Surar Lail

سورة الليل

Surar Dare

Tana karantar da dangantaka tsakanin dabi’a da halitta da akibar mutum bisa aikinsa, da kuma kasuwar abubuwa tsakanin alheri da sharri.

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

 

وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَى

1. Ina rantsuwa da dare a lokacin da yake rufewa.
وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّى

2. Da lokacin rana yayin da bayyana.
وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَى

3. Da abin da ya halitta namiji da mace.
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّى

4. Hakika ayyukanku, mabambanta ne.
فَأَمَّا مَن أَعْطَى وَاتَّقَى

5. To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi takawa.
وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى

6. Kuma ya gaskata kalma mai kyawo.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى

7. To, za Mu saukake masa har ya kai ga sauki.
وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَى

8. Kuma amma wanda ya yi rowa, kuma ya wadatu da kansa.
وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَى

9. Kuma ya karyatar da kalma mai kyawo.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَى

10. To, za Mu saukake masa har ya kai ga tsanani.
وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّى

11. Kuma dukiyarsa ba ta wadatar masa da komai idan ya gangara (wuta).
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَى

12. Lalle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَى

13. Kuma lalle ne Lahira da duniya Namu ne.
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّى

14. Saboda haka, Na yi maku gargadi da wuta mai babbaka.
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى

15. Babu mai shigarta sai mafi shakawa.
الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّى

16. Wanda ya karyata, kuma ya juya baya.
وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى

17. Kuma mafi takawa zai nisance ta.
الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّى

18. Wanda yake bayar da dukiyarsa ,alhali yana tsarkaka.
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَى

19. Alhali babu wani mai wata ni’ima wurinsa wadda ake neman sakamakonta.
إِلَّا ابْتِغَاء وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى

20. Face dai neman yardar Ubangijinsa Mafi daukaka.
وَلَسَوْفَ يَرْضَى

21. Kuma tabbas da sannu zai yarda.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *