Barin Hukuncin Shari’a

Amma idan muka duba mas’alolin da halifofi suka bar aiki da hukuncin shari’a suka yi abin da wasu suka kira ijtihadi ko da kuwa su halifofin ba su ambace shi ijtihadi ba, domin a fili yake cewa wasu abubuwan da suka yi tarihi ya ruwaito musu yin nadama kansa kamar mamayar gidan sayyida Zahra (a.s) da tarihi ya kawo shi cikin abubuwa tara da halifa na farko ya yi nadamar yin su yayin mutuwarsa.

Wani abin kuma halifofi sun shelanta cewa sun san Allah da manzonsa sun yi umarni amma halifa ya haramta, kamar “Hajjin Tamattu’i”, da “Auren Mutu’a”, da fadin “Hayya ala Kharil Amal” a kiran salla. Wannan haramcin ya shahara daga halifa na biyu kuma dukkan musulmi sun ruwaito shi sun yi ittifaki kan shi ne ya haramta wadannan hukunce-hukuncen shari’ar, kuma haramcin ya ci gaba har yanzu a cikin musulmi in ban da na Hajjin Tamattu’i da ya samu tabbata daga baya.

Akwai kuma abin da aka samu saBani tsakanin sahabbai da kansu saboda muninsa kamar kashe Malik bn Nuwaira da Khalid ya yi kuma a lokacin ya kwanta da matarsa, sannan ya zo da ita Madina ya shigo a matsayin gwarzo, har ya cancanci yabo daga halifa na farko yayin da ya kira shi da takobin Allah zararre.

Lamarin ya yi muni da hatta halifa na biyu bai ji dadinsa ba, kuma ya nemi daukar mataki kan Khalid amma wannan bai kara wa Khalid komai ba sai matsayi gurin halifa na farko da sake aika shi wata nahiya ya maimaita irin abin da ya yi a cikin jama’ar Malik bn Nuwaira.

Sai dai dukkan munin yana cikin yin tawilin irin wadannan abubuwan idan sun faru. Mafi muni shi ne kokarin da wasu suke yi na kirkiro wa abin da halifa ya yi ruwaya don su nuna ai da ma annabi ma ya haramta musamman a lamurra irin hana rubuta hadisinsa ko auren mutu’a da makamancinsu. Kuma annabi (s.a.w) ya san da wannan fikira tun lokacinsa don haka ne ya yi alkawarin wutar Allah mai jiran duk wani wanda yake yi masa karya yana jingina masa don kare ra’ayinsa.

Sai kuma lamari biyu da yake biye masa a muni na kokarin nuna ai halifa ma ya yi ijtihadi ne, kuma annabi (s.a.w) yana yin ijtihadi ne a wasu wurare, to wannan shi ne lamarin da zai rusa matsayin annabta, da bude kofar kowa yana iya saBa wa manzon Allah (s.a.w) ya yi wurgi da maganarsa, kuma an samu wasu musulmi da suka yi riko da wannan suka aiwatar da shi suka fassara Kur’ani yadda suka so da da’awar cewa ai annabi ma ra’ayinsa ne ya kawo, kuma yana iya yin kuskure ko ya yi daidai.

Masu wannan salon na kariya ga ijtihadin halifa da fifita shi kan ijtihadin annabi kamar yadda suke rayawa ba su tsaya nan kawai ba sai da suka shiga kirkiron hadisan kariya ga ayyukan halifofi, har sai da suka zake suna kirkiro wasu ruwayoyi masu nuni ga matsayin halifofi na ijtihadi da goyon bayan Allah gare su, da rusa ijtihadin annabi daga Allah da kansa, da rashin ba wa annabi gaskiya, da goyon bayan ijtihadin sahabinsa.

Wannan lamarin kamar yadda muka yi nuni ya rusa sakon Allah baki daya da hadafin aiko annabawa. Kuma ya yi hannun riga da koyarwar Kur’ani da ta yi umarnin biyayya ga annabi a kowane lamari da mika masa wuya mikawa a matsayin sharadin imani. Kuma ta ci karo da Kur’ani yayin da yake gaskata annabin rahama cewa ba ya fadin komai daga son ransa sai dai komai ya kawo to wahayi ne aka yi masa.

Wasu kuwa ba su dauki matakin farko na yi wa annabi (s.a.w) karya ba don kare ra’ayoyin halifofi, kuma ba su dauki manzon Allah a matsayin mujtahidi ba da za a iya saBa masa a ra’ayi. Amma sai suka shiga tawilin duk wani kuskure ko da na ganganci ne da halifofi suka yi, suka tsananta wurin kariya har ta kai su ga wuce gona da iri da shiga cikin maganganu masu karo da juna.

Sai wadannan jama’o’i guda uku suka hadu kan kare duk wani mataki da matsayi da wata daraja ta kowane sahabi ko da kuwa zata rusa annabin Allah da kaskantar da shi da tozarta shi. Kuma ko da kuwa zata rusa sakon Allah da hadafinsa na aiko manzonsa, kuma ko da kuwa zasu ba wa makiyan Allah da manzonsa makamin da zasu iya sukan sa da shi.

Kuma sai irin wannan jama’ar ta dauka cewa duk wani bincike na nuna wa al’umma asalin Musulunci da hakikaninsa kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi, da nuna wa mutane yadda aka gurBata sakon, da kariya ga mutuncin annnabin Allah, da gyara ga shari’ar Allah da sakonsa da ya saukar masa. Sai suka kira mai wannan da sunan mai son fitina mai sukan sahabbai, mai kauce wa salafus salihi da sunaye daban-daban.

Sun manta da cewa Allah madaukaki ba shi da uba ko uwa ko dan’uwa ko da, duk mutane a wurinsa daya ne, yana yi musu ma’auni daya ne, shin a lokacin annabi suka zo ko kuwa a wani zamanin. Shari’arsa kan kowa duk daya ce sahabi ne ko ba sahabi ba babu wani bambanci duk kowa dole ne ya rusuna wa littafin Allah da alayen annabinsa a matsayin makoma bayan manzonsa.

Allah ya riga ya kasa mutane a littafinsa babu ruwansa da sahabi ne ko ba sahabi ba, kowace al’umma akwai mumini mai karfin imani, akwai mumini mai raunin imani, akwai jahili da malami, akwai adali da fasiki, akwai salihi da fajiri, akwai mumini da munafuki, a daya Bangare kuwa akwai wadanda ma ba musulmi ba.

Mumini mumini ne a kowane zamani ya zo, kafiri kafiri ne a kowane zamani ya zo, munafuki munafuki ne a kowane zamani ya zo, salihi salihi ne a kowane zamani ya zo, fajiri fajiri ne a kowane zamani ya zo, adali adali ne a kowane zamani ya zo, faskiki fasiki ne a kowane zamani ya zo, mai karfin imani ko raunin imani ko jahili ko malami duk haka suke a kowane zamani ne kuwa suka zo, a zamanin annabi ne ko waninsa.

Hasali ma na zamanin annabi ya fi muni idan ya kauce hanya kamar yadda wasu ruwayoyi suka nuna domin shi ya ga annabi ya kau ce wa gaskiya. Kamar yadda wanda bai yi zamani da annabi ba idan ya yi kyakkyawa ya fi samun lada saboda bai gan shi ba amma ya kiyaye kamar yadda wata ruwaya ta nuna cewa yana da ladan sahabbai 50[1].

Amma sai idanuwan mutane masu irin wannan salon a bincike mafi yawansu suka makance, sai ya kasance ba sa kallon me aka ce?, me ye ingancinsa?, me ye kimarsa?. Sai ya zama himmarsu waye ya fadi maganar ko da ta saBa wa shari’ar Allah? Tunaninsu ya zama Yaya za a kare mutuncinsa da kimarsa da darajarsa ko da kuwa ta hanyar rusa darajar annabin rahama ne?. Sai al’umma ta fada cikin faganniya da dimuwar da ba zata iya fita daga cikinta ba har sai ranar da ta dawo wa turbar koyarwar ananbin rahama (s.a.w).

Motsin al’ummar musulmi da matsalolin da take fuskanta tun daga na addini da fikira, har zuwa tattalin arziki da rayuwar al’umma duk ta ginu ne kan wannan taskar ruwayoyi da suke hannunmu, kuma matukar taskar ba ta inganta ba to lallai zamu fada cikin daji ba zamu sake iya dawowa kan hanya ba. Kuma hatta da matsalar ta’addanci da ake fama da ita a cikin al’ummar musulmi ta taso ne daga mummunar koyarwa da rashin fahimtar nassin addini da jahiltar yadda za a dabbaka shi a wannan zamanin.

Musulunci yana da hukunce-hukunce masu motsi masu rai don haka yana duba; zamani, mahallin magana, jigon magana, wuri, al’adu. Kuma duk suna tasiri kan nau’in hukuncin shari’a. Hukunci kuma har ila yau yana iya kasancewa taklifi ko wadh’i, yana zama; maulawi, irshadi, wila’i, yana zama; auwali, thanawi, yana zama muhkam ko matashabihi, yana zama muwakkat ko da’imi, yana zama ya ta’allaka da wani sharadi ne ko bai ta’allaka da shi ba, da sauran lamurra masu yawa da ba mu kawo su ba. Kuma duk wani abu da zai zama yana da tasiri wurin fitar da hukunci sai an yi la’akari da shi, in ba haka ba to babu yadda za a samu wata natija mai kyau.

Muna iya fadadawa mu ce: Sau tari mutane mabambanta suna tambayar ma’asumi mas’ala daya amma sai ya ba su amsa ba iri daya ba saboda daya ba ya iya fahimta abin da dayan yake iya fahimta. Ko kuma sharadin da wani yake kansa ba shi ne wani yake kansa ba. Ko wani makiyi ne wani kuwa masoyi ne. Ko wani yana matsayin ilimi babba wani kuwa jahili ne. Wata mas’alar shari’a tana da nata istilahin da ta kawo ba ta bar shi kan fassarar luga ba kamar ma’anar Ahlul-baiti (a.s). Wasu abubuwan kuwa suna komawa kan abin da muka yi nuni da su a sama na dokokin fitar da fatawa da suka dogara a kansu.

Misali daya daga misalai masu yawa da za a iya kawowa kamar da wani malami mujtahidi ya yi tambaya game da wanke kafa ko shafawa, kuma wani jahili ya yi tambaya kan wannan mas’alar, a nan zamu ga tun da fuskar tambaya ta saBa haka ma ya zama dole ne fuskar amsa ta bambanta. Domin mujtahidi za a kawo masa dalilan wanke kafa da na shafar kafa, sannan sai a kawo dalilan rinjayar da shafa kan wankewa bisa hujjoji, amma jahili za a ba shi fatawa ne kawai kan shafar kafa.

Wasu ruwayoyin suna da alaka da zamani, kamar wanda ya ga Imam Ali ba ya rina gashinsa alhalin ya san manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da hakan. Sai Imam Ali ya gaya masa ai an yi umarni da rina shi ne a wancan lokacin saboda ka da kafirai su ga mafi yawan musulmai da furfura sai wannan ya kara musu karfin neman cin nasara kan musulmai su samu karfafuwa da hakan, don haka ne duk da musulmai suna da masu furfura da yawa amma sai suka bayyana kamar samari suka yi wa kafirai kwarjini a Badar.

Ko kuma wanda ya gaya wa Imam Ali (a.s) cewa manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da ka da a ajiye naman layya, ya yi umarnin raba shi ga duk mutane. Sai Imam Ali (a.s)  ya ba shi amsa kan cewa wannan ma ya kasance ne saboda ana cikin fari da yunwa a wannan zamanin, amma yanzu mutum yan da zaBin ya yi sadaka da wani ya ajiye saura don kansa da iyalansa.

Ke nan sanin cewa fagen shari’a yana bukatar koma wa wanda aka saukar wa shari’ar don ya yi wa al’umma bayanin sakon da take kunshe da shi wani lamari ne na tilas.

Da kowane mutum daga wannan al’ummar ya koma wa wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ta biyayya ga littafin Allah da alayensa bayan rasuwar manzon Allah (s.a.w) da ba a samu wata tangarda ko mummunar fahimtar addini ba.

Wanda ya isa ya bugi kirji cewa duk abin da yake hannunsa daga Allah da manzonsa ne su ne Ahlul-baiti (a.s) kawai, amma waninsu ba shi da wani garanti kan abin da yake hannunsa. Imam Ali ya yi nuni da cewa: Abin da yake hannun mutane cakude ne tsakanin; 1.Karyar da aka yi wa annabin rahama. 2.Rashin fahimtar abin da manzon Allah ya fada. 3.Hukuncin da aka shafe. 4.Gaskiyar da ta zo daga annabin rahama. Amma su Ahlul-baiti kashi na 4 ne kawai a hannunsu.

Hada da cewa akwai al’adun larabawa da suka yi tasiri cikin abubuwa masu yawan gaske musamman hukunce-hukuncen da suka shafi zamantakewar al’umma da aka sanya su a matsayin koyarwar addini. Sai wasu mutane suka dauka shi ma yana daga addini alhalin ya keBanta da al’adun larabawa ne.

RUFEWA

Dan’uwana mai karatu ya hau kanka ka san hakikanin sakon annabin Allah kamar yadda ya zo ba jirwaye. Kuma babu wani garanti kan abin da yake hannun wani mutum sai wanda Allah da manzonsa suka yi nuni da shi daga alayen annabin rahama su goma sha biyu (a.s).

Abin da ya wakana na tarihin al’ummar musulmi da ya kai ga samar da madogarar da mafi yawan al’ummar musulmi suke jingina da su na litattafai masu dauke da tauye daraja da kaskanci ga annabawan Allah da suka zo mana da shiriya da annabin tsira wanda shari’arsa ce ta karshe, lamari ne mai dacin gaske.

Hanyar samun shiriya da rabautar duniya da lahira ta zo mana ta hannun jakadun Allah ne wacce take kunshe da kyakkyawan sanin Allah madaukaki mai hikima da daukaka, da sanin sakon da ya aiko mana da shi, da darajar annabawansa da wasiyyansu da ya yi mana baiwarsu. Idan kuwa aka rusa wannan koyarwar, aka toshe hanyar sanin Allah, aka jirkita matsayin jakadun Allah da wasiyyansu, to babu wani abu da zai rage da inganci a addinin Ubangiji. Kuma wannan yana nufin toshe wa dan’adam mafi kyawun hanyar samun kamalarsa ta duniya da lahira.

Babu wata mafita ga duniyar musulmi sai sake duba inda take samun tunaninta da fikirarta domin auna shi a sikelin hukuncin hankali mai yakini da littafin Allah mai tsarki domin tantance bara-gurbi da nagari. Wannan hanyar ce da manzon Allah da alayensa (a.s) suka gindaya wa al’ummar musulmi wacce matukar ba a dawo kan turbarta ba to ba abin da zai kara wa al’ummar musulmi sai nesantar hanyar da aka shata musu.

Godiya ga Allah mai yawa gafara da tausayi. Amincinsa ya tabbata ga annabawansa da alayensu da wasiyyansu masu daraja.

Allah ya sa mu dace.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

 

[1] (Abu Dawud da Tirmizi daga hadisin Sa’alaba). Nailul Autar: Shaukani; j 9, s 229.

Check Also

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali

Gadir Manuniya ce ga Jagorancin Ali (a.s) Jagorancin Ahlul-baiti (a.s) da aka kafa da umarnin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *