Mas’aloli Game Da Annabi – 3

Barbarar Dabino

Muslim[1], da Ibn Majah[2] duk sun kawo cewa manzon Allah (s.a.w) ya ga wasu mutane suna yi wa dabinonsu barbara, sai ya tambayi dalili, sai suka gaya masa. Sai ya ce ya fi kyau su bar wannan aikin, sai suka bi umarninsa. Sai a wannan shekarar duk dabinonsu ya lalace. Sai suka gaya masa abin da ya faru. Sai ya ce: Ai ra’ayin kaina ne na gaya muku don haka ka da ku ga laifina, amma idan daga Allah na gaya muku to ku yi abin da na ce, domin ni ba zan iya yi wa Allah karya ba. A wata ruwayar yana cewa: Ku kuka fi ni sanin duniyarku. A wata ruwayar kuwa tana cewa, sai ya ce; Ni mutum ne ni ma, idan na gaya muku wani abu daga addini to ku yi, amma idan na gaya muku daga kaina to ni fa kamar mutum ne irinku.

Munir Wannan Ruwayar

1- Wannan lamarin da aka nuna ya faru a Madina yana nuna mana cewa ruwayar ba ta inganta ba, domin annabi ya rayu shekaru hamsin cikin al’ummarsa, ya san cewa dabino ba ya fure ya yi ‘ya’ya sai da barbara, ta yaya zai jahilci wannan lamarin!?. Yaya zai jahilci wannan lamarin daga zuwansa Madina!?.

2- An kirkiro ruwayar domin a ba wa sarakuna lasisin keta hurumin shari’a yadda suka ga dama, ta yadda duk abin da suka yi sai su nuna nan ra’ayin annabi ne kan lamarin duniya, don haka ba su da laifi don sun saBa masa a nan. Don haka ne zamu ga labarin keta hurumin shari’ar Allah a wurare da yawa daga sarakuna har zuwa yau.

3- Mafi hadarin Bangaren hadafin wannan ruwayar shi ne kokarin nuna cewa annabi (s.a.w) ijtihadi yake yi ba wahayi ne yake saukar masa kan wasu lamura masu yawa na sha’anin al’umma ba, don haka wannan zai haifar da natijojin da suka fi kowadanne hadari kamar haka:

a- Bayar da kariya ga wadanda suka shahara wurin saBa wa annabi (s.a.w) da cewa ai ra’ayinsa (ijtihadinsa) ne, don haka idan an saBa masa ba komai. Don haka hatta da wasu abubuwan shari’a za a samar wa irin wadannan uzuri. Sai shakar wuyan annabi, rashin biyayya gare shi a Hudaibiyya, rashin bin wasiyyarsa, rashin lizimtuwa da shari’arsa da sauran abubuwan da suka faru a rayuwar halifofi da umayyawa da abbasawa ya samu uzuri ke nan.

b- Mafi hadari kan wannan shi ne sanya manzon Allah (s.a.w) a matsayin mai ijtihadi da fadin ra’ayinsa ba tare da wahayi ba, wannan ke nan yana nufin rusa shari’a da addininsa baki daya, domin mai tambaya zai ce: Ba mu sani ba wanne ne ra’ayinsa, wanne ne kuma shari’a, sai ya zama ke nan babu wani abu da zai lizimta mana karBar maganarsa baki daya. Da wannan ne za a iya rusa sakonsa baki daya, sai duniya ta kalle shi a matsayin mutum kamar sauran mutane, sai ta samu uzuri da rashin lizimtuwa da shari’arsa ke nan.

Da wannan ne aka harbi zuciyar Musulunci! Da wannan ne aka gama da shi!. Sai dai Allah ya yi alkawarin kiyaye addinin da samuwar alayen annabinsa masu tsarki.

Duba ku ga inda aka gama da shi da wannan mummunan harbin yayin da malam Aamudi ya kawo cewa; Shin manzon Allah (s.a.w) yana yin ijtihadi ko kuwa? Sai ya bayar da amsar cewa; Ahmad bn Hambal, da Kadhi Yusuf, da Imam Shafi’i, da Kadhi Abduljabbar, da Abu Husain Albasari, suna da akidar cewa annabi (s.a.w) yana yin ijtihadi. Sai ya ce: Mu ma haka muke gani. Sannan sai ya yi bahasin cewa shin ana samun kuskure a ijtihadin annabi (s.a.w) ko kuwa?[3]!.

Sai suka rabu gida biyu; Wasu suna ganin babu kuskure a ijtihadin annabi (s.a.w). Sai ya ce: Mafi yawan mutanenmu da hambalawa, da masu Hadisi daga mutanen Jiba’i da wasu daga mu’utazilawa suna ganin zai yiwu a samu kuskure a ijtihadin annabi (s.a.w).

Dr Musa a littafinsa na “al’ijtihad wa madaa hajatina ilaihi fi haazal asr” shi ma yana kawowa cewa annabi yana yin ijtihadi a inda ba a yi masa wahayi ba. Haka nan ma zamu ga Muhammad Abduh ya kawo wannan lamarin, kuma yana karfafa cewa a ijtihadinsa yana yin kuskure[4].

Jana’izar Musulunci

Da wannan lamarin ne aka yi janazar Musulunci yayin da zamu ga abubuwan da suka faru kamar haka:

1- Ba wa Abubakar Umar da sauran manyan sahabbai da ‘yan Sunna suke kira goma da aka yi wa albishir da aljanna (idan ka cire Ali tun da shi baya cikin rundunar) uzurin rashin bin su ga rundunar Usama tare da cewa manzon Allah (s.a.w) ya tsine wa duk wanda ya ki bin Usama. Sai suka kawo cewa; Ta yiwu Umar yana ganin ijtihadi ne kawai annabi (s.a.w) ya yi a umarninsa shi ya sa ya ki bin rundunar[5].

2- Fikirar cewa idan ba a ga umarnin annabi (s.a.w) a Kur’ani ba, to tayiwu ya yi ijtihadi ne. Alhalin manzon Allah (s.a.w) ya sanar da al’ummarsa cewa duk wani abu da ya gaya musu na ayar Kur’ani ko zancensa daga Allah ne baki daya, sai dai Kur’ani yana da fifikon cewa Allah ya kare shi daga gurBata, kuma ya yi alkawarin kare shi. Kuma ya sanya shi asalin shari’arsa.

3- Kafa hujja da hadisin barbarar dabino don nuni da cewa annabi yana ijtihadi ne wasu lokuta.

Natija a nan ita ce: Ke nan tun da ijtihadi annabi (s.a.w) yake yi, saBa masa a wasu wurare babu laifi ke nan.

Nunin da nake yi na harbar Musulunci a zuciyarsa da wannan mas’ala yanzu zata fito maka a fili ya kai dan’uwana mai karatu.

4- Da wannan mas’alar ce malam Kushji malamin ilimin Kalam (akida) ya ba wa Umar dan Khaddabi uzurin soke hukuncin annabi (s.a.w) da ya yi na “halaccin mutu’a” da “hajjin tamattu’i” da “hayya ala khairil amal” a kiran salla, da “rusa hanyar raba dukiyar al’umma” saBanin yaddda annabi (s.a.w) yake yi, da wurare masu yawa da suka saBa wa annabi tun a rayuwarsa (s.a.w). Sai malam Kushji ya ba wa Umar uzuri da cewa:

SaBawar da Umar ya ke yi wa manzon Allah (s.a.w) ba yadda za a yi ta bude kofar yi masa nakadi ko raddi ko sukan sa, saboda shi ma ijtihadi yake yi kuma annabi ma mujtahidi ne, kuma saBawar mujtahidi ga wani mujtahidi ba shi da wani aibi[6].

Bisa dogaro da wadannan ra’ayoyi ne zamu ga sunnar Abubakar da Umar ta fi ta annabi daraja domin tana shafe sunnar annabi (s.a.w) amma sunnar annabi ba ta iya shafe ta su.

Wannan shi ne sirrin da mutane masu yawa da suke kiran kansu ‘yan Sunna suka jahilta, kuma wannan shi ne sirrin da ya sanya suka shardanta halifan annabi dole ne ya kasance zai yi aiki da Kur’ani da sunnar Abubakar da Umar, ba tare da la’akari da sunnar annabi ba, wannan ne ya sanya Ali ya ki yarda da wannan sharadin ya rasa halifanci, domin shi ya shardanta littafin Allah da sunnar annabi, sai wannan lamarin ya haramta masa halifanci.

Wannan ne sirrin da ya sanya ba a bar shi ya sakata ba yayin da ya riki jagoranci. Wannan ne kuma ya sanya duk wanda yake bin littafin Allah da sunnar annabi kawai (wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a masu bin sunnar annabi bisa mahangar alayensa) ya cancanci duk wani suka da takura a cikin al’ummar musulmi har yau.

Dan’uwa yayin da kake kukan wannan irin maganar mai cewa Umar mujtahidi ne, annabi ma mujtahidi ne, gaya mini abin da ya rage wa Musulunci baki daya?! Shin akwai wani abin alfahari da ya rage wa irin wannan addinin da annabinsa ya kasance matsayinsa matsayin mujtahidi kamar sauran mujtahidai?!!.

Cutar da Musulmi

Buhari ya kawo a babin “Ludud” da aka fi sani da Hausa da “durar magani ga maras lafiya”, da kuma babin “Diyyat”. Haka nan Muslim a kitabus salam, a babin karhancin yin magani da dura. Sun kawo ruwayar nan da take cewa:

A’isha tana cewa: Mun yi wa annabi (s.a.w) durar magani sai ya rika yi mana nuni da cewa ka da mu yi masa dura, sai muka ce saboda maras lafiya yana kin magani ne. Da ya farfado sai ya ce: Ban gaya muku ka da ku yi mini dura ba? Sai muka ce: Mun dauka ko don maras lafiya ba ya son magani ne. Sai ya ce: Babu wani wanda zai rage a gidan nan sai an yi masa dura ina gani, ban da Abbas domin shi ba ya cikinku. Wannan ruwayar ta zo da sigogi iri-iri, da mafi yawanci tana nuna cewa Abbas ya hana amma suka ki bin umarnin annabi (s.a.w) suka yi masa dura da maganin.

Ruwayar tana nuna cewa an yi wa kowa dura saboda kin umarnin annabi (s.a.w) da suka yi suka yi masa dura. Wasu ruwayoyin suna nuna sun ki bin umarnin annabi (s.a.w) ba su yi kowa dura ba kamar yadda ya yi umarni. Wasu kuwa suna nuna an yi wa kowa dura hatta da maimuna da ta dage kan cewa ba zata iya sha ba saboda tana azumi amma sai da aka yi mata dura! Saboda annabi ya rantse kuma ya dage kan cewa sai an yi wa kowa durar!.

Mai son dubawa sosai sai ya koma wa Buhari, Muslim, Masnad Ahmad, sharhu Nahjul balaga na Ibn Abil Hadid, da Tirmizi. Shi tirmizi yana nuna cewa Abbas da sahabbai sun yi tarayya cikin durar. Sai dai a bisa mafi yawan masu ruwayar sun cire Abbas, wasu sun nuna Abbas ya shigo an gama durar, wasu kuwa sun nuna ya hana amma suka ki suka rinjaye shi da cewa don kin magani ne.

Mafi munin Bangaren wannan lamarin shi ne nuna cewa manzon Allah (s.a.w) bai san an yi masa durar ba sai bayan ya farfado ya ji daci a bakinsa. Kamar dai ya hana yi masa bayan ya ji dacin maganin ne, amma sai ya sake suma, sai kuma suka sake yi masa wata durar.

Ta yiwu mai tambaya ya ce: Ta ina ne aka yi nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) ya cutar da musulmi a wannan ruwayar?. Sai mu ce: Yayin da ruwayar ta nuna cewa ya sanya a yi wa kowa dura hatta da wanda babu ruwansa a ciki, a cikin wannan akwai muzantawa ga annabin rahama da aka sanya shi mai rikon laifin wasu kan kowa.

Hadafin Ruwayar

Wasu malamai sun kawo hadafin kawo wannan ruwayar da ta zo a wadancan litattafai cewa tana son daukaka darajar abbasawa ne, don haka ne aka samo wata falala ga Abbas don a nuna alfaharin da kakansu yake da shi na cewa: Shi yana kiyaye umarnin annabi (s.a.w) a komai bai taBa saBa masa ba. Kuma sun yi nuni da wannan kai tsaye a matsayin abin da hannun abbasawa ya karfafa don samar da falala ga gidansu a wancan lokacin da ake hada ruwayoyi.

Sai dai wasu sun yi nuni da cewa mafi girman hadafin wannan ruwayar domin a ba wa aikin Umar da wasu sahabbai kariya ne da cewa manzon Allah (s.a.w) ya yawaita fita daga hayyacinsa a karshen rayuwarsa a wannan lokacin, har ma ana ba shi magani a yi masa dura bai san inda yake ba. Wannan ra’ayi da wasu malamai suka kawo yana da karfi sosai duba zuwa ga abin da yake kewaye da wannan ruwayar.

A cikin malaman Sunna malam Abu Ja’afar ne kawai ya ki yarda da wannan ruwayar saboda yana cewa: Ba yadda manzon Allah (s.a.w) zai ce a yi wa kowa dura, domin a gidansa akwai Ali, da Fatima, Hasan da Husain (a.s). kuma da haka ta kasance da makiyan Imam Ali da suka hada da wasu daga cikin manyan sahabbai da uwar muminai A’isha da sauransu sun yi masa gori kan hakan. Sai dai duk da haka dalibinsa bahanafe ibn Abil Hadid ya dage kan ingancin wannan ruwayar a littafinsa na sharhin nahjul balaga[7].

Wasu malamai kuma suna kawo cewa an kirkiro wannan ruwayar ne don kawar da tunanin musulmi kan guba da aka shayar da manzon rahama (s.a.w) a karshen rayuwarsa sai dai tarihi ya ki kawo hakikanin lamarin don rufawa.

Mu dai a wannan lamarin ba komai muke son isarwa ba sai cewa manzon Allah (s.a.w) ba ya cutar da kowane mutum, kuma ba zai bayar da umarnin a yi wa kowa dura da abin da aka yi masa dura ba, hatta da wanda bai san an yi masa durar ba. Shi mai tsananin tausayi da rahama da jin kai ne ga muminai, kai shi rahama ne ga dukkan talikai. Shi ne ya fi kowa hankali da tunani da ilimi da sanin Ubangiji da dokokinsa, don haka shi ne ya fi kowa kiyaye hakkin kowane mutum. Sau da yawa abin takaici duk sa’adda aka kirkiro wani abu don kare wasu jama’a ko daga martabarsu sai an rusa martabar annabi da kaskantar da darajarsa da jingina masa wasu ayyukan da bayin Allah masu daraja ta kasa ma ba zasu iya yin sa ba balle kuma fiyayyen halitta.

Don haka ma tarihin da ya inganta yana nuna mana cewa bayan annabin rahama ya yi umarnin wadanda suka yi masa dura su ma su sha abin da suka dura masa babu wani mutum daya da ya sha!. Hatta da Buhari bai yi nuni da cewa wani daga cikinsu ya sha wannan maganin ba. Hasali ma a wannan lokacin babu wani umarni na annabi da yake samun karBuwa, tun daga abin da muke magana kansa na na yi masa dura da abin da ba ya so, har zuwa rashin bin rundunar Usama, har daga karshe kin ba shi abin rubutu don rubuta wa al’umma makomarta ta yadda ba zata taBa Bata ba!.

Mance Kur’ani

A yanzu zai iya yiwuwa wani ya sauwala cewa annabin rahama zai iya mancewa da wata ayar Kur’ani ko ta saraya bai gane ba, sai ya kasance wani yana karatu sai wani ya tuna masa ita?.

Buhari ya ruwaito a ruwayar Hisham daga babansa daga A’isha cewa. Manzon Allah (s.a.w) ya ji wani yana karatu a masallaci sai ya ce: Allah ya yi masa rahama! ya tuna mini da aya kaza da kaza da na saryar da ita a sura kaza da kaza[8]. Ma’anar saryarwa kamar yadda ya zo a wata ruwayar ta Buhari da masu sharhi tana nufin mantawa.

Wannan ruwayar tana daga mafi girman kire da kage da aka jingina wa annabin rahama (s.a.w) don rushe sakonsa musamman mu’ujizarsa mafi girma Kur’ani mai daraja. Kuma idan mun duba zamu ga wannan ruwayar ta ci karo da ruwayar da take cewa an karhanta mutum ya ce na mance aya kaza.

Na biyu kuma ta saBa wa Kur’ani mai daraja da yake cewa: “Da sannu zamu karanta maka ba zaka manta ba”[9].

Idan mun lura a can baya mun yi maganar hanyar tace ruwaya da cewa ana bujuro da ita ga Kur’ani, idan ta saBa masa sai a yi wurgi da ita. Kuma ma’abota shaidana sun san wannan, don haka ne suka yi kokarin gina wani asasi mai hadari da yake cewa Sunna tana shafe Kur’ani amma Kur’ani ba ya shafe Sunna domin duk wani abu da suka kawo wanda zai saBa wa Kur’ani sai ya zama ba za a iya kafa hujja da Kur’ani ba don rusa shi.

Fitsari Tsaye

Buhari da Muslim sun kawo wata ruwaya da aka danganta ta zuwa Huzaifa cewa manzon Allah (s.a.w) ya zo wata bolar wasu mutane sai ya yi fitsari a tsaye, sannan sai ya nemi ruwa ya yi alwala. Daya ruwayar da Buhari ya karBo wacce ta zo daga Huzaifa yana sukan tsanantawa da Abu Musa Al’ash’ari yake yi kan hukuncin bawali ta fi muni, domin tana nuna cewa manzon Allah (s.a.w) bai muhimmantar da tartsatsin bawali da zai iya samun karfarsa saboda yin bawali a tsaye ba.

Lamari na biyu mai muni yadda kuma ya nemi ya tsaya bayansa har ya gama fitsari a tsaye, sai ya kauce ya yi nisa, amma sai manzon Allah (s.a.w) ya nemi ya tsaya kusa da shi har sai ya gama fitsarin a tsaye[10].

Sanannen lamari ne cewa larabawa sun kasance da wannan al’adar a lokacin jahiliyya, kuma Musulunci ya zo ya gyara musu al’adarsu, don haka ta yaya ne wanda ya zo musu da gyara a wannan al’adar shi kuma ya zama yana yin ta?. Ta yaya wanda ya fi kowa kamala zai kasance Huzaifa ya fi shi kunya da kame kai haka?!.

Munin Lamarin

Wasu daga cikin malaman Sunna da suka yi sharhin wannan hadisin sun yi nuni da munin lamarin, sai dai abin haushi maimakon su raunatar da ruwaya sai suka Buge da gyara lamarin kamar dai yadda suka saba yi don kariya ga abin da ake tsarkakewa littafin Buhari fiye da annabin rahama (s.a.w). Mu leka mu ga me suke cewa:

1) Cewa mutanen Jazirar Larabawa a lokacin jahiliyya suna yin fitsari a tsaye don maganin ciwon kugu ko kwankwaso, kuma ta yiwu manzon Allah (s.a.w) ma yana da wannan ciwon.

2) Cewar ko ta yiwu annabi yana da wani ciwo ko maruru da yake hana shi durkusawa ne.

3) Cewar ko ta yiwu babu wani wuri da ya dace ya tsuguna don haka ya zama dole ya yi a tsaye.

4) Cewar yin fitsari a tsaye ya fi kawo aminci ga mafitar bawali, kuma da man Umar dan Khaddabi ma ya ce: Yin fitsari a tsaye yana kiyaye mafitar gayadi. Don haka akwai tsammanin ko don haka ne manzon Allah (s.a.w) ya yi fitsar a tsaye.

5) Cewar ta yiwu wasu lokutan manzon Allah (s.a.w) yana fitsari a tsaye don ya sanar da mutane cewa yin hakan ya halatta[11].

Rashin sanin matsayin annabi (s.a.w) ne ya jawo wannan kariyar da ake yi wa Buhari ba tare da la’akari da matsayin annabi ba. Kuma tsarkin wannan littafin gun mafi yawan sunnawa ya sanya mutanen garin Harat da wasu yankuna na Iraki suke yin fitsari a tsaye dogaro da wannan ruwayar kamar yadda Suyudi ya kawo. Har ma ta kai ga fadin wasu cewa: Ya kamata ne duk shekara ko da sau daya ne mutum ya yi fitsari a tsaye don ya yi aiki da wannan ruwayar.

Babu yadda annabin rahama da ya gaya mana cewa ana azabtar da wani da ke cikin kabari saboda ba ya kiyaye bawali[12], sannan sai ya kasance shi ma ba ya kiyayewa.

Mu mun yarda da hadisin da yake cewa: Manzon Allah (s.a.w) yana fin kowa nisanta da mutane yayin bawali da biyan bukatarsa (ba-haya)[13], da ruwayar da take cewa “Yana zaBar wurin da ya dace don yin biyan bukatarsa (ba-haya) kamar yadda yake zaBar wurin da ya dace ga zamansa”[14], kamar yadda Nisa’i da Tirmizi suka ruwaito.

Da wadannan malamai na sunnawa sun kawar da ta’assubanci (Bangaranci) kan Buhari da Muslim, da sun gwammace su yi kariya ga annabi (s.a.w) fiye da yadda suke kariya ga Buhari da Muslim, da sun fifita kariya ga darajar annabi da matsayinsa fiye da kowane littafi.

Masana sun yi nuni da cewa wannan hadisin an kirkiro shi an jingina shi ga annabi (s.a.w) ne saboda akwai wadanda ake gani da girma kuma sun kasa barin wannan al’adar ta jahiliyya, don haka ne sai ya zama jingina wannan ga annabi (s.a.w) zai wanke nasu laifin. Akwai alamomi masu yawa da suke nuna hakan da suka zo a littattafai daban-daban.

Wata ruwayar Sunan Ibn Majah tana cewa yin fitsari a tsaye al’adar larabawan jahiliyya ce, wata ruwayar a Muwatta tana cewa Abdullah dan Umar yana fitsari a tsaye. Wata tana nuna Umar yana fitsari a tsaye, wata tana nuna Abdullahi dan Umar yana fitsari a tsaye sai annabi ya hana shi, kuma tun daga nan bai sake ba.

A daya Bangaren kuwa sai ga A’isha tana cewa: Duk wanda ya ce maka annabi (s.a.w) ya yi fitsari a tsaye to ka da ka gaskata shi, annabi bai kasance yana yin fitsari a tsaye ba[15]. Don haka magana daya ce ta rage wacce aka nakalto daga Umar dan Khaddabi yana cewa: Yin fitsari a tsaye ne ya fi kiyaye dubura[16].

Tsaface Annabi

Mas’alar sihirce annabin rahama (s.a.w) tana daga cikin mafi girman makamin da Buhari da Muslim da sauran masu ruwayar ‘yan Sunna suka ba wa makiya musuluci. Domin matukar za a yi annabi sihiri a tsaface shi, to babu wata ma’anar a samu nutsuwa da dukkan abin da yake kawowa na wahayi, domin abin da zai ba wa makiya makami shi ne ba mu da wata nutsuwa ke nan da cewa duk abin da ya kawo wahayi ne ko lokacin an tsaface shi ne.

Batun cewa Lubaid dan A’asamu bayahude ya tsaface shi ta yadda ba ya iya ganewa cewa ya yi wani aiki ko bai yi ba, ya kwanta da matarsa ko bai kwanta da ita ba[17]. Wannan ruwayar tana daga cikin abubuwan da suka yi wa addini kwaf daya kuma aka shafa fatihar jana’izar Musulunci da ita.

Makiya sun yi nuni da rashin samun nutsuwa da irin wannan mutumin kuma masu hankali sun san cewa lallai babu wata amsa kan wannan shubuha, domin mutumin da bai san ya yi salla ko bai yi ba, ya yi ciniki ko bai yi ba, gidansa ya shiga ko gidan wani, ya kwana dakin matarsa ko bai kwana ba!? Me kuma ya rage masa har da za a iya dogara da maganarsa ko aikinsa.

A nan ne da kakkusar murya muke kira da duniyar Sunna ta yi tir da wannan ruwayar saboda babu wani makami a yau da ya kai irin wadannan ruwayoyin a hannun makiya a wannan zamanin namu.

Yarda da wannan ruwayar yana nuna mana tsananin karancin sanin annabin Allah ga masu yardar, domin manzon Allah (s.a.w) shi ne hasken Allah na farko, hankalin farko da aka halitta a duniyar mala’iku, mai dauke da sunan Allah mafi girma, don haka babu wani abu ko wani mutum da zai iya yin tasiri kansa a duniyar nan ta jiki. Tasiri kan abu yana bukatar mai tasiri ya fi mai tasirantuwa, shi kuwa annabin rahama (s.a.w) babu wani wanda yake sama da shi sai Ubangiji halitta baki daya.

Mummunan Hadafi

Hadafin wannan ruwayar a fili yake shi ne nuna cewa manzon Allah (s.a.w) yana iya rasa hankalinsa (wal’iyazu bil-Lah!). Kuma ko da yaushe matsafa suna iya kawar da hankalinsa ta hanyar tsafi, don haka akwai yiwuwar ya zama wasu lokuta ya fada wannan lamarin.

Sai ya ji kamar ya isar da wahayi alhalin bai isar ba, sai ya ga kamar ya yi salla alhalin bai yi ba, sai ya ga kamar ya zo wa matarsa da dare alhalin bai zo mata ba. Yaya Allah zai jingina dukkan sakonsa kan irin wannan mutumin da yake iya shiga wannan halin, yaya Allah zai dogara kan mutumin da masu rufa ido da matsafa suke iya kawar da hankalinsa!?.

A fili yake cewa irin wannan shirmen mustahili ne ya samu annabin rahama mai tsarki da daraja, fiyayyen bayin Allah a daukaka da matsayi, hasken farko mai haskaka sauran halittu!. Yaya za a yi mutumin da Kur’ani mai daraja ya nuna ba a iya siherce shi, kuma Allah ya yi masa shedar cewa duk wani abu da yake kawowa daga Allah ne, sai kuma ya fada cikin mafi munin sihiri da za a yi wa dan’adam, mafi munin sihirin da mutum yake rasa hankalinsa!.

Ubangiji kai ne shaida mu mun barranta daga maganar jahilai!.

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] (a babin falala Hadisi 2361 – 2363).

[2] (a babin Barbarar Dabinu a j 2).

[3] Al’ahkam, fi usulil Ahkam: j 4, s 134. ( Al’ahkam, fi usulil Ahkam: j 4, s 134.).

[4] Alamanar: j 10, s 465 – 466.

[5] Ibn abl hadid; sharhun nahjul balaga: j 17, s 176.

[6] Qushji; sharhuttajrid: fasalin Imama.

[7] sharhin nahjul balaga, j 13, s 32, h235.

[8] Buhari: j 8, Kitabud Da’awat. Buhari: J 3, kitabus shahadat; h 5976.

[9] A’ala: 6.

[10] Buahri: j 1, Kitabul wudhu, babul bauli…, h 222, da kuma j 3, h 223, da j 1, h 2339.

[11] Fatahul Bari: j 1, s 343. Irshadus Sari: j 1, s 277, da j 4, s 265. Sharhu Nawawi: j 3, s 165. Sharhu Sunan Nisa’i: j 1, s 20.

[12] Buhari: j 2, kitabul Jana’iz, babu azabul qabari minal fitnati walbauli. Muslim: j 1, babu addalil ala najasatil baul. Abu Dawud; j 1, s 5. Nisa’i: j 1, s 28.

[13] Nisa’i: j 1, s 21. Tirmizi: j 1, s 17.

[14] Tirmizi: j 1, s 17.

[15] Tirmizi: j 1, s 10. Ibn Majah: j 1, s 112. Nisa’i: j 1, s 26.

[16] Fatahul Bari, j 1,s 343. Irshadus Sari: j 1, s 277, da j 4, s 265, da sharhun Nawawi: j 3, s 165.

[17] Buhari: j 7, Kitabut Tib, babus Sihr. Muslim: j 7, Babus sihr.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *