda
88. Cin maniyyin tumaki
89. Cin sauran abubuwan da aka haramta a jikin dabba
90. Sayar da karen kwararo ko alade da sayansu
91. Yakar shugaba na shari’a adali
92. Cin najasa ko abu mai najasa da shansu
93. Karya ga Allah da manzonsa da Imamai (A.S)
94. Buga ganga ko garaya da molo da ihu
95. Yin Sata
96. Yada barna
97. Kashe gaskiya
98. Daudanci da hada zina tsakanin mutum biyu
99. Yin Karya
100. Shiga kungiyoyin bata kamar na kominis
101. Shiga addinan bata kamar na sufancin babiyya
102. Kiyayya da mumini
103. Son makiya addini
104. Zagi musamman ga Allah da Annabi da Imami da addini da Kur’ani da mazhaba da sauran abubuwa masu tsarki
105. Taba littafin Kur’ani babu tsarki
106. Mai baki biyu; ya yabi mutum, idan ba ya nan kuma ya zage shi
107. Karbar rashawa da cin hanci domin boye gaskiya da bayyanar da karya
108. Karbar rashawa da bayar da ita cikin al’amuran hukunci sai da larura
109. Karbar riba da bayar da ita da rubuta sheda a kanta da zama tsakatsaki a kai
110. Zama kasar da mutum ba zai iya kare addininsa ba ko gusar da alamomin musulunci
111. Zuwa kasar da zata cutar da addinin mutum
112. Yin Fashi
113. Tsige gemu da abin da yake mai kaifi daga tushensa
114. Aske gemun wani da abin da yake mai kaifi daga tushensa
115. Yin Rawa
116. Shiga cikin cacar ful
117. Tafiya makarantun da zai kai ga fasadi
118. Tafiya bandaki da wurin wanka na iyo da makarantu da wuraren da ake cakuda maza da mata
119. Raddi ga Allah da manzonsa da imamai da marja’ai da suke kan tafarkinsu cikin hukuncin shari’a
120. Yarda da sabo
121. Jifan wani da zina
122. Yin Annamimanci
123. Sauraron annamimanci
124. Zuwa sinima ta barna
125. Kokarin rusa masallatai
126. Taimako ga azzalumai koda dan aike ne
127. Amfani da kayan kida da caca da kuros da sauransu
128. Waka da fadin karya a ciki
129. Tare Titi da hanyar mutane
130. Aibata mumini da wulakanta shi da zarginsa
131. Karanta girman zunubi da zai kai ga jinkirta tuba
132. Fitar mata ba tsari da kuma cire hijabi (Lullubi)
133. Shirka da Allah mai girma
134. Yada alfasha
135. Saba wa da karya
136. Warware alkawri
137. Yin Shedar zur
138. Sharadi da sanya kudi na tsere sai dai abin da aka fada a littafin fikihu a babin tsere da harbi
139. Yin Rufa ido
140. 40. Yin Munafunci
141. Ba wa azzalumi da ‘yan bidi’a uzuri da kuma kaunarsu
142. Tozarta wanda ake ciyarwa
143. Wasa da tattabaru da tsuntsaye da sauransu na daga abubuwan da sukan kai ga haram
144. Zalunci da ta’addanci
145. Yin Zihari
146. Saba wa iyaye
147. Aikin tsafi da kuma abin da zai raba miji da mata ko kuma abin da yake sanya son wani ba tare da sonsa ba
148. Zubar da jinin mutane
149. Cin dukiyoyin mutane da barna
150. Jiji da kai a ibada
151. Yin Algus
152. Wakar da ake ambaton haram da sauraronta
153. Canja wasiyya
154. Fushi da yakan kai ga haramun
155. Giba: Yin rada da sauraronta
156. Fasadi a bayan kasa
157. Yin Fitina
158. Fasikanci da fajirci
159. Sayar da littafi madaukaki
160. Sayar da makami ga kafirin yaki
161. Kiyafa: danganta mutane da iyayensu ta hanyar kallon kafafunsu ko jikinsu da canke
162. Caca da kayan shadaranji da sanya kudi
163. Yanke salla wajiba
164. Rantsuwa bisa karya
165. Tone kabari
166. Yanke zumunci
167. Jingina ‘ya’ya ga Allah
168. Yin Bokanci
169. Bayar da fatawa ba da ilimi ba
170. Fada da tafarkin Allah
171. Kisa ba da hakki ba
172. Auren mace da aka haramta da nasaba ko shayarwa ko surukuta
173. Aurar namiji da aka haramta aurarsa
174. Kin zuwa jihadi
175. Gudu daga filin daga
176. Yin Kafirci
177. Kasuwanci da abin da aka haramta sayarwa
178. Tauye mudu da awo
179. Boye sheda
180. Boye gaskiya
181. Wake da siffanta mace mai kamewa ko yaro
182. Zambon mumini a waka
183. Bude al’aura ga wanda ya haramta ya gani
184. Yin Luwadi
185. Wasannin banza na holewa
186. Taba jikin ajnabi ko ajnabiyya (mace ko namiji bare)
187. Taba mace ko namiji da sha’awa ba ta hanyar halal ba
188. Amfani da kayan maye kamar sha, da saye, da sayarwa, da dasa su ko shuka su, da aikinsu, da cin kudinsu, da kai wa wani, da kuma hayar kanti ko abin hawa ko wani abu daban don sayarwa, da kuma sauran amfani kamar yin magani da su idan ba da larura ba
189. Saba wa bakance
190. Aikata abubuwan da aka haramta wa mai harama da aikin hajji
191. Zuwa wajen bokaye da ‘yan bori da ‘yan camfi da masu halarto da rauhanai da aljanu da sauransu
192. Mata su shafi juna da sha’awa
193. Maza su shafi juna da sha’awa
194. Hana zakka ko humusi ko sauran hakkoki na wajibi
195. Jinkirta hakkoki
196. Yin Hannu da ajnabiyya ba kyalle tsakani
197. Jayayya da Allah da manzonsa da Imami bisa shisshigi
198. Saba wa Allah da manzonsa da imamai (A.S)
199. Keta umarnin Annabi (S.A.W)
200. Shisshigi da wuce gona da iri musamman ga Allah
201. Leken gidajen makwabta
202. Zama a kan teburin da ake shan giya
203. Hana aikata kyakkyawa
204. Shiga ayyukan azzalumai da taimaka wa zaluncinsu
205. Keta alfarmar Ka’aba da wurare masu tsarki
206. Yanke kauna daga rahamar Allah
207. Ruku’u da sujada ga wanin Allah
208. Rantsuwa da barranta daga Allah da manzonsa ko Imami ko addinin musulunci
209. Kai wa zuwa ga mulki ba ta hanyar shari’a ba
210. Azabtar da mutane don su fadi wani abu da ake bincike

Muna iya ganin wasu mun maimata su saboda muhimmancinsu da kuma hani gare su da aka yi hani mai tsanini ko azaba mai tsanani a kan yin su.
Sannan kuma wasu da muka fada kafirci ne yin su wasu kuma shirka ne, wasu kuma manyan zunubai ne, wasu kuma akwai kaffara a kansu wasu kuwa akwai haddi ga yin su kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a litattafai.

Munanan Halaye Da Kuma Abin Kinsu
Akwai munanan halaye dadabi’u da suke munana kuma ya kamata ga duk wani musulmi ya kaurace musu kuma suna da yawa, malaman ilimin kyawawan halaye sun ambace su a littattafansu, sai dai mu a nan zamu kawo wasu daga ciki, duk da wasu ma an haramta su a shari’ance, ga wasu daga ciki kamar haka:
1. Daukar fansa
2. Yin Alfahari
3. Cutarwa koda ba da haramun ba kamar ya gina gidansa ta yadda zai kare wa makwabcinsa rana ko iska
4. Wulakanci ko da bai kai haddin haramci ba
5. Wulakanta mutane
6. Tsoratar da mutane koda bai kai haddin haramci ba
7. Yada abin da ake son boyewa
8. Karya a cikin raha
9. Yin Izgili
10. Wuce iyaka kamar ya zauna tarabbu’i a waje mai tsukuku
11. Wulakanci cikin alheri
12. Kage cikin raha; kamar ya ce wane yana da ci
13. Magana da abin da babu ruwan mutum
14. Dogaro kan mutane
15. Aikin lagawu (wasannin banza)
16. Boye abubuwan da aka boye da ba su shafi mutum ba
17. Raki gun musifa
18. Jur’ar yin munana
19. Bakin ciki a kan abin da ya kubuce na duniya
20. Rashin kula da al’amuran lahira
21. Son yabo da kurantawa
22. Son shugabanci da girma
23. Son dukiya
24. Son duniya
25. Hassada matukar ba ta kai haddin haramci ba
26. Yin Kwadayi
27. Dora nauyi kan wani
28. Hikidi da mugun kuduri da mugun kulli
29. Tsoron mutane
30. Kutsawa cikin munanan halaye
31. Neman zabar rayuwar da ya so ta duniya, kamar kayyaduwa da nau’in tufafi da sauransu
32. Saba alkawari
33. Riya koda a wanin ibada ne
34. Munana zato ga Allah
35. Munana zato ga mutane
36. Yin Mummunar dabi’a
37. Halartar Mummunan waje
38. Kokarin aikata mummuna da ba haramun ba ne
39. Rashin yarda da rabo
40. Zama da kaskantattun mutane
41. Kukan sha’anin rayuwa
42. Yin Rowa
43. Shige gona da iri a rayuwar duniya
44. Shagube koda ba na haramun ba
45. Kaskanta mutane
46. Kaskantar da kai
47. Kaskantacciyar Himma
48. Dukan kai
49. Kwadayi
50. Yawan bacci
51. Dogon buri
52. Rashin kishi
53. Kishi a inda bai dace ba
54. Yin Gaugawa
55. Shisshigi daidai gwargwadon da bai kai haram ba
56. Kyautata zato ga kansa
57. Kabilanci da bangaranci
58. Rashin girmama babba
59. Rashin tausaya wa karami
60. Rashin dogara da Allah
61. Fushi babu wani dalili na shari’a
62. Yawan wadatar da ta kasance dalilin daga kai
63. Yin Dimuwa
64. Yin Gafala
65. Fankama da abin mutane
66. Mummunar magana koda ba haramun ba ce
67. Tayar da fitina
68. Kekasar zuciya
69. Raba kan mutane da rashin jituwa
70. Yin Girman kai
71. Boye gaskiya koda kuwa boyeta bai kai wajibi ba, koda kuwa ta hanyar shiru ne
72. Ganin alherin kansa da yawa
73. Karanta alherin wani
74. Yawaita sharrin wani
75. Karanta sharrin kansa
76. Butulce wa ni’ima
77. Rashin godiya
78. Yawan raha
79. Rashin daidaituwa tsakanin zahiri da badini koda kuwa a kan al’amuran duniya ne
80. Rashin kunya
81. Nisantar muminai
82. Zaman banza
83. Yawan dariya
84. Waswasi a al’amuran duniya
85. Yawan shagaltuwa da rayuwa
86. Kazanta da rashin lizimtar tsafta
87. Rashin adalci
88. Shisshigi a al’amuran duniya
89. Sakaci a cikin lamurra
90. Zama da masu sabo
91. Yunkune da bata fuska
92. Rashin kulawa da mustahabbai
93. Lizimtar makaruhai
94. Rashin kulawa da abin da ya ce da abin da aka ce game da shi
95. Rashin bayar da muhimmanci ga hukuncin shari’a

 

 
(1) telegram.me/Haidar_Center_Academy

(2) telegram.me/Haidar_Center_Enlightenment

(3) telegram.me/Haidar_Center_Books

(4) telegram.me/Haidar_Center_Tarbiyya

www.haidarcenter.com
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

Check Also

45-Halayen Imam Mahdi

  Kowane imami shi ne mafi kamalar mutane a zamaninsa, Imam Mahdi (a.s) shi ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *