Dacewar Halifofi A Sikeli

Ayar Hijabi

Idan mun duba misalan dacewar halifa ga wahayi da suka kawo zamu ga suna da yawa, sai dai zamu iya kawo wasu misalai kana hakan. Ayar hijabi tana daga cikin abin da suka jingina wa halifan kansa.

Ruwayar Farko

Karo da juna a hadisan dalilan saukar ayar hijabi kawai yana sanya raunin wannan maganar. A ruwayar A’isha ya zo cewa tana cin abinci ne tare da annabi a kwano daya, sai Umar ya zo wucewa sai annabi ya yi masa tayi, sai ya sa hannu tare da su yana ci, sai hannunsa ya ci karo da na A’isha. Sai ya ce: Da an bi tawa ne da wani ido na ajnabi da bai taBa ganin ku ba. Sai aka saukar da ayar hijabi[1].

Ruwaya ta Biyu

A wata ruwayar kuwa ta zo cewa ne matan annabi suna fita ban daki gefen gari ne don yin bayan gida, sai a wani dare Umar ya zauna kan hanyar da suke wucewa, Saude ta kasance doguwa ce sosai, sai ta fito don yin bukatarta da dare, sai Umar ya duba sai kuma ya ga Saude, sai ya ce: Ke Saude! Na gane ki! Kuma ya yi haka ne ba don cutar da ita ba, sai dai don ya takura wa matan kawai don a saukar da ayar Hijabi. Sai kuwa ayar hijabi ta sauka[2].

Ruwaya ta Uku

Tambaya a nan ita ce: Yaushe ne wannan ayar ta hijabi ta sauka? Shin lokacin da yake gaya wa annabi ne cewa tun da mutane suna shiga gidansa don haka ya kange matansa ne? ko kuma lokacin da yake cin abinci da shi matar annabi har hannunsa ya ci karo da dan yatsanta? Ko kuwa lokacin da yake zama kan hanyar da matan annabi (s.a.w) suke wucewa yin bayan gida don takura su, har ya ce wa Saude: Na gane ku?!. saboda a saukar da ayar!?.

Ruwaya ta Hudu

Sai dai akwai ruwayar da ta ci karo da duk wadanann ruwayoyin kuma ta fi kusa da dacewa da ayar Kur’ani kan hijabi, ita ce ruwayar Anas dan Malik da yake cewa: Ya kasance wata rana an yi amarci a gidan annabi sai sahabbai suka ci abinci, bayan nan sai suka zauna suna hira, ga ananbi yana nuni da su fita amma babu wani wanda ya kula, sai daga baya wasu suka fita, haka nan dai ya yi ta jira har sai da sauran suka fita, yayin da kowa ya fita sai ya dawo cikin gida, ni kuwa sai na biyo shi a baya sai ya sanya labule tsakanina da shi. A wannan lokacin ne aka saukar da ayar hijabi[3].

Wanda ya koma wa ayar hijabi zai ga ta fi kusa da wannan lamarin domin tana hana shiga gidan annabi, sannan tana hana zama bayan an ci abinci a gidan.

Salla ga Munafukai

Batun salla da dan Abdullahi dan Ubayyu ya nema kuma manzon Allah ya amsa masa wani abu ne shahararre. Ya nemi manzon Allah (s.a.w) ya ba shi rigarsa don ta zama wa babansa likkafani, kuma annabin rahama ya gaya masa bayan wanke shi ya sanar da shi.

Yayin da annabi ya zo salla Umar dan Khaddabi yana cewa: Sai na sha gabansa na gaya masa abubuwan da dan Ubayyu ya yi, amma ya ki, sai da ya ga na dage sai ya yi murmushi ya ce: Ni an ba ni zaBi ne. Har dai inda ruwaya take cewa: Ba su dade da dawowa daga yi masa salla ba sai aka saukar da ayar hana yin salla ga munafukai[4].

Wannan ruwayar ta rasa inganci saboda wasu dalilai da suka hada da cewa: Babu yadda wani mutum zai fi annabin Allah sanin maslahar da take cikin hukuncin shari’a. Na biyu: ayar ta sauka a shekara 8 hijira lokacin safarar yakin Tabuka, alhalin shi kuma ibn Ubayyu ya rasu a shekara ta 9 hijira[5].

Sannan maimakon ta kasance falala ga Umar zata zama suka da aibi ne gare shi, domin shi da kansa yana cewa a karshen ruwayar: Na yi mamakin shisshige wa annabin Allah da tsageranci da na yi a wannan ranar, alhalin Allah da manzonsa su ne mafi sani.

Sannan matanin ruwayar ya saBa da abin da ya kunsa, domin Umar yana cewa ne: Yaya zaka yi masa salla alhalin Allah ya hane ka yi wa munafukai salla. Don haka ne sai malamai suka shiga warware wannan matsalar da cewa: Ai ayar tana nufin zaBi ne domin fadin Allah “… duk daya ne shin ka nema musu gafara ko ba ka nema musu ba…” sai dai ko kusa abin da ayar take fada ba ya nuna zaBi.

Kurtabi yana cewa: Ta yiwu ko ilhama ce aka yi wa Umar tun kafin lokacin haramcin. Wato Allah ya jefa wa Umar haramcin ta hanyar ilhama kafin ayar Kur’ani ta saukar da shi, sai Umar ya furta shi[6].

Sannan batun cewa annabin rahama (s.a.w) yana son kari ne bisa saba’in shi ma kaskantar da darajarsa ce, domin saba’in a wannan ayar ba adadi ba ne, kowane mai fasaha ya san yana nufin yawa ne. Kuma manzon Allah (s.a.w) ya barranta da kasancewa kasa da matsayin fahimtar masu fasahar lugogi.

Don haka ne daga cikin malaman Sunna alkali Bakilani yake cewa: Wannan hadisin bai inganta ba, ba zamu iya karBar abin da ya kunsa ba mu ce: Manzon Allah (s.a.w) ya fahimci zaBi ne daga wannan ayar[7]. Kuma wannan ne ra’ayin Imamul haramain, Imam Gazali, da Dawudi.

BUHARI da MUSLIM a SIKELI

Bahasin ; Dacewar Halifofi A Sikeli

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

[1] Arriyadhun Nadhira: j 1, s 263. Sharhu Nahjul Balaga: j 12, s 58.

[2] Buhari: j 8, ayar hijab, h 1. Da kuma: j 1, babu khurujun nisa’ ilal baraz, h 5886. Muslim: j 7, babu ibahatul khuruj linnisa’ liqadha’i hajatil insan: j 2170.

[3] Durrul Mansur: j 5, s 213.

[4] Buhari: j 2, kitabul jana’izi, h 1210. Da J 6: Tafsiru suratit Tauba, h 4393. Da j 7: Kitabul libas; h 5460. Muslim: j 7, babu fadha’ilu Umar; h 2400. Da J 8: kitabu sifatil munafiqin wa ahkamihim; h 2774.

[5] Almizan: j 9, s 385.

[6] Fathul bari:L j 8, s 252.

[7] Fathul bari: j 8, s 252, da 355.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *