Halifanci A Sikelin Buhari Da Muslim

Halifanci bayan wucewar ma’aikin Allah shi ne mafi muhimmancin bahasin da duniyar musulmi ta fuskanta wanda ya jawo rabewarta gida biyu har yanzu, kuma babu wani abu da ya sabbabba kisan mutane da ribace su da tozarta su fiye da wannan mas’ala[1]. Tare da cewa al’ummar musulmi ta yi imani da cewa babu wasu mutane da suka fi alayen manzon Allah (s.a.w) daraja sakamakon dasa wannan dashen da annabin rahama da kansa ya yi a zukatan al’ummar, kuma Allah ya tsarkake su a littafinsa ya wajabta yi musu salati tare da annabinsa a cikin littafinsa da ruwayoyin da suka zo daga annabinsa (s.a.w).

Sai dai a halifancin annabin rahama da maye gurbinsa a jagorancin al’umma a nan al’umma ta yi watsi da alayen annabin rahama (s.a.w) duk da kuwa nassosi masu yawa da suka zo kan hakan wanda babu wani mai inkarin hakan sai wanda ya samu makancewar basira. Imam Ali (a.s) yana kawo wannan mas’ala a wurare masu yawan gaske: “… a cikinsu ne hakkin jagoranci yake, kuma wasiyya da gado nasu ne…”[2].

Sannan babu wata mas’ala komai kuwa karancinta da rashin muhimmancinta da Allah da manzonsa ba su fadi hukunci kanta ba, hatta da abin da ya shafi maganin cututtukan mutane[3], sai dai idan bai zo hannunmu ba. Sai dai mas’alar halifanci bayan manzon Allah (s.a.w) ce ‘yan Sunna suka tafi a kan cewa ita kam manzon Allah (s.a.w) bai yi wasiyya ga wani ba, wannan lamarin kamar yadda marubuta da yawa suka kawo yana da bam mamaki domin ba komai ba ne sai jingina rashin muhimmantar da lamarin Allah da na al’umma ga fiyayyen halitta alhalin ya barranta daga irin wannan mummunar sifa.

Manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni ga al’umma da ka da mutum ya kwana ba tare da wasiyyarsa tana tare da shi ba[4]. Wannan kan lamarin duniya ke nan, yaya kuwa zata yiwu ya bar duniya ya bar lamarin al’umma sakakai babu wata makoma da ya jingina su da zasu koma mata wacce zata jiBinci lamarin al’umma bayansa. Maimakon mutanen su dora laifin kauce wa wasiyyar annabi (s.a.w) kan al’umma da ta ki biyayya ga umarninsa sai ta kirkiro abubuwa na rashin hankali ta jingina wa annabin rahama (s.a.w).

Sai ya zama ko da yaushe manzon Allah (s.a.w) ya ba wa al’umma umarni ba ta yi aiki da shi ba, sai a kore umarnin da ta bayar, idan kuwa ya yi hani sai al’umma ta ki bin haninsa a nan ma sai a samu wani tawilin da aka bayar ko kuma a kirkiro karya a jingina masa cewa ai shi ma ya hana. Da haka ne sai aka yi ta kirkiro matsayi ga wasu mutane don samar musu da mafita da uzuri amma fa abin takaici sai wannan ya kasance ta hanyar rushe kima da darajar annabin kansa.

Sai ya kasance kamar yadda al’ummar annabi Musa (a.s) ta yi wurgi da wasiyyarsa ta nesanci Yusha’ (a.s) ta yi wurgi da shi, kuma al’ummar annabi Isa (a.s) ta yi watsi da wasiyyarsa ta yi wurgi da Sham’unus Safa (a.s) ta yi riko da waninsa, haka ma al’ummar annabin rahama (s.a.w) bayan wafatinsa ta yi watsi da wurgi da wasiyyinsa Imam Ali (a.s) ta riki waninsa.

Sannan zaluncin da al’ummar manzon Allah (s.a.w) ta yi masa ya fi na wanda aka yi wa wadancan annabawan, domin bayansu al’ummarsu sun yi furuci da kuskure ne aka yi sai dai suna yi masa tawili, amma manzon rahama (s.a.w) shi kai tsaye ne al’ummar ta rubuta cewa bai ma yi wasiyyar ba, sai ta jingina masa wannan rashin hankali da tunani. Ina ma dai ta tafi a kan cewa kuskure ne da mabiyansa suka yi bayansa, suka nema musu gafara a kan hakan, amma sai ya zama gwara kare mutuncin mabiyansa da mutuncinsa kamar yadda suka saba yin haka a kowane lamari da ya shafi annabi da wani daga mabiyansa musamman idan ya hada da wani daga manyan sahabbansa!.

Yaya hankali zai yarda cewa duk da Kur’ani mai girma da annabin rahama (s.a.w) sun yawaita karfafa mas’alar wasiyya hatta kan lamarin duniya don kawar da duk wani rashin fahimta da wata rigima kan lamarin mamaci bayan wucewarsa, sai kuma da lokacin da annabin rahama (s.a.w) mai yawaita karfafa wannan lamarin ya zo rasuwa shi sai ya yi shiru ya ki yi wa al’umma da alayensa kowace irin wasiyya. Idan aka sanya wannan a gaban mai hankali wanda bai san waye annabin rahama (s.a.w) wane irin hukunci masu wancan lalataccen garBataccen tunani suke tsammani zai yi ga annabin rahama.

Yaya kuwa zai kasance annabin rahama (s.a.w) ya yi wasiyya kan wanke shi da binne shi da biyan basussukansa ga Imam Ali daga abubuwan da suke kanana mas’aloli sai kuma ya kasance bai yi wa al’ummarsa wasiyyar komai ba game da matsayinta bayansa! Wane irin hukunci kuke yi wa fiyayen halittun Allah (s.w.t)?!.

Sannan idan muka koma wa ruwayoyin da suka zo kan cewa halifofinsa goma sha biyu ne bayansa da dukkan al’umma ta yi ittifaki kan hakan, su ma muna da tambaya a kan cewa: Shin zai yiwu ya fada wa al’umma cewa halifofinsa goma sha biyu ne bayansa sannan sai ya yi shiru ya ki gaya wa al’umma su waye, don ya bar wadanda suka fi shi hikima bayansa (wal’iyazu bil-Lah) irin su Baihaki da Suyuti su zo bayansa don su gaya wa mutane su waye!.

Tare da sanin cewa ita ce mas’alar da ta fi kowacce muhimmanci a rayuwar al’ummar musulmi amma sai ya yi gum bai yi wa kowa bayanin su waye wadannan halifofin nasa ba don a al’ummarsa akwai irinsu Baihaki da Suyuti da suka fi shi sanin ya kamata (wal’iyazu bil-Lah) da zasu zo su gaya wa al’umma su waye wadannan halifofin.

Da wani mutum zai kaurace wa kowa da komai na wannan duniya a kan wannan jahilci da rashin hankali da ka jingina wa annabin kamala, ya kulle dakinsa ya yi kwana da kwanaki yana kuka dare da rana, babu ci babu sha har mutuwarsa! Da na kasance cikin mutanen farko da zasu girmama matsayinsa!.

Sai dai manzon Allah (s.a.w) tun farkon sakonsa ranar da aka yi masa umarni da gargadin makusantansa a gida ya fada musu wasiyyinsa wazirinsa halifansa bayansa Ali, kuma ya gaya musu matsayinsa da shi kamar Harun ne gurin Musa, ya gaya musu ya bar musu littafin Allah da alayensa bayansa, kuma tsawon sakonsa shekaru 23 yana karfafa wannan lamarin, sai dai siyasa ce da ta yi halinta!.

FALALAR ALAYEN ANNABI

Idan muka duba falalar alayen manzon Allah (s.a.w) a Muslim zamu ga ya kawo ruwayar Ayar Tsarki da ta sauka ga alayen manzon Allah masu tsarki da daraja yayin da ya sanya su cikin bargo, wannan aya ce da take nuni ga tsarkinsu daga duk wata daudar saBo da zunubi, kuma tana daga cikin babban dalilin kariyarsu daga dukkan saBo da siffantuwarsu da Isma[5].

Lamarin Mubahal

Kuma zamu ga sun ruwaito falalarsu kan mubahala da Imam Ridha (a.s) ya yi nuni da cewa ita ce mafi girman ayar da take nuni da fifikon Imam Ali kan kowane mahaluki bayan annabin rahama (s.a.w). Muslim ya kawo wannan a cikin ruwayar nan da Sa’adu bn Abi Wakkas ya ki la’antar Imam Ali yayin da Mu’awiya ya yi masa umarni da hakan, sai ya kawo falalolinsa da suka hada da; 1.Matayin Ali gun annabi kamar matsayin Harun ne gun Musa. 2.Siffanta Imam Ali (a.s) da cewa Yana son Allah da manzonsa kuma Allah da manzonsa suna son sa a yakin Khaibar. 3.Sai kuma batun kasancewarsa ainihin rai din Annabin rahama sai dai shi ba annabi ba ne, kamar yadda ya zo a ayar Mubahala[6].

Hadisin Gadir

Haka nan Muslim ya kawo hadisin Gadir da wasiyyar da annabi (s.a.w) ya yi wa al’ummarsa da alayensa bayansa, sai dai masu ilimi sun tabbatar da tashin warin jirkitarwa a wannan ruwayar, domin ruwayar tana nuni da cewa “… na bar muku nauyayan alkawura biyu a kanku, na farko shi ne littafin Allah…”, amma bayan ya kawo na biyun a fadin annabi “… da alayena..” sai da ya kawo wata fakara cewa “… ina hada ku da Allah game da alayena har sau uku …”, kamar dai an yi wasiyya da kiyaye su ne ba da biyayya gare su ba. Maimakon nuni da cewa an yi wasiyyar biyayya gare su, sai ya kawo cewa an yi wasiyyar kiyaye su.

Da ya bar kalmar “… da alayena …” kai tsaye abin fahimta shi ne littafin Allah da alayena su ne na bari hujja da nauyi a kanku, amma kawo jumlar “… ina hada ku da Allah game da alayena har sau uku …” tana nuna wa mai karatu kamar dai an yi wasiyya da kula da su ka dare hakkinsu ne kawai, ba wasiyya da biyayya gare su ba.

Sai dai wannan karin da ya zo bayan kalmar “… da alayena …” ba zai iya tabbatar da kasancewarsu hujja kan dukkan al’umma bayansa ba. Wannan kuwa ya zama haka ne domin tun farkon ruwayar ya kawo cewa: “… na bar muku nauyayan alkawura biyu a kanku, na farko shi ne littafin Allah…”, sannan bayan nuni da riko da littafin Allah kai tsaye sai ya zo da jumlar “… da alayena …”[7].

Abin tambaya a nan don me ya sa ba su kawo mas’alar taron ba dalla-dalla kamar yadda sauran masu ruwaya na Sunna suka yi. Masu ruwayoyi sun kawo taron wurin nan na Gadir da abin da ya faru, da hudubar annabi, da kalmomin da ya yi amfani da su, da bai’ar da aka yi wa Imam Ali, da taya shi murna da Abubakar da Umar da sauran sahabbai suka yi.

Sannan me ya sa a farkon ruwayar aka kawo wata mukaddima daga Zaid dan Arkam yana cewa: Ya manta da wasu abubuwan da annabi (s.a.w) ya fada?! Me ya sa duk sa’adda wani abu ya shafi wasiyyar annabi (s.a.w) ga al’umma ko dai ka samu an hana shi rubutawa a wani wuri ana jifarsa da sumbatu bai san me yake cewa ba! (wal’iyazu bil-Lahi!), ko kuma a farkon ruwayar sai an yi nuni da mai ruwaitowa ya ce: Ya manta da wani abu daga ciki!? Ko kuma mai ruwaya bai ji wani Bangare daga ciki ba?!. A lamari mai muhimmanci da girma irin wannan da makomar al’umma shiriyarta ko Bacewarta yake dogara da ita, don me bai koma wa wani daga cikin sahabbai ba don tunawa don ya isar da sakon annabin Allah (s.a.w) kamar yadda ya ji shi?!.

Sannan sai kuma jirkita manufar annabi ta hanyar fadada ma’anar Ahlul-baiti ta yadda zai yi daidai da Banu Abudlmutallib wanda ya saBa da hadisai masu yawan gaske mutawatirai da manzon Allah (s.a.w) ya bayyana alayensa a fili. A yanzu zai Buya ga Muslim ya kasa bambance ma’anar Ahlul-baiti da ma’anar luga da ma’anarta ta Istilahin shari’a ba?! Idan kuma ya bambance su ta hanyar fitar da matan annabi daga cikinsu, shin kuma a yanzu zai Buya gare shi cewa sun keBanta da wasu mutane ne ayyanannu ba duk Banu Abdulmutallib ba?!. Ko kuwa zai yiwu wadancan hadisan na Bargo da ya kawo su da kansa a wasu wurare musamman a Ayar Tsarki su ma sun Buya gare shi ne!?.

Sannan don me ba su kawo mafi muhimmancin yankin wannan hudubar ta annabi ba a fadinsa: “… wanda duk na kasance jagoransa to Ali ma jagoransa ne …”.?

Allah ya saka wa Hakim da alherinsa yayin da ya ga ba su kawo wannan Bangaren mafi muhimmanci ba sai ya kawo shi cikin littafinsa Mustadrak da yake kawo ruwayoyin da bisa dokar Buhari da Muslim sun inganta amma su ba su kawo su ba[8].

Halifofi Sha Biyu Ne

Idan kuma muka duba hadisin halifofi bayan manzon Allah (s.a.w) cewa goma sha biyu ne da duk masu ruwayar al’umma Sunna da Shi’a suka yi ittifaki kansa, sai mu ga an so taBa shi da jirkita shi ta hanyar taBa karshensa. Mai ruwaya yana cewa: Na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Zai kasance a kanku akwai jagora goma sha biyu, sai ya fadi wata kalma da ban ji ba, sai na tambayi babana, sai ya ce: Ya ce ne: Dukkansu daga Kuraishawa ne”[9].

Hadisin ya zo da sigogi daban-daban wani ya ambace su da halifofi, wani kuma jagorori, wani sarakuna, sai dai manufa daya ce da al’umma ta yi ittifaki a kanta cewa yana nuni da halifofin annabi (s.a.w) bayansa. Kuma zasu kasance har karshen zamani, kuma annabi Isa (a.s) zai yi salla bayan na karshensu[10].

A farkon wannan fasalin mun kawo bayanai da suka shafi wannan ruwayar yayin da muka yi nuni da maganar wasu daga malaman Sunna kan cewa annabi bai ayyana wasiyyansa halifofinsa ba, suna gafala da ko sane da cewa maganar cin mutunci ne mai girma ga matsayin annabin rahama (s.a.w). Sai irin wadannan malamai sun saba da jingina wa annabi (s.a.w) tawaya ko wace iri ce don kare matsayin wasu sahabbai don kokarin rufe wasu kurakurai da suka yi.

Da annabi (s.a.w) ya ayyana wasu mutane ne daban ba alayensa ba, da lamarin ya zama abin alfahari ga al’umma, kuma da an yi bukukuwa da wannan ranar, da an shelanta lamarin dare da rana. Sai dai annabi (s.a.w) ya ayyana alayensa ne da masu karfi da fada-ajin al’ummarsa ta ke dauke da tsananin gaba da kiyayya da su. Annabin rahama ya ayyana su waye halifofinsa da sunayensu, ya ayyana wa al’umma cewa na farkonsu shi ne Ali na karshensu Mahadi (a.s), kuma ya rage wa al’umma ko ta karBa ko ta watsar. Kasancewar alayensa ne ya ayyana sai wannan lamarin ya sanya Boye wannan lamarin da inkarinsa da da’awar cewa annabin Allah (s.a.w) bai yi wasiyya ba.

Sai masu da’awar annabi bai yi wasiyya ba suka mance da lamarin ruwayar halifofi goma sha biyu ne bayansa, suka gafala cewa sun ruwaito wannan ruwayar, amma sai zukata da kiraza suka makance da soyayyar masu gaba da alayen annabin Allah wadanda suka rasan hasken kaunar alayensa, sai suka fada cikin karo da juna a maganarsu.

Wasu daga cikin malaman makarantar Sunna sun wuce matakin cewa annabi bai yi wasiyya ba ma, sai kuma suka koma neman bayar da matsayin wasiyya ga wasu jama’a daban ba alayen manzon rahama ba. Wato suna son nuni da cewa idan ma annabi (s.a.w) ya yi wasiyya to ya yi wa wasu mutane ne daban ba Ahlul-baiti ba.

A kokarin haka ne suka duba sai suka ga farkon wanda ya yi halifanci shi ne Abubakar, don haka sai suka yi riko da duk wani abu mai rauni da mafi yawancinsa hatta a makarantar Sunna bai inganta ba, hada da cewa ya ci karo da juna da tarihin Musulunci da hadisai mutawatirai, don dai kawai su yi nuni da cewa akwai wata wasiyya a fakaice ga Abubakar. Sun manta cewa Abubakar ko wani daga cikin manyan sahabbai bai taBa nuni da wadannan lamurran da suke kawo ba.

Da an samu wani ko mai karancinsa kuma ko da shi ne mafi kankanta da zai taimaka wa halifan musulmi Abubakar ko mai rauninsa, da ya yi riko da shi. Da an samu wani abu ko da ba ya nuni da halifanci kamar yin limancin salla, ko biyan bashin annabi bayansa, ko alkawarin kyauta ga wasu mutane, da halifan musulmi Abubakar ya kafa hujja da shi a sakifa yayin jayayya kan jagoran bayan annabi da ma bayan sakifa a lokacin halifancinsa.

Sai dai wadanda suke kirkiro irin wadannan ruwayoyin don su kare kurakuran magabata sun zalunci Abubakar da Umar da sauran sahabbai da da’awar karya da suke jingina musu da sunan nema musu matsayi da falala da su ba su taBa da’awar ta ba. Sun kuma zalunci kansu da hasarar duniyarsu da lahirarsu da jingina wa annabin Allah karya da sunansa, da kuma tauye darajojinsa da kaskantar da shi don kawai gyara wani kuskure na magabata.

Idan mun duba adadin halifofin annabin tsira da aminci zamu ga babu wata mazhaba a duniya baki daya Shi’a ce ko Sunna da ta yi daidai kan wannan lamarin sai shi’awan Ahlul-baiti (a.s) kawai da aka fi sani da Shi’a imamiyya isna ashariyya. Amma sauran mazhabobi hatta masu amsa sunan shi’anci kamar “Zaidiyya” da “Isma’iliyya” ba su da wadannan halifofin goma sha biyu. Da wannan lamarin ne zamu kai ga natijar cewa a duk fadin duniya babu wani mazhabin musulmi da ya dace da wannan wasiyyar ta annabi (s.a.w) mai riko da littafin Allah da alayensa sha biyu sai mazhabar Shi’a da aka fi sani da Ja’afariyya ko Isna Ashariyya.

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] Almilal wan Nihal: fasali 5, muqaddima 4, s 14.

[2] Nahjul balaga: Ibn Abil Hadid; Huxuba 2, j 1, s 138.

[3] Kitabut tib: Timizi, da Muslim: Hadisi 2217; manzon Allah ya sanar da wani sahabi maganin gudawa.

[4] Buhari: Kitabul wasaya; j 5, h 2587. Muslim: j 5, kitabul wasiyya. Abu Dawud, Nisa’i, Ibn Majah, da Masnad duk sun kawo shi.

[5] Muslim: j 7, kitabu fadha’ilus sahaba; babu fadha’ilu ahlil bait, h 2424.

[6] Muslim: j 7, kitabu fadha’ilus sahaba; babu fadha’ilu ahlil bait, s 257. Da kuma babu fadha’ilu Ali, h 2404 – 2407.

[7] Muslim: j 7, kitabu fadha’ilus sahaba; babu fadha’ilu Ali, h 2408 .

[8] Hakim: Mustdarak; j 3, s 533. Masnad Ahmad: J 4, s 372.

[9] Muslim: J 6, kitabul imara; b 1, h 1821. Da kibatul fitan: j 8, h 2913 – 2914.

[10] Muslim: Kibatul fitan: j 8, h 2913 – 2914. Buhari: Kitabul Anbiya, babu nuzuli Isabni Maryam, h 3265.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *