Annabci A Buhari Da Musulim

Annabci matsayi ne mai daraja da daukaka da babu mai samun sa sai mutumin da ya kai matukar matsayin daukaka da daraja da kamala. Kur’ani mai daraja ya yi nuni da wannan lamarin na zaBin Allah ga bayinsa masu daraja[1] kuma Allah ne ya san inda yake sanya sakonsa[2].

Annabawa su ne suka fi kowa tsarkin rai da daraja da girma da tsarkaka da karfi, suka fi kowa kyawawan halaye da sanin Allah. Don haka ne suka cancanci matsayin masu shiryar da mutane da nuna musu hanya zuwa ga tsiransu da sanar da su tsarinsu na duniyarsu da lahirarsu.

Idan mun duba kissoshin annabawa zamu samu cewa su ne suka fi kowa nagarta da kyawawan halaye a cikin al’ummarsu, tun kafin a aiko su al’ummarsu takan shaida da tsarkinsu. Mutanen annabi Salihu suna cewa da shi: “… ya Salihu kai ka kasance abin kauna a cikinmu kafin wannan …”. Haka nan zamu ga ‘yan matan nan ‘ya’yan annabi Shu’aibu (a.s) suna fada wa babansu game da annabi Musa (a.s) cewa; “… mai karfi amitacce…”. Kamar yadda zamu ga manzon Allah (s.a.w) ya shahara da sunan “amintacce” a cikin al’umarsa.

Ismar Annabawa

Ismar ananbawa tana daga cikin abin da yake abin sallamawa da shi gun dukkan musulmi a dunkule, Allah madaukaki ya dauki nauyin shiryar da annabawa shiriya ta musamman da babu wata hanyar Bata tare da ita. Allah yana cewa: “… wadannan su ne wadanda Allah ya shiryar, sai ka yi koyi da shiriyarsu…”[3]. Tun da Allah madaukaki ya shiryar da su shiriya ta musaman wannan yana nuna cewa babu wata hanyar Bata gare su, kuma tun da Allah ya yi umarni da bin shiriyarsu wannan yana nunawa a fili cewa babu wani Bata ko kauce hanyar shiriya ga wanda ya bi tafarkinsu.

Idan muka koma wa Kur’ani zamu samu cike yake da ayoyi masu yawan gaske da suke tsarkake annabawa daga dukkan Bata da kauce hanya ko wani saBo, kuma a wurare masu yawa ya karfafa cewa bai aiko su ba sai don a yi biyayya gare su. Kuma Allah ba zai sanya mutane su yi biyayya ga wanda yake wasu aiyukansa saBo ne ba, domin idan ya yi hakan kuma mutane suka yi saBo, to ya zama ke nan shi ne ya bude musu hanyar yin saBo. Don haka annabawa ma’asumai ne daga dukkan irin wani saBo.

ANNABI A KUR’ANI DA HADISI

Kur’ani mai daraja ya siffanta annabin rahama da cewa shi ne ya fi kowa kyawawan halaye, kuma tsatsonsa yana da tsarki domin ya fito daga dukkan masu sujada ga Allah ne[4]. Kamar yadda tarihin gidan hashimawa ya shahara da cewa su masu bauta wa Allah ne tun lokacin annabi Ibrahim (a.s) babu wani daga tsatsonsu da ya kasance mai bautar gumaka har zuwa kan annabin rahama (s.a.w).

Wannan tsarkin bai takaita ga manzon Allah (s.a.w) ba, domin ya hada har da alayensa masu tsarki, Allah mai daraja da daukaka ya yi nuni da wannan a ayar nan ta 33 daga surar Ahzab da fadinsa cewa: “Lallai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gare ku Ahlul-baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”. Kuma wannan tsarkin tsarki ne na halitta ba na shari’a ba, domin idan ya kasance na shari’a da bai keBanta da su ba, don haka ne zamu ga manzon Allah (s.a.w) ya keBance wannan tsarki da shi kansa da Ali, Fatima, Hasan, Husain (a.s) a wasu ruwayoyi mutawatirai[5].

Tsarkin da manzon Allah (s.a.w) yake da shi ya fara tun daga annabi Adam (a.s) har zuwa kansa da shi da wasiyyansa wanda na farkonsu shi ne Imam Ali (a.s), kuma lallai wannan yana nuna mana a fili cewa suna da tsarkin ruhi a halittarsu ba tare da wata daudar kafirci ko ta zina ta taBa samun wani daga cikin kakanninsu ba. A nan ne ya zama wajibi duk wani abu da ya saBa wa wannan koyarwar ta Kur’ani a yi watsi da shi.

Daudar shirka, daudar munanan halaye, daudar saBa wa shari’ar Allah, daudar rafkanwa da gafala duka sun koru ga manzon Allah da tsarkakan alayensa kamar yadda aya ta nuna, kuma wannan yana nufin tsarki da babu kamarsa. Don haka ne ya kasance kamamme, amintacce, da dukkan siffofin kamala tun lokacin haihuwarsa har barinsa wannan duniyar, don haka duk wani abu mummuna da aka jingina wa annabin rahama (s.a.w) da alayensa (a.s), ko wani daga cikin annabawa da Allah ya tabbatar da cewa ya shiryar da su kuma ya yi umarni da bin shiriyarsu to Batacce ne.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana bauta wa Allah tun yana karami tare da amminsa Abutalib yayin da yana dan shekara hudu ya yi tafiya da shi zuwa Basara. Ya kasance yana keBancewa daga mutanensa yana bautar Allah shi kadai sai yaron da yake tare shi wato dan renonsa Ali (a.s). Ruwayoyi masu yawa sun yi nuni da yin hajjinsa da ibadojinsa a Boye tun kafin a aiko shi[6].

Annabin rahama Muhammad Al’mustafa (s.a.w) ya taso cikin tsatso mai tsarki da asali da Allah bai yi wa wani tsatso mai daraja irinsa ba. Sannan kuma sai ya tsarakake shi daga duk wata daudar jahiliyya yayin da yake cewa : “Na fito tun daga Adam daga aure ba tare da wata alfahasha ta shafe ni ba”[7].

Ya siffantu da dukkan siffofi nagari, ya kai kololuwar kamala da ya kasance amintacce a al’ummarsa har ta dogara da shi a komai nata, sannan sai Allah ya aika shi zuwa ga mutane yana mai yabonsa da siffofin kamala yayin da yake cewa: “Hakika manzo daga kawukanku ya zo muku, abin da ya ke Bakanta muku rai yana yi masa nauyi, mai yawan kwadayin alheri gare ku, mai tausayi da jin kai ga muminai”[8].

Kur’ani ya siffanta shi mai tausayi, mai rahama da jin kai, ba don ya kasance mai haka ba da sun watse daga gare shi[9]. Haka nan ma yana jin nauyin yi wa sahabbansa magana su fita daga gidansa bayan cin abinci har sai da Allah ya yi musu fadan hakan[10].

Kuma ya fara tarbiyyar mutum na farko da ya damfaru da shi a matsayin dan renonsa wato Ali (a.s). Imam Ali yana cewa: Ni ne bawan Allah kuma dan’uwan manzonsa, ni ne siddik mafi girma, kuma babu wani mai fadin wannan bayana sai makaryaci mai kage, na yi salla kafin mutane shekaru bakwai[11]. Wani lokaci ya yi wa kansa da lakabin Siddik da Faruk yana mai cewa babu mai kiran kansa da wadannan lakabobi sai makaryaci.

Muhimmin lamari ne a nan mu ga yadda manzon rahama (s.a.w) ya fara yi wa dan renonsa tarbiyya tun kafin a aiko shi da shekaru bakwai. Ya kasance yana daukar sa zuwa kogon Hira har Allah ya yi masa wahayi sannan sai ya shelanta lamarinsa ga sauran Banu Hashim kafin sauran mutane.

Wahayi da Ijtihadi

Wahayi fahimta ce ko sako da Allah ya ke sanya ta ga bawansa da ya zaBa, sau da yawa ana kiran ta da ilhama. Tana iya kasancewa ta hanyar mafarki, aiko mala’ika, magana ta hanyar wani abu, ko sako kai tsaye daga Allah zuwa ga bawansa ba tare da wata tsakiya ba. Wahayi yana kasancewa bayyananne ba tare da wani Boyuwa ko rashin gane inda yake ba, wanda ake yi wa wahayi yana sanin cewa daga Allah ne, don haka babu wani abu da yake Buya gare shi.

Wanda ake yi wa wahayi ya saBa da masu yin ijtihadi, a ijtihadi malami yana koyon ilimi ne har ya kai wani mataki da yake iya fitar da hukuncin shari’a, amma a wahayi wani sako ne da Allah yake ba wa wanda ya zama, sai ya sanar da shi gaskiyar komai ba tare da wani kuskure ba domin daga Allah ne, don haka ne sakon da annabawa suke zuwa da shi ya kasance ba tare da wani kuskure ba kuma ya zama wajibi ga kowane mutum ya karBe shi.

Duk wani wanda zai zo da wani abu na da’awar cewa annabi ya yi kuskure a isar da sako, ko kuma bai ji daidai ba, ko bai fahimta daidai ba, ko kuma wani abu yana iya shiga tsakaninsa da wahayin da ake yi masa, ko kuma suna yin jayayya da wani daga sahabinsa sai wancan sahabin ya yi daidai shi kuwa annabi (s.a.w) ya yi kuskure, to duk wannan magana ce Batacciya da ba ta da wani asasi daga shari’a.

Babu wani mutum da ya fi annabi daraja ko ilimi, ko fahimtar gaskiya, ko sanin abin da ya fi dacewa a kowane hukunci. Umayyawa sun yi kokarin rusa kimar annabi ta hanyar nuna shi a matsayin mutum ne mai karancin ra’ayi, sau tari yakan yi magana sai ra’ayinsa ya ki dacewa sahabbansa su fi shi gaskiya. Sau tari bai taBa jayayya da Umar sahabinsa ba sai ya kasance gaskiya tana tare da sahabinsa Umar da sauran hanyoyi da suka bi don rusa kimar annabi (s.a.w).

Sai dai mafi muni ba su ne umayyawa da suka kirkiro wannan a rayuwar annabi ba, wanda ya fi su muni shi ne wanda ya dauki wannan batsattsale ya yada shi ya kuma yarda da shi, ya dauki nauyin yada shi da koyar da shi cikin al’ummar musulmi. Maganar gaskiya babu wani mutum da ya fi manzon Allah (s.a.w) karfin tunani da ra’ayi da sani da ilmi, babu wani wanda ya fi shi kamala a kowane fage baki daya.

ANNABTA A GUN AHLUL-KITAB

A cikin Attaura da Injila an siffanta annabawa da siffofin da wani lokaci zamu ga hatta da mutanen da suke rayuwa a titina wadanda ba su san ubangijinsu ba wani lokaci sukan guji irin wadannan siffofin. Mafi yawan siffofin kaskanci da aka jingina wa annabi lokacin halifofi na farko ko lokacin umayyawa ya samu tasirin daga malaman Yahudawa da na Kiristoci da suka musulunta ne kuma halifofi da sarakuna suka ba su damar bayar da karatu da fatawa ga mutane, sai suka yi amfani da wannan damar.

Don haka zamu ga wani muhimmin abu a tarihin halifancin Imam Ali bayan an yi masa bai’a shi ne farkon abin da ya yi na korar irin wadannan masu bayar da fatawar na jahilan masu bayar da kissoshi, da kuma ahlul-kitabi da suka musulunta suka samu wurin bayar da fatawa ga musulmi a masallacin annabi.

Da yawan kissoshin annabawa da suka zo a littattafan da suka gabaTA na ahlul-kitab sun cire tsentseni hatta da mutunci ga annabawa, balle kuma su kasance masu kamalar da ya kamata a yi koyi da su. Zamu ga babu isma tare da annabawa a akidarsu, don haka ne suka jingina musu kowace irin tawaya.

Suna ganin annabawa suna samun wahayi ne daga Allah kuma wannan ne lamarin fifikonsu kan sauran mutane, amma batun ismarsu daga saBo babu ita. A nan ne zamu ga Yahudawa ba sa ganin ismar annabi Musa (a.s) duk da kuwa suna ganin shi ne mutumin da ya fi kowa daraja a duniya.

Na farko: A kissar annabi Lut (a.s) da ‘ya’yansa mun ga yadda Littafin ahlul-kitabi ya nuna yadda ‘ya’yan annabi Lut (a.s) ‘yan mata guda biyu da suke rayuwa tare da shi a dutse suka ce da junansu. Babbar ta ce: Ga babansu ya tsufa, ga shi ba mu da wani namiji da zai aure mu. Zo mu ba wa babansu giya idan ya bugu sai mu kwanta da shi, sai suka ba shi giya sai babbar ta kwanta da shi bai sani ba. A rana mai zuwa sai ta ce da ita: Yau ma zamu ba shi giya idan ya bugu ke kuma sai ki kwanta da shi, sai kuwa suka yi hakan.

Sai duka ‘yan matan biyu suka samu ciki, babbar ta haifi yaro da suka sanya wa suna “Mu’ab” shi ne baban kabilar “Mu’abawa”, karamar ma ta haihu aka sanya masa suna “Ibn Ama” shi ne baban “Banu Amun”[12].

Na biyu: Attaura ta jingina wa annabi Dawud (a.s) kwanciya da matar Urya, da ya ga ta samu ciki sai ya aika wa Urya ya dawo daga yaki, da ya zo sai ya ba shi umarni ya tafi gida ya kwanta da matarsa. Amma sai Urya ya ki zuwa ya rantse da Allah ba zai yi ba. Ganin haka sai Dawud ya ce ya zo gidansa ya ci abinci tare da shi. Sai Dawud ya ba shi abinci da giya ya bugu, sannan sai ya mayar da shi filin yaki, ya kuma ba wa kwandansa “Yu’ab” umarnin ya sanya Urya a gaban yaki inda kibau suke sauka, sai ya yi haka, sai Urya ya yi shahada. Da labarin kashe shi ya zo wa Dawud sai ya shriya zaman makoki gare shi, sannan sai ya mayar da matarsa gidansa ya sanya ta cikin matansa, har ta haife masa wani yaro[13].

Bayan Attaura ta kawo wannan kissa, sai kuma ga shi Injila tana cewa Wannan yaron shi ne Sulaiman[14].

A Injilar Yohana Isa Masihu ya yi tarayya a wurin angwancin wata amarya, da giyarsu ta kare sai ya sake yi musu wata giya mai yawa ta hanyar mu’ujiza suka yi ta sha[15].

A injilar Luka zamu ga Isa Masihu ba kawai giya ba, har kayan alkahol duka yana sha[16].

Wadannan su ne misalai na siffofin annabawa da zamu ga daga mai kwanciya cikin maye da ‘yarsa bai sani ba, sai mai lalata da matar kwamandansa, sai kuma mai shan giya ko ma ya yi giya ga mutane su sha. Irin wannan ne suka so su yi wa annabin Musulunci suka kasa kai shi matsayin munanan halaye da Attaura da Injila take cewa game da annabawa.

ANNABTA A BUHARI DA MUSLIM

Abin takaici ne mu samu irin wadannan isra’illiyyat a cikin Buhari da Muslim da yake nuna mana cewa akwai tasirin makircin Umayyawa da suka fada cikinsa ko da sani ko da rashin sani. Sai muka samu kissoshin annabawa kamar tatsuniya wani lokaci a bayar da labari kamar ana isgili da annabi ko abin dariya da sauran kissoshi da idan aka bayar da su game da wani mutum da muke girmamawa fushinmu zai taso. Idan muka dora wadannan kissoshin a kan sikelin Kur’ani zamu samu cewa wadannan kissoshin sun yi hannun riga matukar gaske musamman game da fiyayyen halitta da Allah ya yabe shi da siffofi madaukaka.

Mun san cewa an yawaita yi wa annabin Allah karya har sai dai ya shelanta cewa duk wanda ya yi masa karya to ya tanadi mazauninsa a wuta. Umayyawa musamman lokacin Mu’awiya dan Abusufyan sun sami karfin kirkiro hadisai masu yawan gaske don muzanta annabi da dan’uwansa Ali da duk wani daga hashimawa. Sai abin da yake hannun mutane ya kasance cakude ne na gaskiya, da karya, shafaffe, da mai shafewa, muhkam, da mutashabih, da sauran kire da aka jingina wa annabin rahama (s.a.w)[17].

Ta wani Bangaren suna son ganin sun sauko da darajar annabi ta hanyar nuna cewa shi ma mutum ne wanda kowane irin hali na jahiliyya yana iya aiwatarwa domin su shirya wa kafa hukumar da mutum fasiki irin Yazid zai iya zuwa ya zama jagoran mutane. Kuma ba su da wata babbar hanyar cimma kafa hukuma irinta Yazid sai ta hanyar nuna cewa Musulunci da annabin rahama ba su da wata kamala da ta dara ta sauran mutane, don haka ke nan kowane irin mutum zai iya zuwa ya maye kujerar halifancinsa.

Kafin mu kawo misalai yana da kyau mu yi nuni da cewa Abuhuraira babban mai ruwaya ne da ya samu cakudewa tsakanin hadisin da ya ji gun annabi da kuma wanda ya ji a wurin malaminsa Ka’abul Akhbar kamar yadda malam Abu Rayya na Jami’ar Azhar da sauran wadanda suka yi rubutu game da Abuhuraira suka kawo a littafinsa “Abuhuraira”. Mafi yawan ruwayoyin da suke sukan daraja ko kaskantar da annabawa babu wani kokwanto ba sa wuce cewa suna daga abin da ya ji daga malaminsa Bayahuden da ya musuluta kuma halifofi suka ba shi damar bayar da karatu da ilimi wanda Abuhuraira suna daga cikin dalibansa.

Don haka ne da yawan marubuta game da Abuhuraira duk da sun bar bincike mai zurfi kan da gangan ne yake yin haka ko bisa kuskure sai dai zamu ga wasunsu sun tafi a kan lamarin farko. Sai dai abin da ba su yi inkari ba shi ne cewar yana cakudewa tsakanin abin da ya ji daga annabi a lokacin da ya gabata wanda ya dauki shekaru domin bai rayu da annabi ba sai watanni 16-18, sai ya sanya shi yaron gwamnansa ya aika shi tare da shi Bahrain, bai sake ganin annabi ba kusan shekara biyu har annabi ya rasu, kuma bai dawo Madina ba sai lokacin halifancin Umar, to bisa al’ada ne ya manta da duk wani abu da ya ji daga annabi tun da ba rubutawa ya yi ba.

Amma cakuda abin da ya ji daga annabi (s.a.w) da wanda ya ji daga malaminsa Ka’abul Akhbar wani abu ne da babu mai kokwantonsa. Wannan cakudawar tana iya yiwuwa sakamakon dalilai daban-daban da masu tarihi suka yi magana a kai, kuma hidimarsa ga Mu’awiya da abin da ya sani shi ne mafi girman abin da ya haifar masa da jingina wannan lamarin ga annabawa kamar yadda zamu kawo.

Domin Abuhuraira ya fada cewa: Ali ya fi ilimi, amma Mu’awiya ya fi maiko, sai dai dutse (wato zama ba tare da shiga yaki ba) ya fi kuButar da rai. Kuma mun san yadda Banu Umayya suka ba shi matsayi da aura masa mata daga danginsu, duk wannan ya yi masa tasirin karkata da hidimarsa gare su da dukkan abin da zai iya. Ta yiwu ya fara wannan lamarin tun lokacin halifancin Umar dan Khaddabi don haka ne Umar ya hana shi bayar da Hadisi ya yi masa bulala, kuma ya yi masa alkawarin ukuba mai tsanani idan ya ji ya sake bayar da Hadisi.

Muhimmin abin da nake son kawowa a nan shi ne babu wani kokwanto hadisan da Abuhuraira ya kawo masu rage darajar annabawa wadanda suka yi kama da na Attaura tabbas ba daga annabi ba ne, daga malamansa da suka musulunta na daga Yahudawa da Kiristoci irinsu Ka’abu, da Abu Rukayya Tamim bin Ausuddari. Kuma wanda yake son fadada bahasin kan wannan lamarin to ya koma wa littattafan da aka rubuta game da Abuhuraira kamar na malam Abu Rayya na Jami’ar Azhar.

1- Karyar Ibrahim

Buhari ya zo da ruwaya daga Abuhuraira da take nuni da cewa annabi Ibrahim (a.s) ya yi karya da jur’a irin wannan. Suna nufin batun matarsa da ya ce wa sarki ‘yar’uwarsa ce, da batun gumaka da ya ce babbansu ne ya yi, da batun rashin lafiya yayin da ya ki fita zuwa bukin shekarar mutanensa.

Sai dai lamarin takiyya ko tauriyya wani abu ne sananne a al’adu da addini, kuma mai hankali yana gane wannan lamarin, sannan bai fita daga irin abin da ya fada ba game da rana, wata, da taurari, sai dai ba mu san dalilin da ya sanya suka ki kawo wannan ba don karyar ta zama guda hudu.

Sannan a batun ceto da ya kawo uzurin ba zai iya ceto ba saboda ya yi karya uku, idan wannan karyar da suke fada ta kasance don kare addini ko ransa ko al’ummarsa da shiryar da ita ne me zai hana ya zama daga babin abin da addini ya zo da shi na “Takiyya”. Ammar bn Yasir da sauran musulmi da suka fadi saBanin akidarsu suka yi “Takiyya” don su tsira daga ransu me ye hukuncin Allah a kan abin da suka yi, shin ba mu ga manzon Allah ya karfafe su kan su maimaita ba matukar suka sake samun kansu a cikin irin wannan matsalar ba!.

Ta wani Bangaren zamu ga yadda wannan hadisin ya yi kama da kissar Ibrahim da ta zo a cikin Attaura yayin da ya tafi Misira, sai mutanen Misira suka ga mace mai tsananin kyawu sai suka kawo ta wurin sarki. Kamar yadda ya zo a cikin Attaura[18].

Sannan cewa annabi Ibrahim yana neman kariya daga cutuwa gun sarki da neman matsayi gurinsa idan sarki ya ji cewa matarsa ‘yar’uwarsa ce kuma ya aure ta, sai ya zama daga makusanta wurin sarki ke nan, wannan ne lamari da ya fi muni daga dukkan wani abu da aka fada a ruwayar. Yaya zai yi haka ya bayar da matarsa kan amfanin da babu tabbas gare shi, shin akwai mai hankali da zai yi hakan balle shugaban masu hankalin duniya annabin Allah Ibrahim (a.s) masoyin Ubangiji!.

2- Kwanciyar Sulaiman da Mata

A nan ma zamu ga Buhari ya kawo ruwaya daga Abuhuraira cewa Sulaiman (a.s) ya rantse cewa zai kwanta da matansa 100 ko 99 kowacce ta zo da yaro da zasu yi yaki a tafarkin Allah, sai mala’ika ya ce da Sulaiman ya ce in Allah ya so amma ya ki fada!. Sai wai annabin rahama (s.a.w) ya ce: Da ya fada da duka sun haifi ‘ya’ya amma sai guda daya ce ta zo da Bari. Idan mun duba wannan ruwayar zamu ga tana da rauni ta wasu fuskoki:

a- SaBanin ruwayoyin tare da cewa sun zo ne a Buhari da Muslim wasu su ce 100, wasu kuwa 99, wasu kuwa 60, da sauransu. Kuma da yawa wasu ma sun yi nuni da wannan raunin da yake cikin wannan ruwayar.

b- Wane mutum ne zai iya fuskantar mata masu yawa haka a dare daya, kuma yaya za a iya samun wani mutum ya yi hakan, alhalin dan’adam ba zai iya haka ba. Kuma idan an ce yin hakan zai zama mu’ujiza ne to wannan ba mahallin mu’ujiza ba ne, kuma mu’ujiza ba haka kawai take faruwa babu wani dalili ba.

c- Tsawon dare ba zai iya isa ga wannan lamarin ba ga kowane mutum, don haka wannan yana nuna cewa wannan ruwayar kage ce.

d- Sannan annabawa ba sa gafala daga Allah balle Sulaiman (a.s) ya bar fadin “In Allah ya so” balle kuma a tare da tunin da mala’ika ya yi masa sai ya ki fada. Wannan irin aikin mutane ne masu taurin kai da kin gaskiya da jin suna dogaro da kansu ba da Allah ba. Sha’anin girma da darajar annabawa ya fi karfin hakan.

3- Marin Azara’il

Abuhuraira ya fadi cewa: Annabi Musa (a.s) ya mari mala’ikan mutuwa saboda yana jin haushin ya zo daukar ransa, kuma mala’ika ya kai kuka wurin Allah sai Allah ya mayar masa da idonsa. Sa’alabi ya yi kokwanto kan wannan ruwayar yayin da yake cewa shi ba shi da wata mahanga kan inganci ko rashin ingancin wannan ruwayar. Idan mun duba yaya zamu ga wannan ruwayar ta mahangar hankali da ilimi kan wadannan lamurran:

1- Yaya Allah zai zaBi mutum mai irin wannan halin da tsoron haduwa da shi hakan a matsayin annabi da zai yi wa al’ummar duniya alfahari da shi har ya kira shi abin yi wa maganarsa (Kalimul-Lah).

2- Maimakon Musa (a.s) ya zama Allah ya yi masa fadan abin da ya yi na fasa idon mala’ika ma, sai ma aka ce to ya zaBi san/saniyar da ya ga dama ya dora hannunsa a kai, iyakancin adadin gashin da hannunsa ya rufe zai samu yawan shekarun hakan, wannan shi ne ladansa da zai samu sakamakon mari da fasa idon mala’ika. Kuma da ya yi shekaru adadin gashin da hannunsa ya rufe da yanzu haka yana raye tare da mu bai cinye ko daya bisa goma na rayuwarsa ba sakamakon cewa tafin hannunsa zai rufe gashi mai yawan gaske a fatar jikin san/saniyar.

3- Musa (a.s) da yake daya daga cikin Ulul-azm yaya zai kasance da wannan halin alhalin yana daga cikin mafifita halittar Allah a bayan kasa, tabbas wannan halin ya saBa da na bayin Allah tsarkaka da yake zaBa a cikin bayinsa.

4- Shin zai yiwu mu yarda cewa annabawa (a.s) zasu wulakanta mala’iku yayin da mala’iku suke isar musu da sakon Allah (s.w.t). A yayin da muke zargin Fir’auna, Karuna, Abujahal da sauran masu girman kai domin sun ki karBar sakon Allah, to a kan me zamu jingina irin wannan halin ga annabawan Allah. Su kuma idan sun ki umarnin Allah wane matsayi ke nan za a ajiye su!.

5- Wai shi mala’ika yana da ido da jiki irin na mutane ne har da za a mare shi a fasa masa idonsa. Kuma shin mala’ika yana fitowa fili ne ga mutane yayin da zai dauki ransa annabawa ne ko waninsu.

Wannan ne ya sanya Abuhuraira ya bayar da amsa kan wannan lamarin da cewa: Ai mala’ika ya kasance yana bayyana ga mutane kafin wannan lokacin ne, amma tun da Musa (a.s) ya mare shi ya fasa masa ido sai ya ke zo musu a Boye!.

Abin mamaki ne da ya zama a Muslim ya ruwaito wannan a cikin falalolin annabi Musa (a.s), ba mu san wace falala annabi Musa (a.s) yake da ita a cikin irin wannan lamarin mai muni ba.

4- Tsaraicin Musa

Abuhuraira ya sake ruwaito cewa; Musa (a.s) ya kasance mutum mai yawan kunya don haka yake lulluBe jikinsa baki daya, ba ya bari wani mutum ya ga jikinsa ko yaya, sai suka tuhume shi da cewa tayiwu yana da wata cuta kamar kuturta ko gwaiwa ne don haka ba ya son ganin jikinsa. Wata rana ya je wanka a rafi ya ajiye tufafinsa a kan wani dutse, sai Allah ya so ya kuButar da shi ya nuna wa Banu Isra’il cewa ba shi da wata cuta ko kadan, sai da Musa (a.s) ya gama wanka ya zo daukar tufafinsa sai dutsen nan ya gudu da tufafin, sai Musa ya bi shi da sanda yana! Kai dutse ba ni Tufafina! Kai dutse ba ni Tufafina! Kai dutse ba ni Tufafina! Har sai da dutsen nan ya zo sarari cike da mutane (kamar tsakiyar kasuwa a ranar kasuwa ko cikin gari inda ya fi cikowar jama’a) sai ya dakata. Sai Musa ya dauki tufafinsa bayan duk mutane sun ga tsaraicinsa ba shi da gwaiwa. Sai Musa ya fusata ya doki dutsen nan da sanda da karfi.! Abuhuraira yana cewa: Na rantse da Allah akwai tabo a jikin dutsen saboda ciwon da Musa ya ji masa!.

Zamu ga Buhari ya kawo wannan hadisin a babin wanka tsirara a keBe, daga J 1, b 20, h 271. Da cikin juzu’i na hudu, Kitabul Anbiya, b 29, h 2332. Muslim ma ya kawo shi a babin wanka tsirara a keBe, a Kitabul Haidh, h 339.

Abin mamaki dogaro da wannan hadisin ya sanya malam Badruddin a sharhin wannan hadisin a Buhari ya kawo wasu bayanai kamar haka:

1- Idan ya zama akwai larura babu laifi a kalli al’aura dogaro da wannan ruwayar.

2- Tasirin sandar Musa (a.s) kan dutse da yin tabo yana daga mu’ujizar musa (a.s) mai girma, kuma ya daki dutsen tare da ya san cewa Dutsen ya yi haka ne da umarnin Allah madaukaki.

Nawawi ma a sharhin Muslim ya kawo cewa wannan hadisin yana da babbar mu’ujiza guda biyu da suka hada da:

1- Gudun da dutsen ya yi da tufafin Musa (a.s).

2- Tabon da dutse ya samu saboda dukan sandar Musa (a.s).

A yanzu saboda Allah kunyata annabin Allah da nuna al’aurarsa a tsakiyar gari mutane su gani ba wulakanta annabin Allah ne ba?!. Musamman ma da ya zama ta hanyar isgili da gudun da dutse yake yi, shi kuwa yana bin sa yana; Kai dutse ba ni Tufafina!.

Kuma tun da ya zama da umarnin Allah ne dutsen ya gudu da tufafin, don me ya sa Musa (a.s) zai yi fushi haka har ya doke shi dukan da zai ji masa ciwo.

Shin gudun da dutse ya yi da tufafin Musa (a.s) zai ba wa Musa (a.s) damar yaye al’aurarsa har cikin kasuwa ko taron jama’a, a nan akwai wani mai hankali da zai yi hakan balle annabin Allah!.

Ina mu’ujiza duk a nan in ban da wulakanci da keta hurumin annabin Allah babu wani dalili!.

Kuma shin domin a kuButar da shi daga sukan Isra’ilawa cewa ba shi da gwaiwa dole ne sai an tozarta shi hakan, ashe bai wadatar ba a yi wahayi a shiryar da su.

Idan Musa (a.s) ya kasance ba shi da lafiya mece ce matsalar da sai an tozarta shi hakan, shin annabawa da suka rigaye shi kamar Ayyub daga nasabar jikan ananbi Ibrahim bai samu rashin lafiya ba, ko kuwa Yakub da ya rigaye shi da kusan shekaru 500 ko sama da haka bai samu ciwon idanuwa da ya kawar masa da ganin sa ba. Don me ya sanya shi Musa (a.s) sai an wulakanta shi don nuna cewa ba shi da gwaiwa, ko kuma rashin lafiyar wata tawaya ce ga annabcinsa?!. Idan dai rashin lafiyar annabawan da suka gabace shi bai zama aibi ba, to me zai sanya nasa ya zama aibi. Ko kuwa wannan ma daga Buhun Abuhuraira ne!?.

Don haka ne zamu ga Imam Ali da dalibinsa ibn Abbas sun tafi kan cewa ayar kuButar da Musa (a.s) tana nuni da tuhumarsa da kashe Harun ne. Ko da yake wasu sun kawo shi a sharrin da Karuna ya so yi masa da wata karuwa, ko kuma jingina masa sihiri da hauka da suka yi[19].

5- Kona Tururuwa

Tururuwa al’umma ce mai ambaton Allah da tsarkake shi da girmama shi, sai dai Abuhuraira ya ruwaito cewa annabi Musa (a.s) ya kona baki dayan wasu tarayyar tururuwa masu yawa saboda ya fusata sakamakon wata daga cikinsu ta cije shi.

Abin mamaki a nan yadda Tirmizi, Kastalani, da Ibn Hajar suka yi nuni da kekashewar zuciyar annabin sakamakon ya kona dubunnan tururuwai saboda daya ta cije shi, da cewa annabi Musa (a.s) ne[20].

Imam Ali wasiyyin annabin rahama (s.a.w) yana rantsewa da Allah cewa: Wallahi da za a ba shi sammai bakwai da kasa da dukkan abin da yake ciki a kan ya kwace wa wata tururuwa wani kwayar alkama da ta dauko da ba zai yi ba[21]. Ba ma Imam Ali da yake daya ga hujjojin Allah a kan mutane ba, hatta da jikansa Sayyid Khomaini Jagoran Juyin Musulunci a Iran wani daga cikin malamai yana nakalto labarin sun je wurinsa da dare, sai wani ya buge sauro da yake damun sa, sai ya yi musu nuni da cewa halittun Allah ne da suke yin tasbihi. A nan ne suka tambaye shi game da kashe sauro ya nuna musu shi dai bai taBa kashe wani kwaro ba, domin duk komai yana tasbihi ga Allah ne. Wannan malamin addini ke nan daga jikokin annabi masu daraja.

Kwatanta wannan halin na malamin addini da na Musa (a.s) dan Imrana a cikin wadannan ruwayoyi. Idan mai hankali zai yi hukunci waye ya fi kamala a cikinsu. Haka nan ne aka suranta annabawa da siffofi masu muni a cikin ruwayoyi masu yawan gaske da suka zo a sahihaini Buhari da Muslim, a yanzu zamu kare kimar littafin ne ko kuwa kimar annabawa mu yarda da cewa akwai hadisai masu yawa da ba su da inganci a cikin wadannan littattafai mu hutar da kanmu daga tozarta addinin Allah da muzanta annabawansa!.

Babbar matsalar tana koma wa ga musulmi ne da suka ki riko da abin da Umar ya yi musu nuni na rashin karBar hadisan Abuhuraira. Umar bn khaddab ya hango wannan hatsarin don haka ya yi masa bulala a kan ruwaya, ya hana shi ruwaya, amma bayan wafatin Umar da Boyuwar bulalarsa a bayan kasa sai Abuhuraira ya koma wa ruwayoyi, ya kuma yi wa umayyawa hidimar da babu wani wanda ya yi musu da ruwayoyinsa. Abin mamaki kamar yadda Aburayya yake kawowa sai ma musulmi suka yi kunnen uwar shegu da maganar Halifa Umar kansa suka kira shi da mai ruwayar Musulunci[22].

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] HAJJI: 75.

[2] AN’AM: 124.

[3] An’am : 90.

[4] Shu’ara: 217 – 218.

[5] Tabari: j 22, s 5.

[6] Biharul Anwar: j 15, s 361.

[7] Tabaqat Kubra: Ibn Sa’ad; j 1.

[8] Tauba: 128.

[9] Aali Imran: 159.

[10] Ahzab: 53.

[11] Masnad Ali: j 1, s 99, daga Masnad Ahmad bn Hambal. Da wasu littattafai masu yawa da suka naqalto wannan ruwayar.

[12] Taurat: Sufuri Takwin; Asihah 19, faqara 30 – 38.

[13] Taurat: Samwel na biyu, Asihah 11 – 12.

[14] Injilar Matta: Asihah 1.

[15] Injilar Yohana: babi 2.

[16] Injilar Luka: babi 7, da Injilar Matta: babi 11.

[17] Nahjul balaga: Ibn Abil Hadid; j 11, s 38, h 203. Salim bn Qais: s 104.

[18] Sufuri Takwin, Asih’hah 12, faqara 11 – 16.

[19] Sharhin Badruddin a Umdatul Qari: j 15, s 302.

[20] Buhari ya kawo shi a Kitabul Jihad, j 4, b 50, h 2856. Sai kuma Muslim a j 8, kitabu qatlil hayyat, h 2241.

[21] Nahjul balaga; 224.

[22] Shaihul Mudhira: s 90.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *