Ahlul-Baiti A Sikelin Buhari da Muslim

Falaloli masu yawa ne suka zo game da alayen annabin tsira tun daga littafin Buhari da Muslim zuwa sauran litattafai, Buhari da waninsa sun kawo wasu lamurran tarihi masu yawan muhimmanci, muna iya duba wasu daga ciki kamar haka:

Ali dan Abutalib

A falalar Imam Ali ya kawo falalar yabon sa da Allah ya yi kan yakin Badar[1]. Da ruwaya mai cewa: Duk wanda ba ya son sa to munafuki ne, sai kiyayya da shi ta zama alamar munafunci, kuma duk wani musulmi ko mai darajarsa a idanuwan wasu mutane idan aka tabbatar da ba ya kaunar Imam Ali to tabbas munafuki ne[2].

Sannan saboda an canja sallar da annabi ya zo da ita an jirkita ta, sai bayan Imam Ali ya hau halifanci a yayin da ya yi salla a Basara a lokacin ne ya tuna wa sahabbai yadda ananbi (s.a.w) yake salla, har sai da Umran bn Hasin ya yi furuci da hakan[3].

Sannan sai falalar ambaton Imam Ali da annabin rahama ya yi ya ba shi alkunyar suna Abu Turab[4]. Na’am a cikin wannan falalar da aka kawo akwai wasu maganganu da ba nan ne mahallin tattauna su ba.

Sannan ya kawo falalar Imam Ali ta ilimi a kan kowane sahabi, sai ya zama a cikin al’ummar manzon Allah (s.a.w) babu wani wanda ya kai Ali sanin hukunce-hukunce Allah, da ma kowane fage na ilimi[5].

Sannan akwai falalar cewa Imam Ali shi ne yake son Allah da manzo kuma Allah da manzon suke son sa[6]. Sai ya kasance a cikin wannan al’ummar shi kadai ne ya samu wannan shedar gun annabin rahama (s.a.w) kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslim da wasunsu. Kuma sahabbai da yawa sun yi burin samun wannan matsayin da aka keBanci Imam Ali da shi.

Sannan sun kawo falalar Imam Ali da matsayinsa a cikin wannan al’ummar da cewa: Kamar yadda annabi Harun (a.s) yake a cikin al’ummar annabi Musa (a.s) haka nan Imam Ali (a.s) yake a cikin al’ummar annabin rahama (s.a.w) sai dai babu annabin bayan manzon Allah (s.a.w) don haka Ali ba annabi ba ne, sai dai wasiyyi ne[7].

Wannan matsayin da yake da shi manzon Allah (s.a.w) ya maimaita shi ga al’umma a lokuta masu yawa, sai dai wasu masu karancin ilimi sai suka dauka ya keBanta da lokacin da ya bar shi jiran gari a yakin tabuka ne.

Duk wani matsayi da Kur’ani ya ba wa Harun na dangantaka tsakaninsa da shi da Musa (a.s) to Ali yana da wannan matsayin dangantarkar da annabi (s.a.w). Kamar yadda Harun (a.s) yake waziri[8] dan’uwa[9], halifa[10], wasiyyi[11], mataimaki da Allah ya karfafi lamarin annabi Musa da shi kuma mai tarayya cikin lamarinsa[12], haka nan Ali ya kasance game da annabin daraja Almustafa (s.a.w).

Sayyida Zahara

Hakan sun ruwaito wasu falaloli na sayyida Zahra (a.s) ‘yar annabin karshe mai rahama da tausayi (s.a.w) da cewa: Ita ce mafi darajar matan talikai baki daya[13]. Da wannan ne zai bayyana cewa Allah bai halicci wata mace da ta kai ta daraja da daukaka wurinsa ba, kuma duk wani matsayi da wata mata take da shi yana kasan matsayinta.

Sai falalarta na cewa ita ce farkon wacce zata hadu da shi bayan wafatinsa[14]. Kuma ita ce tsokar jikin annabi, kuma duk wani hukunci da ya ke ya shafi annabi (s.a.w) to ya shafe ta. Duk wanda ya fusata ta to ya fusata annabi ne, wanda kuwa ya faranta mata rai ya faranta wa annabi rai, wanda ya cutar da ita to ya cutar da annabi[15].

Wannan ruwayar kawai ta isa ta nuna mana cewa; kamar yadda annabi yake ma’aunin gaskiya, to bayansa ma’aunin gaskiya ita ce Fatima (a.s), sai a duba duk wani abu da ba ta so to Allah ba ya sonsa, kuma duk wani abu da ta ki to Allah yana kinsa. Haka nan yardarta da fushinta da wani abu yana nuna yardar Allah ko fushinsa ga wannan abin. Kamar yadda shi kansa Buhari ya kawo.

Bayan Buhari ya kawo cewa Allah yana fushi da fushinta, yana yarda da yardarta, sai wani abu da ya kawo game da ita da halifofin farko cewa:

Buhari da Muslim sun kawo cewar Abubakar da Umar sun zo duba sayyida Zahra (a.s) a lokacin ba ta da lafiya, sai ta shaida musu wannan lamarin na cewa Allah yana yarda da yardarta kuma yana fushi da fushinta. Bayan sun ba ta amsa da cewa haka ne. Sai ta shelanta cewa tana fushi da su kuma ba ta yarda da su ba. Buhari da Muslim duka sun shaida cewa ba ta yarda da su ba, ta yi fushi da su, kuma ba ta sake yi musu magana ba har ta rasu[16].

Sannan malaman sunna a litattafansu sun ruwaito cewar ta yi wasici da ka da su halarci sallarta. Wannan ne ma ya sanya imam Ali (a.s) da ‘ya’yansa suka yi mata salla da dare suka Boye kabarinta har yau babu wanda ya san inda yake.

Daga cikin falalar sayyida Zahra (a.s) akwai ba ta Tasbihi da zamu ga a yau duk al’ummar musulmi suna yin sa bayan salla, da farko suna yin kabbara 34, hamdala 33, sai tasbihi 33[17]. An ba ta wannan maimakon samun ‘yar aiki da zata taya ta yin aikin gida, sai ta yarda da hakan lamarin da ya zama albarka da lada ga duk al’umma baki daya.

Sayyida Zahra (a.s) ta kasance mace mai hikima da jarumta irin ta babanta da babarta, ta kasance ita ce wacce ta dauke wa annabin kamala mahaifar da aka dora masa yayin da ya yi sujada a ka’aba[18]. Sannan ta kasance tana halartar yaki tana taimaka wa babanta da mijinta jagorantar yakar mahara da suka kawo wa daular Musulunci hari.

Tarihi ya kawo mana isa matukar da take da shi wurin hikima yayin da Imam Ali mijinta yakasance yana zuba ruwa a fuskar annabin Allah (s.a.w) ita kuwa tana wanke wa annabi ciwon da aka ji masa na rotsa fuskarsa da futar da hakorinsa da fasa masa kansa, sai dai amma jini ya ki tsayawa, sai sayyida Zahra ta kona wata tabarma ta sanya tokar kan ciwon nan take sai jini ya tsaya kuma ciwon ya kame[19].

Sayyida Zahra ta kasance wacce ta fi kowa bakin ciki mai tsanani da wafatin ananbin rahama (s.a.w) ba don kawai yana babanta ba, sai don kasancewarsa hanyar samun kamalar halittu zuwa ga Allah madaukaki, kariya ne shi daga duk wani Bata, malamin kowane mutum, mahallin saukar wahayin Allah madaukaki[20].

Hasan da Husain

Hasan da Husain (a.s) amincin Allah ya tabbata gare su sun kasance jikokin annabin rahama (s.a.w), kuma annabin rahama (s.a.w) ya ambace su da wadannan sunayen ne don ya kammala matsayin Ali gun sa cikin kamanci a kowane abu, don haka sai ya ambace su da sunan ‘ya’yan Harun (a.s) wasiyyin annabi Musa (a.s).

Manzon Allah (s.a.w) yana son su fiye da kowane mutum bayan ‘yarsa, kuma ya shelanta wa duniya cewa su ne shugabannin samarin aljanna, kuma su ne sanyin idanuwansa da kanshinsa a wannan duniya, kuma su jagorori ne kan kowane mutum a zamaninsu sun tsaya ne ko sun zauna (sun yi yaki ko kuwa, sun riki halifanci ko kuwa).

Batun son su a gun annabi (s.a.w) da matsayinsu gun sa, da kamanninsu da shi a halaye da halitta, da girman darajarsu gun Allah da halittunsa, wani abu ne da kowane mutum malami da waninsa suka sani, don haka ba ya bukatar dogon bayani[21].

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] Buhari: j 5, Babu Qatli AbuJahl. Da: J 6; h 3747, 3750, 3751.

[2] Muslim: j 1, Kitabul Iman; h 78.

[3] Buhari: j 1, kitabus salat, Itmamut Takbir fir Ruku. Muslim: j 2, kitabus salat, babu Isbatit Takbir fi kulli Khafrin wa Raf’in.

[4] Buhari: j 4, kitabu manaqib Ali…, da babu naumur rajul fil masjid…, da j 4, kitabul adab; babut Takanni bi Abi turab. Muslim: j 7, babu fadha’ili Ali.

[5] Buhari: j 6, kitabut Tafsir, h 4211. Ibn Majah: j 1. Isti’ab; j 1, s 8.

[6] Buhari: j 4, kitabul jihad; babu ma’qila fi liwa’in Nabi, h 2812. Da J 4, h 2847. Da Hadisi; 2783, 3498, 3499, babu gazwatu Khaibar; h 3972, 3973. Muslim: j 7, kitabu fadha’ilu Ali, h 2405, da h 1807.

[7] Buhari: j 4, babu gazwatu Khaibar: h 4154, Kitabu bad’il Khalq, manaqibu Ali, h 3503. Muslim; j 7, falalar Ali, h 2404.

[8] Taha: 30.

[9] Taha: 31.

[10] A’araf: 142.

[11] Taha: 30 -36.

[12] Taha: 36.

[13] Buhari: j 4, kitabul manaqib; b 22, h 3426, da j 8, kitabul isti’izan, b 43, h 5928. Muslim: j 7, kitabul fadha’ilus sahaba, b 15, fadha’ilu Fatima, h 2449, 245.

[14] Buhari: j 4, kitabul manaqib; b 22, h 3426. Da: J 5, h 3511. Da: J 4, kitabul magazi, babu maradhin Nabi; h 4170. Muslim: j 7, kitabul fadha’ilus sahaba, b 15, fadha’ilu Fatima, h 2450.

[15] Buhari: J 5, kitabul fadha’ilus sahaba, babu manaqibu qarabatir Rasul; h 3510. Da: b 16, h 3532. Muslim: j 7, kitabul fadha’ilus sahaba, b 15, fadha’ilu Fatima, h 2450.

[16] Buhari: 4/96. Buhari: 8/185. Muslim: 3/1380/ H 1759.

[17] Buhari: h 4, kitabul Khums, h 2945. Da: j 5, falalar Ali, 3502. Da: j 7, kitabun Nafaqat; b 6, h 5046. Muslim: j 8, h 7272.

[18] Buhari: j 1, kitabul wudhu’; h 69. Muslim: j 5, babu ma laqiyan nabiyyi mi azal mushrikin; h 1794.

[19] Buhari: kitabul wuhdu’; bab gaslil mar’ati abaha an damin an wajhin; h 230. Buhari: Fadhlul Jihad; h 2753. Muslim: gazwatul Uhud; h 1790.

[20] Buhari: j 6, babu mardhin Nabi wa wafatihi.

[21] Buhari: j 5, h 3542, 3543. Buhari; j 8, h 5648, 5651. Da: j 3, b 24, h 3543. Manad Ahmad: j 2, s 269. Muslim: j 7, h 2421.

Check Also

45-Hajjin Tamattu’i 3

  Hajjin tamattu’i shi ne bangare na biyu da yake farawa daga ranar Arafa har …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *