Siffofin Halifa a Buhari da Muslim

Idan muka duba hudubobi da wasikun Imam Ali (a.s) game da yadda halifan annabi (s.a.w) ya kamata ya kasance zamu ga ya kawo siffofi masu yawa da wajibi ne halifan annabi ya siffantu da su.

Irin wadannan siffofin sun hada kyauta, sani, ilimi, adalci, amana, kyawun hali, taushin zuciya, riko da dokar Allah, hukunci da dokokin Allah, kiyaye Kur’ani da Musulunci da hukuncin shari’arsa.

Sai dai idan muka duba irin wadannan siffofin da suka zo a shari’a zamu ga Buhari da Muslim da ma sauran litattafan Sunna sun kore wa halifofi da yawa daga wannan kamalar, wannan kuma kai tsaye yana nuni da cewa maganar Allah da manzonsa ta cewa a koma wa Kur’ani da alayen annabin Allah da ta zo a littattafan shi’awa da sunnawa ita ce gaskiya, kuma kai tsaye wannan yana nuna cewa halifofin da suka cika wadannan siffofin kamala daga alayen annabin Allah su 12 kamar yadda yake a ra’ayin shari’a kanta da shi’awa suke riko da su, gaskiya tana tare da su.

Ayyukan Halifofi

A nan muna son takaita bayani kan wasu ayyukan halifofi da suka zo daga Buhari da Muslim. Akwai mas’aloli masu yawa da suke nuna barin hukuncin shari’a da ya zo daga halifofi, sai suka yi hukunci da wani abu daban saBanin wanda ya zo daga Allah da manzonsa.

Imam Ali (a.s) yana cewa: Hakika halifofi kafin zuwana sun yi aikin da suka saBa wa manzon Allah (s.a.w) a cikinsa suna yi da gangan don saBa masa, suna masu warware alkawarinsa, masu canja sunnarsa. Kuma da na dora mutane a kan barin abin da suka yi, na sanya komai mahallinsa kamar yadda yake lokacin manzon Allah (s.a.w) da rundunata ta watse ta bar ni har sai na rage ni kadai tare da ‘yan kadan daga shi’ata da suka san falalata (matsyina da darajata) da wajabcin riko da jagorancina a littafin Allah da sunnar manzonsa[1].

Imam Ali ya kai matsayin zama abin tausayi a cikin wannan al’ummar ta yadda ya kai matakin da ya hana mutanen yin jam’in sallar asham amma sai masallatan suka yi ihu baki daya: Wayyo sunnar Umar! Wayyo sunnar Umar!! Ya yi sallar kasaru raka’a biyu rundunarsa ta tashi ta yi sallarta raka’a hudu saboda biyayya ga sunnar Usman da ya hana yin sallar kasaru.

Sa ya kasance a irin wannan yanayin ba shi da wani zaBi sai ya zaBi ko dai ya tsaya ya kare daula daga harin munafukai masu son rusa addini na inganci da sunnar annabi ta gaskiya. Ko kuma ya tsaya yana ta fada da mutanen daular yana mayar da su kan sunnar annabi da aka canja kuma mutane ba zasu yarda ba sai dai sunnar Abubakar da Umar kawai, sai ya wahalar da kansa kan abin da ba zai iya cimma sa ba ke nan, don haka ne ya zaBi hanyar farko da zata zama mai amfani fiye da ta biyun, domin ya kare abin da ya rage na addini!.

Imam Ali ya so ya gama da yakar munafukai ya karfafi daula don ya hada karfin ikonsa, sannan sai ya canja wadannan dokokin ya dawo da na annbin Allah (s.a.w). Amma kafin ya kai ga wancan matakin sai ya kasance munafukan cikin rundunarsa sun hada kai da munafukan da suke yakar sa aka kashe shi.

Zamu ga Imam Ali yana cewa kan wannan lamarin: Da karfina ya kafu sosai, da na canja wadannan lamurran duka[2].

Idan ya kasa canja sallar asham, ko sallar kasaru, yaya ake tsammanin kuma ya kwace mata daga wadanda suka aure su ya mayar da su hannun mazajensu! Ya kwace dukiyoyi ya mayar da su baitul-mali ko hannun masu su na asali! Da sauran hukunce-hukunce masu yawa da hadarin gaske da ya ambata a wata huduba tasa!.

Siffofin Halifofi

Ba ya daga cikin siffofin Jagoran al’umma ya kasance mai kekasar zuciya da kausasa wa al’umma da rashin hakuri da karancin ladabi. Idan muka duba muka koma wa ma’aunan da Allah da manzonsa da wasiyyansu suka kawo game da siffofin wanda ya kamata ya jagoranci al’umma, to zamu ga a bisa ruwayoyin Buhari da Muslim kansu babu wani wanda ya cancanci siffofin kamala da ya kamata halifa ya siffantu da su kamar imam Ali (a.s), da yawa ma zamu ga wasu ma an rasa su ga wasu halifofin kai tsaye.

1. Karancin Ladabi

Buhari ya kawo jayayyar halifofi biyu a gaban manzon Allah (s.a.w) har sautukansu suka daga murya da karfi da jayayya, kowannen yana gaya wa manzon Allah (s.a.w) ga wanda zai sanya a matsayin jagoran Banu Tamim. Sai aya ta sauka tana haramta daga wa annabi sauti da murya, da kuma bayanin shafe ayyukan alheri baki daya ga wanda ya aikata hakan[3].

Kuma ko ba komai wannan shiga ne gaban annabin rahama da bai dace da halin mai ladabi gare shi ba. ZaBar wanda yake dacewa da wakilcin al’umma wani lamari ne da yake hannun jagoran musulmi ma’asumi annabi wanda komai yake yi bisa wahayi ne don haka bai kamaci musulmi su rigaye shi ba.

Wannan lamarin da ya faru a shekara ta tara bayan hijira yana nuna mana cewa duk da halifofi sun zauna kusan shekara 20 tare da annabin rahama (s.a.w) amma har ya zama sauran watanni kusan kasa da shekara ya yi wafati amma ba sa kiyaye ladabin zaman majalisinsa, suna fada da jayayya a gabansa, suna sukan juna alhalin yana zaune ba tare da sun kiyaye hurumin samuwarsa ba!.

A yanzu Buhari da sauran malamai sun yarda su fifita wanda yake fusata annabi da jayayya a gabansa da shafe ayyukansa na alheri da yin wadannan ayyukan, sai su fifita shi a kan wanda yake Allah da manzonsa suke son sa, yake son Allah da manzonsa a bisa ingantattun ruwayoyin da suka kawo?!.

2- Kekasar Zuciya

Imam Ali yana kawowa a hudubarsa cewa: Ka da shugaba ya kasance mai jafa’i (zafin rai da kekashewar zuciya) in ba haka ba, zai yanke al’umma da jafa’insa[4]. Buhari da waninsa na daga masu ruwaya da tarihi sun siffanta halifa na biyu da cewa shi mai kausasa wa muminai ne, ya kasance suna siffanta shi da mai tsanani (mai azaba) kan muminai.

Ya kasance mata[5] da maza[6] suna tsoronsa matukar gaske bayan ya samu madafan iko a hannunsa, kuma tun lokacin annabin rahama (s.a.w) ya kasance yana takura musu amma annabin Allah yana taka masa burki.

Ta kai matukar tsoron al’umma ga halifa abin da yake nuna maka hakan yayin da aka tambayi Abdullah dan Abbas da ya kasance ya yi shiru kan maganar “Aulu” da ya saBa wa ra’ayin halifa cewa me ya sa bai bayyana ra’ayinsa ba lokacin rayuwar halifa? Sai ya ke cewa: Ina jin tsoronsa ne, domin jagora ne mai ban tsoro mai firgitarwa[7].

Ya ishe ka zane Ummu Farwata ‘yar Abu Kuhafa ‘yar’uwar Abubakar da ya yi yana mai shiga gidanta ba da izininta ba don kawai ta yi kukan mutuwar dan’uwanta Abubakar[8], sai ya shiga gidanta kai tsaye ya fara zane ta tare da sauran matan da suka taru duk da kuwa ranar ce aka yi musu mutuwar, ga kuma yawan shekarunsu amma duk da haka hatta da huruminsu bai kiyaye ba, sai zafin bulala ne ya sanya su watsewa da gudu suna masu tserewa da kafafuwansu.

3. Jahiltar Shari’a

Amma idan muka duba maganar Imam Ali kan cewa “… ka da jagora ya kasance jahili sai ya Batar da al’umma da jahilcinsa”[9], sai mu leka mu ga mene ne Buhari da Muslim da waninsu suka siffanta halifofi da shi. Imam Ali ya koka da wannan lamarin matukar gaske yayin da yake kawo mummunan halin da aka fada yana mai cewa:

Ana kawo wa daya daga cikinsu wani lamarin hukunci sai ya yi hukunci da ra’ayinsa sannan sai a sake kawo wannan lamarin kansa ga waninsa sai ya yi hukunci da saBanin maganarsa, sannan sai masu hukuncin su taru gun jagoran da ya nada su sai ya zartar ra’ayoyinsu. Alhalin ubangijinsu daya, annabinsu daya, littafinsu daya. Wai shin Allah ya umarce su da yin saBani ne sai suka bi shi, ko kuwa Allah ya saukar da addininsa tauyayye ne sai ya nemi taimakonsu don cika shi, ko kuwa sun kasance masu tarayya da shi don haka suna da ikon su yi magana shi kuma ya yarda. Ko kuwa Allah ya saukar da addininsa cikakke ne sai manzon Allah ya takaita wurin isar da shi da aiwatar da shi. Alhalin Allah madaukaki yana cewa: “… ba abin da muka bari a littafi, …” a cikinsa akwai bayanin komai…”[10].

Tabbas wadannan kalmomi na sarkin muminai suna da dukan zuciya da muhimmanci ga wanda ya kasance yana da hankali da tunani da basira. Wannan ne lamarin da al’umma ta fada cikinsa tun lokacin kafin halifancinsa sai sakamakon hakan ya kai mu ga fadawa halin da muke a yau, sai addini ya koma Bata da Barna, mai riko da shi ya zama bare a cikin al’umma. Sai dai Allah muna godiya gare ka da ka bayyanar da shiriya a littafinka da kare mana ruwayoyin wasiyyan annabinka ta yadda mai son komawa turbar annabinka zai samu kofar yin hakan a bude take.

a- Hukuncin Taimama

Buhari da waninsa sun kawo abubuwa masu yawan gaske da halifofi suka jahilta na daga lamuran da bai kamata ba ga matsayin halifa ya jahilce su domin lamura ne da mutanen da suke rayuwa ba tare da halartar makarantu ba suka san su.

Duk musulmi ya san cewa idan ya rasa ruwan wanka to zai yi taimama ne, kuma halifan musulmi yana daga cikin wadanda manzon Allah (s.a.w) ya yi bayanin hakan, amma ba mu san me ya sanya halifa jahiltar hakan ba, kuma ba mu san me ya sa ya tsananta wa wanda ya yi riko da hakan ba.

Kuma maimakon a samu karBar hakan daga Ammar sai ya kasance ya fuskanci magana daga Halifa mai ban tsoro da ta sanya shi dole ya juya kan ra’ayinsa yana mai cewa: Idan Halifa ya ga babu maslaha kan hakan to zan janye maganta. Domin kalmar Halifa gare shi cewa “ka da ka yi salla” ko “ka ji tsoron Allah” wannan yana nuna rashin yardarsa da maganar Ammar, kuma saBa wa hakan yana nufin saukar masa da wata ukuba ke nan.

Wannan tsoron yana bayyana a cikin maganar Shakik da tambayar da Abu Musa Al’ashari ya yi wa Ibn Mas’ud kan wannan mas’alar, amma sai Ibn Mas’ud ya wadatu da ba shi amsa cewa: Ai Halifa bai karBi maganar Ammar ba. Da Abu Musa ya nuna cewa ai akwai ayar Kur’ani mai nuni da yin taimama karara a fili, sai Ibn Mas’ud ya yi shiru bai kara kalma daya ba. Domin ko dai ya yi magana saBanin ra’ayin halifa sai ya samu ukuba mai tsanani gun sa kamar yadda waninsa ya samu, ko kuma ya fadi ra’ayin Halifa sai ya samu fushin Allah da azabarsa, tare da sanin cewa idan akwai cutuwa to Allah ya yarda ka Boye gaskiyar lamari (Takiyya) kamar yadda Ammar ya yi da mutanen Makka suka azabtar da shi, don haka ne sai Ibn Mas’ud ya zaBi yin shiru.

Mummunan Tawili

Babu abin da ya fi takaici maimakon ma’abota ilimi su nuna kuskure ne da rashin sani daga Halifa, sai suka dora wata Barna da tafi munin Barnar farko.

Ibn Hajar yana cewa: Wannan lamarin yana nuni da cewa sahabbai suna yin ijtihadi a zamanin annabi (s.a.w)!. Yana mai cewa: Rashin yin salla ga wanda ya rasa ruwan wanka wani ra’ayi ne da ya shahara gun Umar. Sai dai wannan lamarin yana nuna cewa sahabbai suna yin ijtihadi a lokacin annabi (s.a.w) ma.

Shi kuwa Ibn Rushd malamin Fikihu da Falsafa yana cewa ne: Malamai sun yi imanin cewa wajibi ne a yi taimama ga mai janaba saboda hadisin Ammar da Umran dan Hasin da Buhari ya nakalto, kuma mantuwar da Umar ya yi ta yin aiki da hadisin Ammar ba ta da wani tasiri. Sai ya yi ishara da cewa Halifa ya yi mantuwa ne, alhalin halifa bai yi nuni da hakan ba[11].

b- Haddin Giya

Haddin shan giya bulala 80 ne, haka nan manzon Allah (s.a.w) ya aiwatar sai dai halifa ya yi 40 ne. Sai dai yayin da halifa na biyu ya zo sai ya ga shan giya ya yawaita sakamakon an samu budin dauloli mutane sun fara tara mata suna komawa rayuwar jin dadi, sai da yawa tunanin shan giya ya dawo musu.

Sakamkon shan giya ya fara yawaita ne halifa ya nemi shawarar sahabbai, sai Imam Ali ya mayar da shi kan sunnar annabi (s.a.w) bulala 80, wasu suna kawo cewa Abdurrahman ne, amma bisa hakika Imam Ali ne ya dawo da shi kan wannan turbar domin shi ne aka yi ittifaki a kansa[12].

c-Diyyar Jariri

Daga cikin abubuwan da Buhari da Muslim suka kawo na daga jahiltar halifofi ga shari’a, kuma wani lokaci har da jan kunne da gargadi ga wanda ya saBa musu ko ya tunatar da su kan saBa wa sunnar annabi. Wani lokaci kuwa lamarin yana zama bisa sharawa ne sai halifa ya zaBa.

Diyyar Jariri da halifa ya jahilta har sai da Mugira da Muhammad bn Maslama suka ba shi shawara[13]. Buhari da Muslim sun kawo wannan daga cikin hukunce-hukuncen da halifa ya nemi shawara a kai kuma ya yi aiki da maganar Mugira tare da cewa ya san halayensa amma sai ya dogara da shi.

Sakamakon irin wannan ne maimakon marubuta masana su yi furuci da gazawar halifa a ilmance, sai suka shiga ba wa lamarin tawili. Wasu ma sun karfafi wannan suna masu dora shi kan sikelin cewa: “Lamarinsu shawara ne tsakaninsu”, kai kace lamarin Allah lamarin mutane ne.

Idan lamari ya kasance na mutane to wannan yana bukatar shawara tsakaninsu, amma lamarin Allah madaukaki ba ya bukatar shawararsu, abin da yake bukata shi ne sallamawa da mika wuya ga umarnin Allah da manzonsa kawai, kuma idan ba a sani ba to sai a tambaya a nemi sani ba neman shawara ba, wannan ita ce koyarwar littafin Allah da sunnar ananbinsa da babu wani mai saBani a kai.

d-Izinin Shiga Gida

Hukuncin neman izinin shiga gida da sallama sau uku, da koma wa ga wanda ya ji ba a amsa masa ba, kuma saboda Abu Musa ya yi aiki da Sunna a wannan mahallin sai ya fuskanci tsanani wurin Halifa Umar har sai lamarin ruwayar ya inganta gun sa. Sai dai bayan warware matsalar wacce da yawan sahabbai suka taru kan hakan sai halifa ya yi furuci da cewa: Shagaltuwa da cinikayya kasuwa ne ya hana shi sanin hukunce-hukuncen shari’a[14].

Neman tozarta Abu Musa kan lamari da ake tsammanin kowa ya san shi da Halifa ya yi bai yi masa dadi ba, ta yadda ya shigo a fusace har sai da Abu Sa’id ya tambaye shi dalilin kasancewa cikin wannan halin, sai ya ba shi labarin lamarin da ya wakana na wulakanci da Halifa ya yi masa.

Kuma su ma sahabbai da suka ga lamarin bai cancanci kulawa ba don haka ne suka nuna masa yaro (Abdullah bn Abbas) daga cikinsu suka nemi ya tambaye shi, sai kuwa yaro ya bayar da amsa. Sai ya zama babu wani uzuri da halifa ya bayar sai kasancewar shagaltuwa da kasuwanci ne ya hana shi sanin hukunce-hukuncen shari’a[15].

e-Lamarin Kalala

Daga cikin abubuwan da Buhari da Muslim suka kawo na daga rashin sanin Halifa ga shari’a akwai mas’alar “Kalala” ita mas’ala ce da Halifa ya yi furuci da cewa bai tambayi manzon Allah (s.a.w) wani abu ba irin yadda ya tambaye shi ma’anar “Kalala” sai dai bai iya rikewa ba, kuma har sai da wata rana manzon Allah (s.a.w) ya sanya danyatsansa ya soki kirjinsa, amma duk da haka dai bai rike ba.

Kuma matukar manzon Allah (s.a.w) yana ba wa Halifa amsa kan wannan mas’ala duk sa’adda ya tambaye shi me ya sa Halifa ba ya iya rikewa? Ko kuwa lamarin yana da matsalar da Halifa ba zai iya rikewa ba. Kuma me ye hikimar fadin Halifa cewa: Idan na rayu zan yi hukunci da “Kalala” hukuncin da mai karanta Kur’ani da wanda ba ya karanta Kur’ani zai yi!. Shin bayan hukuncin Kur’ani akwai wani kuma dandano na ra’ayin kai da ya rage ga wani mutum?![16].

f-Jefe Mahaukaciya

Daga cikin abubuwan da Buhari da Muslim suka kawo na daga rashin sanin halifofi ga shari’a akwai batun jefe mahaukaciya, sai dai Allah madaukaki ya cece ta da samuwar Imam Ali a hanyar jefe ta, sai ya dawo da mutanen ya gaya wa Halifa cewa Allah ya dauke alkalami daga mutane uku: Mahaukaci, Yaro da Mai bacci.

Masu tarihi suna kawo wannan mahallin a cikin daya daga wuraren da Umar dan Khaddabi yake cewa: “Ba don Ali ba da Umar ya halaka”. Kuma a Buhari ya cire farkon lamarin sai dai kawai ya kawo karshe yana cewa: Ali ya ce da Umar ba ka san cewa an dauke alkalmi daga mahaukaci ba har sai ya warke, da yaro har sai ya balaga, da mai barci har sai ya farka[17].

g-Karatun Sallar Idi

Daga cikin abubuwan da Buhari da Muslim suka kawo na daga rashin sanin halifofi ga shari’a akwai rashin sanin surar da manzon Allah (s.a.w) ya ke karanta wa a sallar idi har sai da ya aika gidan Abu Wakid Allaisi don a tambaye shi wace sura annabi ya ke karantawa a idi.

A yanzu zai iya yiwuwa uzurin da irin Suyudi yake bayarwa kan hakan cewa halifa yana shagaltuwa da kasuwanci ne shi ya sa bai san shari’a ba, ko da yake wani lokaci halifan ne da kansa ya kawo wannan uzurin.

Sai dai batun idi da ba ya faruwa sai a shekara sau daya bai kamata ya zama daga cikin abin da halifa zai manta ba ko wani ya yi da’awar shagaltuwa da kasuwanci ne ya sanya jahiltar sa ga hakan[18].

h-Ajiyar Cikin Ka’aba

Daga cikin abubuwan da Buhari da Muslim suka kawo na daga rashin sanin hukuncin shari’a daga halifofi daban-daban, akwai batun kin ajiye kowane irin Zinare da Azurfa a cikin Ka’aba[19]. Sai dai da godiyar Allah Imam Ali (a.s) ya sha gaban halifa bai samu aiwatar da hakan ba.

i-Kalmar “Abba”

Da kuma mas’alar nan ta rashin sanin ma’anar “abba” a ayar nan mai cewa: “wa fakihatan wa abba”. Kuma Halifa ya ki ba wa mai tambaya ma’anar kalmar yana mai amsa masa da cewa mu an hana mu Kallafa wa kai zurfafawa[20].

j-Rashin Wankan Janaba

Fatawar cewa: “Idan mutum ya yi jima’i da matarsa amma bai fitar da mani ba, to wanka bai hau kansa ba sai dai ya wanke zakarinsa ya yi alwala ya yi salla”. Wannan fatawa daga Usman bn Affan tana da ban mamaki, domin wannan mas’ala ce da ta shahara tsakanin musulmi cewa Jima’i kawai ya mayar da mutum mai janaba ko da bai fitar da komai ba, kamar yadda fitar da mani ko da ba da jima’i ba shi ma ya mayar da mutum mai janaba.

Abin da ya fi mamaki fiye da komai shi ne cewar da Halifa na uku ya yi: Ya ji wannan daga annabin Allah, daga kuma wasu sahabbai, da cewa Ali ma ya gaya masa haka, haka nan Zaubair, Talha, Ubayyu bn Ka’ab. Alhalin babu wani daga cikinsu da aka taBa jin wata magana mai kama da hakan daga gare shi[21].

 

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] Salim bn Qais: s 162. Raudhatul Kafi: s 15. Biharul Anwar: j 13, s 704. Ihqaqul Haqq: j 1, s 61.

[2] Ibn Abil Hadid; Nahjul balaga: j 19, s 161.

[3] Buhari: j 9; kitabul i’itisam bil-kitab was Sunna, babul iqtida bi af’alin Nabi, h 6872, j 5, babu wafdi bani Tamim, h 3109. Fathul Bari: J 10, s 212. Masnad Ahmad: J 4, s 60.

[4] Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga; j 8, s 263, huxuba 131.

[5] Buhari: j 4, kitabu bad’il Khalq; h 3120, da j 5, manaqibu Umar bn Khaxxab; h 3438, da j 8, kitabul adab, babut tabassum wadh dhihk; h 5735.

[6] Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga; j 6, s 363, huxuba 83.

[7] Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga; j 6, s 363, huxuba 83.

[8] Tabari: J 4, Wafatin Abubakar; Abubuwan da su ka faru a shekara ta 13 H.

[9] Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga; j 8, s 263, huxuba 131.

[10] Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga; j 1, s 288, huxuba 18.

[11] Buhari: J 1, kitabut Tayammum; h 331, 338, 339, 332. Muslim: J 1, Babut Tayammum, h 368. Fathul Bari: J 1, s 46. Bidayatul Mujtahid: j 1, s 65.

[12] Muslim: j 5, kitabul hudu; h 1706. Buhari: j 8, kitabul hudu; 6391, 6393. Bidayatul Mujtahid: j 2, s 444.

[13] Buhari: j 9, kitabud diyyat; h 6509, 6510, kitabul i’itisam; h 6887. Muslim: j 5, kitabud diyyat; h 1689.

[14] Buhari: j 8, kitabul isti’izan; h 5891. Muslim: kitabul aadab: h 2153. Abu Dawud: j 2, b 38, s 637. Nur: 28-29.

[15] Buhari: j 8, kitabul isti’izan; h 5891. Muslim: kitabul aadab: h 2153. Abu Dawud: j 2, b 38, s 637. Nur: 28-29.

[16] Muslim: kitabul fadha’idh; babu mirasul kalala, h 1617. Algadir: j 6, s 130.

[17] Buhari; j 7, kitabut Talaq, babut Talaq fil iglaq wal kurh. Da: j 8, kitabul muharibin, babu la yurjamul majnun wal majnuna. Sunan abu Dawud: j 2, b 16, h 4399, s 402. Ibn Majah: j 2, s 227. Isti’ab: j 3, s 39.

[18]Muslim: j 3, kitabu salatil idain; h 891. Ibn Majah: j 1, h 1282. Algadir: j 6, s 320.

[19] Buhari: kitabul i’itisam bil kitabi was Sunna, h 6847. Da: j 2, kitabul hajj, babu kiswatul ka’aba, h 1517. Ibn Abil Hadid: Nahjul balaga: j 19, s 158-159, huxuba 276, kalimat qisar 270.

[20] Buhari: kitabul i’itisam, babu ma yukrahu min kasratis su’al; h 6863. Fathul baari: j 13, s 229. Umdatul qaari: j 25, s 35. Irshadus saari: j 10, s 311. Da sauran littattafai.

[21]Al’ummu: j 1, kitabut Tahara; s 31. Muslim: kitabul haidh; h 348 – 349. Buhari: j 1, kitabul gusli, babu gasli ma yusibu min farjil mar’a, h 287 – 289. Kibatul wudhu; h 177. Muslim: j 1, kitabul haidh; h 347. Fathul baari: j 1, s 339.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *