Yankin Larabawa Kafin Annabi

SHIMFIDA DA GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya k’ara tabbata ga bayinsa wad’anda ya zaba

Kuma lalle hakika kana da ladar da ba ta yankewa. Kuma lalle hakika kana kan halayen kirki manya[1].

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Daga Allah ne muke neman taimako muna gode masa a cikin kowane hali muke na farin ciki da bakin ciki, kuma muna gode masa a kan rahamarsa da sakon da ya aiko annabawa da shi, musamman annabin karshe Muhammad (s.a.w) Dan Abdullah (a.s) Dan Abdulmudallib (a.s) tsira da amincin Allah su tabbata ga alayensa tsarkaka. Wanda shi ne aka aiko da kur’ani domin ya fitar da mu daga duhu zuwa haske, ya tseratar da mu daga bata, ya canja mana mafi munin al’adu da shiriya zuwa tafarki madaidaici. Sai muka bi shi muna masu mika wuya, muka yi koyi da shi, ya zama mana abin koyi kyakkyawa.

Saudayawa idan marubuta zasu yi rubutu game da tarihin rayuwar wani mutun sananne mai daraja da muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam, sukan fifita bincike game da bangaren rayuwarsa ta ilimi da kyawawan dabi’unsa daidai gwargwadon bukatun su da suke hankoron cim musu ta hanyar bincike game da wannan mutum, sai dai mu a wannan makala zamu yi bincike game da sirar mafi girman mutum, mafificin halitta, mafi tsarkin samammu, shi ne cikamakoin annabawa da manzanni da Kur’ani ya siffanta shi da cewa:

“Ba ya magana da son rai, sai dai shi wahayi ne da aka yi masa shi”[2].

Da fadinsa: “Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai”[3].

Ya umarce mu da mu rike shi abin koyi, yana mai fadin: “Lallai kuna da abin koyi kyakkyawa ga manzo”[4].

Manufar da ake son kai wa gareta ita ce; sanin Annabi Muhammad (s.a.w) domin mu dauki darussa da abin la’akari mu kuma yi koyi da shi, mu lizimci abin da ya zo da shi da umarni, mu koyi sadaukarwa saboda muusulunci daga gareshi, kuma kada mu yi gezau ko rauni gaban abubuwa masu rudarwa, sai ya zama mana alami kuma jagora mafi daukaka a wannan rayuwa.

Zamu yi kokarin yin bincike game da sirar Annabi (s.a.w) da suka hada da bincike game da sanin Annabi (s.a.w) da haihuwarsa, da tijararsa, da bishararsa, da annabta, da matansa, da wahayin manzanci, da kira a boye da fili, da hijirar Annabi, da yakokinsa, zuwa bude Makka da hajjin bankwana, da halifan Annabi (s.a.w) zuwa wafatinsa.

Muna rokon Allah ya sanya mu daga wadanda suka kari musulmi wajan sanin wani abu daga tarihin annabinmu, domin ya zama mana haske kuma ya karbi wannan dan kadan daga ayyukanmu ya yi mana gafara, domin shi ne mai karbar tuban muminai. Kuma ina rokonsa ya bayar da ladan ga wanda aka rubuta makalar game da shi (s.a.w) musamman da aka ambaci wannan shekarar da sunansa. Kuma muna rokon Allah madaukaki ya hada kan musulmi gaba daya musamman da gabatowar makon hadin kai.

JAZIRAR LARABAWA KAFIN MUSULUNCI

Idan muna son fahimtar musulunci da sanin girman annabin rahama mai shiryarwa Muhammad (s.a.w) Wanda da ikon Allah ya iya tseratar da dan Adam, ya sanya shi a kan tafarkin cigaba da daidaituwa a ayyuka, yana mai farawa da wadanda suke gefensa na larabawa. To yana kanmu da farko mu san wane hali ne larabawa suka kasance kafin musulunci domin mu san yanayin da, daga nan ne da’awa zuwa ga musulunci ta fara, daga cikin mafi kyawun magana a kan wannan al’amari ita ce maganar Sayyid Allama Tiba’tiba’i (K.S) da yake cewa:

“Hakika wannan kur’ani yana ambaton lokacin zamanin larabawa da yake tukewa har zuwa bayyyanar musulunci a lokacin jahiliyya, ba komai ba ne sai nuni daga gareshi zuwa cewa; abinda yake hukunci a cikinsu a wannan zamani shi ne jahilci ba ilimi ba, kuma abin da ya mamaye su a cikin kowane al’amari nasu ba komai ba ne sai barna ba gaskiya ba[5], sun kasance a kan hakan kamar yadda kur’ani ya ke ba mu labarinsu yana mai cewa: “Suna tsammani ga Allah abin da yake ba gaskiya ba zato na jahiliyya suna masu cewa shin mu na da wani makami na wani abu”. Ali imran: 154.

Ubangiji madaukaki ya ce: “Shin hukuncin jahliyya suke so waye yafi kyautata hunkunci fiye da Allah ga mutane masu yakini”. Al-ma’ida: 50.

Ya ce: “Yayin da wadanda suka kafirta suka sanya gaba a zuciyarsu irin gaban nan ta jahiliyya, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa a kan manzonsa da kuma a kan muminai ya kuma lizimta musu kalmar takawa, kuma da man sun kasance su ne mafi cancanta da ita kuma su ne ma’abotanta, kuma Allah ya kasance masani da kowane abu”. Al-fath:26.

Ya ce: “Ku tabbata a gidajenku kada ku yi fita irin fitar jahiliyya ta farko, ku tsayar da salla, ku bayar da zakka, ku bi Allah da manzonsa”. Ahzab: 33.

Wannan ayoyi su ne mafificin madubi da yake nuna halin da larabawa da yanayinsu ya kasance, al’ummar larabawa musamman yankin hijaz ba ta da wata wayewa, kuma babu wani abu na wayewa da cigaba da ya rage a cikinta kafin bayyanar musulunci, kuma ga al’adu iri-iri da koyi da iyaye da ya yadu a cikinta da mafi shahararsu su ne:

Shirka da Allah a ibada, ta hanyar bauta ga gumaka da taurari.

Musun tashin kiyama, wato komawar mutum zuwa rayuwa a wata duniyar bayan mutuwarsa.

Yaduwar surkulle da kauce wa tafarki madaidaci da camfi, abubuwan da suke dakushe hankulan mutane, wadannan al’adu ne da suka yi karfi a suka kafu a cikinsu, kuma suka kasance dalili mai karfi na ci bayansu, kuma suka zama hani mai karfi a tafarkin cigaban da’war musulunci daga baya, abin da ya sanya Annabi (s.a.w) yake aiki da dukkan karfinsa da kokarinsa wajan kawar da wadannan al’adu na jahiliyya, da gurbatattun akidu.

Fasadi da lalacewar dabi’a, kamar yaduwar caca, da giya, da zina, da luwadi, da karuwanci.

Binne ‘ya’ya mata, wannan wata al’adace mai muni da kur’ani ya yi magana game da ita a matsayin laifi mai muni da ba zai bari haka nan ba a lahira ba tare da ya yi hisabi a kai ba.

Ya ce: “Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka yana mai bakin ciki, yana boye kansa daga mutane daga munin aibin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne a wulakance ko kuma ya turbude shi a turbaya, hakika abin da suke hukumtawa ya munana”. Nahal: 58-59.

Ya ce: “Idan wacce aka binne ta aka tambaye ta. Da wane laifi ne aka kashe ta”. Takwir: 8-9.

Saboda haka ne mace ta zama an haramta mata dukkan hakkokin zamantakewar al’umma har da gado, namiji ya zama yana auren matar babansa idan ya sake ta ko bayan wafatinsa, da yawa daga ‘ya’ya suka yi fasin-fasin da matar babansu daya bayan daya, kamar yadda namiji yake gadon matar dan’uwansa idan ya mutu ya bar ta tamkar yadda yake gadon kayan gida, hada da cewa su ba sa ba wa ‘ya’ya mata gado kamar yadda suke ba wa ‘ya’ya maza.

Shan jini, da cin mushe, da cin naman alade, da cin naman sauran dabbobi da suke kashewa ta hanyar rashin tausayi.

Cin riba, wannan kuma yana zaman kashin bayan cinikayya a tattalin arzikinsu.

Kwace da karfi, kwace abin da yake hannun mutane da kai hari, da kisa, da kashewa, yana daga al’adu masu karfi a wajansu, har ma ya zama yana daga abubuwan alfahari gun maza.

Amma a janibin ilimi da wayewa, mutanen hijaz sun siffantu da rashin iya rubutu da karatu, wadanda suka san karatu da rubutu a Makka gaba dayanta adadinsu bai wuce mutane goma sha bakwai ba daga kuraishawa kafin zuwan musulunci.

Daga cikin munanan al’adunsu a wancan zamani akwai abin da Ja’afar Dan Abi Talib (a.s) ya fada yayin da ya yi huduba a gaban Najashi sarkin Habasha yana mai cewa: “Ya kai sarki! Mu mun kasane mutane ne na jahiliyya, muna bauta wa gumaka, muna cin mushe, muna zo wa alfasha, muna yanke zumunci, muna munana wa makwabci, mai karfi a cikinmu yana cin mai rauni, mun kasance a haka…”[6]. Wannan ita ce hakikar larabawa kafin musulunci.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

www.haidarcenter.com

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

hfazah@yahoo.com – hfazah@hotmail.com

10 Rabi’ul awwal 1427

20 Parbardin 1385

9 Afrilu 2006

 

[1] Surar Kalam: 3 – 4.

[2] Najmi: 3 – 4.

[3] Anbiya: 107.

[4] Ahzab: 21.

[5] – Tafsirul mizan: 4/151.

[6] – Majma’azzawa’id: 6/26.

Check Also

57-Aqidun Shi’a

  Akidojin shi’a sanannu ne da su ne dai akidojin musulmi na asali da aka …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *