Hakkin Sauran Al’umma

Hakkin Mai Yin Alheri: “Amma hakkin wanda ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu’a a tsakaninka da Allah mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zai zama ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka), idan kuwa ba haka ba, to sai ka saurari damar da zaka (rama masa) kana mai sanya wa ranka wannan”.

Hakkin Ladani: “Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mafi girman mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa. Idan kuwa ka kasance mai muhimmantar da gidanka ne (ta yadda ko ya yi kiran sai ka yi zamanka), to kai ba ka muhimmantar da lamarinsa na Allah ba, ka sani shi ni’imar Allah ce kanka babu kokwanto cikinta, to ka kyautata kasancewa tare da ita da godiyar Allah kanta a kowane hali, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Limami: “Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu’a kai ba ka yi addu’a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka da yi maka rokonsa kai ba ka isar masa da wannan ba. Idan an samu wata tawaya tana kansa ban da kai, idan ya kasance mai sabo ne to kai ba ka yi tarayya da shi a cikinsa ba, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan, kuma babu karfi da dubara sai da Allah”.

Hakkin Abokin Zama: “Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi’arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka kura masa idanuwa yayin da kake kallo, kuma ka yi nufin fahimtar da shi idan ka yi magana, idan kai ne ka zo wurin zamansa to kana da zabin tashi idan ka so, idan kuwa shi ne ya zo wurin zama gunka yana da zabi ya tashi amma kai ba ka da zabin tashi ka bar shi sai da izininsa, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Makoci: “Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa ka agaza masa a duka halayen biyu, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma kada ka binciki wani mummunan abu nasa da ka sani, idan kuwa ka sani ba tare da ka bincika ba ko ka dora wa kanka neman sanin, to sai ka zama mai matukar katangewa mai matukar suturtawa, ta yadda da masuna zasu nemi kaiwa ga wani sirrin da ba su iya kaiwa ba saboda tsananin tattarewa gareshi, kada ka saurare shi (da satar jin me yake cewa) ta yadda bai sani ba. Kada ka sallama shi yayin tsanani, kada ka yi masa hassada yayin wata ni’ima, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, kada ka bar yin hakuri da shi yayin da ya yi maka wauta, kuma kada ka fasa zama mai aminci gareshi, kada ka yi masa raddin zagi, ka kuma bata makircin mai zuwa (da sunan yi maka) nasiha (kansa), ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu dubara babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Aboki: “Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) matukar ka samu damar yin hakan, idan kuwa ba ka yi ba to mafi karanci shi ne ka yi masa adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, ka kiyaye shi kamar yadda yake kiyaye ka, a tsakaninka da shi kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, kada ka takaita masa abin da ya cancanta na kauna, ka dora wa kanka yi masa nasiha, da nuna masa hanya, da dora shi kan biyayyar ubangijinsa, da taimakonsa ga kare kansa cikin abin da ya yi nufi na sabon ubangijinsa, sannan ka kasance rahama gareshi, kada ka zama masa azaba, kuma babu karfi sai da Allah.”.

Hakkin Abokin Tarayya: “Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka daidaita kanka da shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra’ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha’ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami, ka sani labari (daga manzon Allah) ya isar mana cewa; hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha’inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Dukiya: “Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta halal, kada ka karkatar da ita daga inda ta dace, kada ka juyar da ita daga hakkinta, kuma kada ka sanya ta ko’ina idan dai daga Allah take sai gareshi tsani zuwa gareshi, kada ka zabi kanka da ita a kan wanda tayiwu ba ya gode maka, ta yiwu (mai gadonka) ba zai kyautata gadon abin da ka bari ba, tayiwu ba zai yi biyayyar Allah da ita (dukiyar) ba sai ya zama kai ka taimaka masa a kan hakan, ko kuma ya zama ya kyautata gani ga kansa da abin da ya farar a dukiyarka sai ya yi biyayya ga Allah da ita, sai ya tafi da riba (ladan aikin alheri da ita) kai kuma ka koma (lahira) da zunubi (saboda tarin haram da ka yi) da hasara da nadama tare da tababbun (mutane), kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai bin Bashi: “Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, ka isar masa da ita ka wadata shi, kada ka hana shi ka yi taurin bashi. Domn Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Taurin bashin mawadaci zalunci ne”. Idan ka kasance maras yalwa, to sai ka nemi yardar da shi da kyautata magana, ka nemi (ya sake ba ka dama ta hanyar) kyakkyawan nema, ka mayar da shi daga kanka mayarwa mai taushin (hali), kada ka hada masa (zafi biyu na) karbar dukiyarsa da yi masa mummunar mu’amala, wannan wani mummunan hali ne, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Abokin Cudanya: “Amma hakkin Abokin cudanya shi ne kada ka yi masa ‘yar rufe, kada ka yi masa zambo, kada ka yi masa karya, kada ka shammace shi, kada ka yi masa yaudara, kada ka yi wai abu na muzantawa gareshi irin aikin makiyin da ba ya rage wa abokinsa komai, idan kuwa ya samu nutsuwa da kai sai ka raga masa ga kanka, ka sani cewa yaudarar wanda ya sakankance (ya saki jiki) da kai (daidai yake da zunubin) cin riba, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai Kara: “Amma hakkin abokin shari’a wanda ya yi da’awar wani abu a kanka, shi ne idan abin da yake da’awarsa a kanka gaskiya ne to kada ka bata hujjarsa, kuma kada ka yi kokarin lalata da’awarsa, sai ka yi husuma da kanka saboda shi, ka yi hukunci a kanka, ka yi sheda gareshi a kanka da hakkinsa ba tare da shedar shedu ba. Amma idan abin da ya yi da’awarsa a kanka ya kasance karya ne, to sai ka tausasa masa, ka hada shi da (girman) addininsa, ka karya zafafawarsa gareka da ambaton Allah. (Ka sani) Jefa masa batanci da mummunar magana ba ya iya kawar maka gabar makiyinka, (idan ka bace shi) sai dai kawai ka samu zunubinsa, da wannan ne kuma zai sake wasa takobin gaba da kai, domin batanci yana tayar da sharri ne, alheri kuwa yana gamawa da sharri ne, kuma babu dubara sai da Allah”.

Hakkin Wanda ake Kara: “Amma hakkin abokin shari’a da ka kai shi kara, (ka sani) idan ka kasance mai gaskiya a kararka to sai ka kyautata maganarsa da (neman) hanyar (samun) mafitar karar, domin kara tana da zafi a cikin jin wanda ake kaiwa kara, kuma ka yi nufin hujjarka da tausasawa, ka saurara kadan, sai ka yi bayani dalla-dalla, ka tausaya da tausayi, kada jayayya da shi da ance-ance ta shagaltar da kai ga barin hujjarka, sai hujjarka ta tafi, kuma ya zama ke nan ba ka da wata riba a nan, kuma babu karfi sai da Allah “.

Hakkin Mai neman Shawara: “Amma hakkin mai neman shawara shi ne; idan wata makamar ra’ayi ta zo maka to sai ka ba shi nasihar, ka yi masa nuni da abin da ka san cewa da kai ne a matsayinsa da ka yi aiki da shi, ya kasance akwai rahama da tausasawa daga gareka, ka sani tausasawa tana kawar da dimuwa, amma kausasawa tana kawar da nutsuwa. Amma idan wani ra’ayi bai zo maka ba, kuma ka san wani wanda ka amintu da ra’ayinsa, ka yarda da shi ga kanka, to sai ka nuna masa shi ka shiryar da shi zuwa gareshi, sai ka zama ba ka hana shi wani alheri ba, ba ka boye masa nasiha ba, kuma babu dubara babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai bayar da Shawara: “Amma hakkin mai ba ka shawara shi ne kada ka tuhume shi idan ya ba ka shawarar ra’ayinsa cikin abin da bai yi muwafaka da kai ba na ra’ayinsa, ka sani ra’ayoyi ne da yadda kowa yake gani da sabanin mutane, ka ba shi nasa zabin ra’ayi idan ka tuhumi ra’ayinsa, amma tuhumarsa ba ta halatta gareka idan dai shi ya kasance wanda yake cancantar neman shawararsa ne gunka, kuma kada ka bar yi masa godiya bisa abin da ya bayyana maka na ra’ayinsa, da kyakkyawar madafar shawararsa. Idan kuwa ya yi muwafaka da kai to sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka, ka karbi wannan shawarar daga dan’uwanka da sauraron damar saka masa da irin wannan duk sa’adda ya zo maka da tasa neman shawarar, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai neman Nasiha: “Amma hakkim mai neman nasiha shi ne ka ba shi nasihar gaskiya wacce kake ganin zai dauka, ka ba shi mafitar da zata tausasa a jinsa, ka yi masa maganar da hankalinsa zai dauka, ka sani kowane mai hankali yana da abin da zai iya dauka na magana da yake iya gane ta kuma ya karbe ta, kuma ma’auninka ya kasance shi ne tausayawa, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai yin Nasiha: “Amma hakkin mai yin nasiha shi ne ka tausasa masa dabi’arka, ka rusuna masa zuciyarka, ka bude masa jinka (ka ba shi fuska), har sai ka fahimci nasiharsa, sannan sai ka yi duba cikinta, idan ya kasance ya dace cikinta sai ka gode wa Allah a kan haka, ka karba daga gareshi ka yi masa alherin nasiharsa. Amma idan kuwa tausayawarsa ba ta samu yin katari ba, kada ka tuhume shi, ka sani cewa shi bai yi maka rowar nasiha ba, sai dai kawai ya yi kuskure ne. Sai dai kuwa idan ya cancanci tuhuma ne a wurinka, to kada dai ka kula da komai nasa ta kowane hali, kuma babu dubara sai dai Allah”.

Hakkin Babba: “Amma hakkin babba shi ne ka girmama shi saboda shekarunsa, da daukaka musuluncinsa idan ya kasance daga ma’abota falala a musulunci saboda rigonsa a cikinsa, da barin jayayya da shi gun husuma, kada ka riga shi wata hanya, kada ka shiga gabansa a wata hanya, kada ka nuna jahilcinsa, idan kuwa ya yi maka wauta to sai ka jure ka daure, ka girmama shi saboda hakkin musulunci da alfarmarsa da shekarunsa, ka sani hakkin shekaru da darajar (gwargwadon) musulunci ne, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Karami: “Amma hakkin karami shi ne ka tausaya masa, da wayar da shi, da koyar da shi, da yi masa afuwa, da suturta masa, da tausasa masa, da taimaka masa, da rufa masa asirin munanan da ya yi lokacin yarinta da kuruciya wannan shi ne (zai zama) dalilin tubansa da tausasa mu’amala da shi, da barin tsokano shi, domin wannan shi ne ya fi kusa da shiryuwarsa”.

Hakkin Mai Roko: “Amma hakkin mai roko shi ne ka ba shi idan alamar gaskiyarsa ta bayyana, kuma (ya zama) kana da ikon biyan bukatarsa, da yi masa addu’ar (Allah ya yaye masa) abin da ya same shi (na talauci), da taimakonsa ga abin da yake neman sa, idan kuwa ka yi kokwanton gaskiyarsa (don haka sai) ka riga tuhumarsa ba ka yi masa wani alheri ba, to ba ka sani ba ko makircin shedan ne da yake son ya hana ka rabautarka ya kare maka kusanci da ubangijinka. Kuma ka bar shi cikin rufin asirinsa (kada ka tona shi idan ka san ba mabukaci ba ne), sai ka mayar da shi mayarwa kyakkyawa (wato kada ka kyare shi sai dai ka hana shi kawai ba tare da wani muzanta masa ba), amma idan ka rinjayi ranka cikin lamarinsa (ka ga ya kamata ka kyautata ka bar zatonka), sai ka ba shi abin da ya nema gunka, to wannan yana daga cikin manyan alherai”.

Hakkin Wanda ake Roka: “Amma hakkin wanda ake roka shi ne idan ya bayar to sai ka karba daga gareshi da godiya gareshi, da sanin kyautatawarsa, ka nema masa uzurin hana ka (idan ya hana ka), ka kyautata masa zato, ka sani cewa idan ya hana dukiyarsa ya hana ke nan, kuma babu zargi a dukiyarsa, idan kuwa ya kasance mai zalunci ne (da hana ka), to mutum mai yawan zalunci ne mai yawan kafirci (rashin godiya)”.

Hakkin Mai Farantawa: “Amma hakkin wanda Allah ya faranta maka rai ta hanyar sa (ta hannunsa), idan da gangan ne ya yi maka to sai ka gode wa Allah sannan sai ka gode masa a kan hakan da gwargwadonsa a mahallin sakamako, ka rama masa a kan kyautatawar farawa da ya yi, ka yi sauraron sai ka rama masa. Amma idan ba da gangan ne (ya faranta maka) ba, to sai ka gode wa Allah ka gode masa, ka sani cewa wannan ka samu ne daga gareshi (Allah) kai kadai, kuma ka so wannan lamarin idan ya kasance dalili ne na samun ni’imar Allah gareka, kuma (shi wannan mutumin) ka so masa (samun) alheri bayan wannan, domin dalilan ni’ima suna da albarka duk inda suke ko da ba na gangan ba, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mai Bakantawa: “Amma hakkin wanda aka kaddara samun mummuna (bacin rai) ta hannunsa da wata magana ne ko wani aiki, idan ya kasance da gangan ne to kai ka fi cancanta da ka yi afuwa, saboda abin da yake cikin (yin afuwar) na kunyata shi, da kyautatuwar ladabinsa, tare da wasu (mutanen) masu yawa irinsa na daga halittu (tayiwu su ma su dauki darasin). Domin Allah madaukaki yana cewa: “Duk wanda ya nemi taimako bayan zaluntarsa to wadannan babu wani laifi a kansu….. daga manyan alherai” (Shura: 40)”.Da kuma fadinsa madaukaki: “Idan kuka yi (ramuwar wata) ukuba, sai ku yi ukuba da irin abin da aka yi muku ukuba da irinsa, amma idan kuka yi hakuri to wannan shi ne ya fi alheri ga masu hakuri” Nahal: 126. Wannan duk a cikin (munana maka) da gangan ke nan.

Amma idan bai zama da gangan ba, to kada ka zalunce shi da ganganta neman yin fansa kansa, sai ka kasance ka dauki fansa da gangan a kan abin da yake bisa kuskure ne, sai dai ka tausaya masa, ka mayar da shi da tausasawa yadda zaka iya, kuma babu karfi sai da Allah”.

Hakkin Mutanen Gida: “Amma hakkin mutanen gidanka gaba daya shi ne ka sanya jin aminci, da yada tausayi, da tausasa wa mai sabawarsu, da yin sabo da su, da neman gyaransu, da godiya ga mai kyautatawarsu ga kansa da kuma gareka, domin (wanda ka) kyautata wa kansa shi ma (wannan aikin) kyautata maka ne idan ya kame cutarwarsa gareka, ya isar maka nauyinsa (ya wadatu da kansa), ya kame kansa daga (cutar) da kai. To ka game su gaba daya da addu’arka, da taimaka musu gaba daya da taimakonka, ka sanya su gaba daya a matsayinsu wurinka, babbansu a matsayin uba, karaminsu a matsayin da, matsakaicinsu a matsayin dan’uwa. Kuma duk wanda ya zo maka sai ka yi sabo da shi da tausasawa da tausayawa, ka sadar da zumuncin dan’uwanka da abin da yake wajibi ne kan dan’uwa a kan dan’uwansa.

Hakkin ‘Yan Amana: “Amma hakkin ‘yan amana (wadanda ba musulmi ba da suke rayuwa tare da musulmi bisa yarjejeniyar rayuwa tare), hukuncinsu shi ne ka karbi abin da Allah ya karba daga garesu (na su yi nasu addinin da rayuwarsu), ka cika musu abin da Allah ya sanya musu na nauyinsa da alkawarinsa, ka yi musu maganarsa cikin abin da suka nema ga kawukansu da aka tilasta su a kansa, ka yi hukunci garesu da abin da Allah ya yi hukunci da shi a kanka cikin abin da yake gudana tsakaninka da su a mu’amala.

Kuma kiyaye alkawarin Allah da cikawa da nauyinsa da ka dauka da nauyin alkawarin Manzon Allah (s.a.w) da ka dauka ya kasance maka katanga da zata hana ka zaluntarsu, domin labarin fadin Manzon Allah (s.a.w) ya isar mana cewa: “Duk wanda ya zalunci dan amana, to ni ne abokin husumarsa”. To ka ji tsoron Allah, kuma babu wata dubara ko karfi sai da Allah”.

Wadannan su ne hakkoki hamsin da suka kewaye ka, ba ka iya fita daga cikinsu ta kowane hali, wajibi ne ka kiyaye su, da aiki da abin da suka kunsa, da taimakon Allah mai girman yabo a kan wannan, babu dubara babu karfi sai da Allah[1].

 

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa’id

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

Saturday, June 04, 2011

[1] Tuhaful Ukul: 260 – 278.

Check Also

42-Daidaito a Hakkoki 2

  Babu wata sura da duniya ta iya kawowa da zata kai wacce manzon Allah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *