HIKIMA

Salon Hankali da Gwaji

Mun sani cewa Kiyasi ba ya bayar da yakini sai idan ya kasance na Mantik (Logic) kuma mukaddimarsa ta kasance mai kai wa ga yakini. Mukaddima dole ne ta kasance ita da kanta tana da yankini a kunshe da ita ko kuma ta kasance tana kai wa ga mukaddima mai …

Read More »

c. Kiyasi (Syllogism)

Mun gama magana kan Kamantawa (Analogy) da Kididdiga (Induction), sai kuma magana kan Kiyasi ((Syllogism)) kamar yadda Mantik (Logic) yake kiran sa. A Kiyasi ana sanin doka ne ta wasu daidaiku sannan sai a dabbaka wannan dokar kansu, kamar dokar da take cewa; “Duk wani mai motsi jiki ne”, sai …

Read More »

b- Kididdiga (Induction)

Mun yi nuni da wasu bayanai kan Kamantawa (analogy), mun ga cewa ba hujja ba ce a hankalce ko a shar’ance saboda munin natijar da yake haifarwa. Idan muka bi Kamantawa zai dagula rayuwa ya yamutsa tsarin al’umma hatta da akida sai ta rushe. Amma Uslubi ko Salon Kididdiga (Induction) …

Read More »

a- Kamantawa (Analogy)

Ita ce hanyar Kwatanta tsakanin abubuwa guda biyu saboda suna da wani kamammi a sifa ko hali ko adadi da sauransu, sai mu yi hukunci da wannan sifar ga wani abu bisa dogaro da irinta da muka samu a wanda ya yi kama da shi. Kamar idan muka ga wani …

Read More »

Usulubin (Salon) Falsafa

Salon da ake bi a bahasin Falsafa shi ne salon hankali (rational) ta yadda za a kafa dalili a hankalce domin kafa hujja da dalili kan tabbatar da wani abu ko kore shi, sai dai an samu wani canji a gun wasu daga malaman Falsafar yammancin duniya ta yadda suka …

Read More »

Hadafin Falsafa

Hadafi shi ne abin da ake son kaiwa gare shi wanda ake hankoron cim masa da yana iya kasancewa na kusa ko na nesa sakamakon haka ne zamu ga wani lokaci mutane suna daukar hadafi na kusa ba tare da sun kawo na nesa ba. Misali idan ka tambayi mai …

Read More »

MATSAYIN FALSAFA

A bahasin da ya gabata mun yi bincike kan Jigon bahasin Falsafa wato Take da Jigon abin da take magana kansa, a nan kuma muna son magana a takaice game da mas’alolin da take bincike kansu. Idan mun kula zamu ga mun yi bahasin a fakarorin da suka gabata kan …

Read More »

JIGON ILIMIN FALSAFA

Jigon magana (subject) a ilimin Falsafa ya gabata shi ne samuwa, sai dai abin nufi da samuwa a nan ita ce samuwa ta bai-daya, ko samuwa kamar yadda take, kuma muna iya kiran ta samuwa a dunkule (unibersal) ba kebantacciyar samuwa (non-unibersal) ba. Misali Ilimin Falsafa yana bahasi kan samuwa …

Read More »

MA’ANONIN (CONCEPTS) FALSAFA

Ma’anonin Kalmomin bincike da Jumlolin da kowane ilimi yake amfani game da su suna da alaka da jigon bahasinsa ko hadafinsa ne. Mafi yawan Ilimomi sun kasu bisa asasin jigo (subject) ne fiye da yadda aka kasa su bisa asasin hadafi, don haka ne jigon bahasi ya kasance shi ne …

Read More »

FALSAFA A KARNONI BIYUN KARSHE

Idan mun duba zamu ga yammancin duniya a tun lokacin da ya fara fuskanta matsalar juyin tunani bai samu wata mazhaba mai kwari ta Falsafa ba a matsayin wani tsarin tunani da zai iya nuna wa duniya shi, sakamakon haka ma abin dai ya yi yawa lokacin da karni na …

Read More »